Rufewa
Masu bin shafin namu nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnim.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
Amma kafin nan muke cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 02/09/2025
Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida
Masu bin shafin namu nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnim.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
Amma kafin nan muke cewa mu kwana lafiya.
Jami’an ƴansanda a birnin Marseille na Faransa sun harbe wani mutumin da ake zargi da kashe mutum biyar ta hanyar caka musu wuƙa.
Mutumin da ake zargi dan asalin Tunisia ne. Rahotanni sun ce ya fara caka wuƙar ne a wani otal da aka kore shi saboda rashin biyan kuɗin kwana.
Wani mai gabatar da kara a yankin ya ce, ɗaya daga cikin mutanen da abin ya rutsa da su, na cikin mawuyacin hali.
Wani Bidiyo da aka wallafa ya nuna jami’an ƴansanda cikin fararen kaya suna harba bindiga kan wanda ake zargin, yayin da yake zare wuƙar a cikin jama'a.
Sabuwar girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 5.2 ta sake afka wa kudu maso gabashin Afganistan, kwana biyu bayan wata girgizar ƙasar mai ƙarfi ta yi ajalin daruruwan mutane.
Wani jami’in yankin ya ce, an sake samun girgizar ƙasar a sassan lardin ƙunar da ta afku a ranar Lahadi.
Jami'in ya ce suna amfani da dabbobi irin su Jakuna wajen shigar da agajin abinci zuwa yankin.
Sai dai ba'a samu rahoton wata sabuwar ɓarna ba da girgizar ƙasar ta yi a halin yanzu.
Tun da farko, gwamnatin Taliban ta ce adadin mutanen da suka mutu a ƙarshen mako ya ƙaru zuwa sama da 1,400.

Asalin hoton, EPA
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya soki matakin Amurka na hana jami'an Falasɗinawa biza, gabanin babban taron Majalisar Dinkin Duniya da za a gudanar ckin watab da muke ciki.
Mista Macron ya kira matakin da ''abin da ba za a lamunta ba'', yana mai kiran Amurka ta janye ƙudirin.
A jawabinsa na baya-bayan nan kan rikicin Isra'ila da Falasɗinawa, Mista Macron ya ce yana tattaunawa da Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman, domin faɗaɗa kiran amincewa da kafa ƙasashe biyu.
Ya ce babu wasu hare-hare ko yunƙurin mamaya ko kuma tilasta kwashe mutane, da zai dakatar da shi da Yariman na Saudiyya daga ƙudirinsu.
Mista Macron ya ce Faransa za ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kai cikin wannan wata.

Asalin hoton, Social Media
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bayar da umarnin mayar da tsohon shugaban hukumar Talbijin na Ƙasar, NTA da aka sauke kwanan nan, Salihu Abdullahi Dembos.
Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar ya ce Dembos wanda Shugaba Tinubu ya naɗa a 2023 - a yanzu zai dawo domin kammala wa'adin mulkinsa na shekara uku.
A ƴan kwanakin nan ne aka sanar da sauke Dembos sakamakon wasu sauye-sauye da aka gudanar da hukumar.
Sauke shi ya janyo zazzafar muharawa da suka musamman daga yankin arewacin ƙasar, inda Salihu Abdullahi Dembos ya fito.
Haka ma shugaban ƙasar ya bayar da umarnin maido da Mista Ayo Adewuyi a matsayin babban daraktan sashen labarai na NTA, domin shi ma ya ƙara wa'adinsa na shekara uku da zai ƙare a 2027.

Asalin hoton, Google
Tsohon Ɗan Majalisar Dattawan Najeriya mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya, Sanata Kabiru Marafa ya sha alwashin rage wa Tinubu ƙuri'u masu yawa a zaɓen 2027.
Marafa, wanda a baya-bayan nan ya sanar wa BBC ficewarsa daga jam'iyyar APC, bayan ya zargi Tinubu da ''watsar da shi bayan cin zaɓe'' ya ce sai ya kawo wa shugaban ƙasar cikas a zɓen 2027 da ke tafe.
Yayin wata hira da hgidan talbijin na Channels, Sanata Marafa ya ce sai ya janyo wa Tinubu asarar kimamin ƙuria' miliyan guda.
Tsohon ɗan majalisar - wanda ya kasance babban daraktan yaƙin neman zaɓen Tinubu a Zamfara a 2027 - ya ce zai nuna wa shugaban ƙasar matsayinsa a siyasar jihar Zamfara.

Asalin hoton, Reuters
An yi wa dakarun ko-ta-kwana na Isra'ila kiran gaggawa domin su dawo baki daga a fafata da su a yaƙin Gaza.
Gwamnatin Isar'ila ta ce ya zama wajibi a gayyato tare da amfani da kaso mafi yawa na dakarun ko ta kwanan, domin shiga cikin manyan farmakin da za ta kai mafi girma tun bayan fara yaƙin Gaza, wanda zai ba ta damar karbe ikon Gazan baki daya.
Sai dai kafofin yaɗa labaran Isra’ilar na cewa ana fuskantar ƙalubale a wannan kiran, domin da dama daga cikin dakarun ko ta kwanan ba su shirya dawowa bakin aiki ba, bayan kusan shekara biyu ana fafatawa.
Rahotanni sun ce a wasu sansanonin dakarun Isara'ilar an fuskanci ƙarancin dakarun ko ta kwanan da dama, idan aka kwatanta da kiran da a kai musu a baya.

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi kira ga ɓangarorin da ke yaƙi a Sudan da su shiga yarjejeniyar tsagaita wuta domin bai wa agajin jin ƙai damar isa ga waɗanda mummunar zaftarewar ƙasa ta rutsa da su a yankin Darfur.
Shugaban kungiyar, Mohamoud Ali Yusuf, ya ce dole ne a gaggauta kai tallafin jin ƙai.
Mataimakin mai kula da harkokin jin ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya Antoine Gerard ya bayyana wa BBC cewa, yankin yana da mutuƙar wahalar shiga, kuma hakan ya haifar da cikas wajen kai kayan agaji.
Ƙungiyar masu ɗauke da makamai ta Sudan Liberation Army Movement, wadda ke da iko a yankin Jebel Marra inda lamarin ya auku, ta ce kusan mutum dubu ɗaya ne suka mutu.

Asalin hoton, Senator Bala A. Mohammed
Shugaban ƙungiyar gwamnanonin jam'iyyar PDP, Bala Mohammed ya ce jam'iyyar ta gaji da mutanen da ke jefa ta cikin rikici.
Gwamnan Bauchin na mayar da martani ne kan sharuɗan da tsagin Nyesom Wike ya gindaya kan gudanar da babban taron jam'iyyar na ƙasa.
Tsagin na Wike ya gindaya wasu sharuɗɗa da ya ce dole jam'iyyar ta bi idan tana son komai ya tafi yadda ya kamata.
Sharuɗɗan sun ƙunshi dole shugaban jam'iyyar ya fito daga yankin arewa ta tsakiya.
To sai dai yayin martanin nasa, gwamnan na Bauchi ya ce jagororin PDP mutane ne da suka san ciwo kansu.
“Ba za mu ci gaba da yin shiru muna barin wasu mutane suna yi mana yawo da hankali ba.'' in ji shi.
Gwamnan ya ce, “Shugaban jam'iyya na ƙasa ya yi magana da kyau, babu wani kokwanto game da jagorancin kwamitin shirya babban taron ba, domin sun yi a baya, kuma mun yi imanin za mu yi nasara'', in ji shi.
Jam'iyyar PDP dai ta faɗa rikici tun gabanin zaɓen 2023, matsalar da wasu masana ke alaƙanta rashin nasarar jam'iyyar a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban China Xi Jinping ya nemi Pakistan da ta ƙara inganta tsaro ga ‘yan ƙasar ta da aka rika kai wa hare-haren ‘yanbindiga yayin da suke aiki a kan ayyukan da Beijing ke ɗaukar nauyi.
A wani taro da ya yi da Firayim Ministan Pakistan Shehbaz Sharif, yayin wani taro wasu kasashen tsohuwar tarayyar Soviet da kuma wasu kasashen Asia, Mista Xi ya roƙi Islamabad da ta tabbatar da tsaro ga ma’aikatan China da kuma cibiyoyinsu da ke Pakistan.
Kasashen biyu na gudanar da ayyuka da suka kai biliyoyin daloli na samar da manyan aiyuka, wanda ya haɗa da gina hanyoyi, layin dogo da kuma tashar jiragen ruwa.
Sai dai an dakatar da dama daga cikin ayyukan, inda batun tsaro ya kasance ɗaya daga cikin dalilai.

Asalin hoton, ANDRE BORGES/EPA/Shutterstock
Kotun ƙolin Brazil ta fara shirye-shiryen matakin ƙarshe kan shari’ar Jair Bosonaro, tsohon shugaban ƙasar, bisa zargin jagorantar shirin juyin mulki don rusa sakamakon zaɓen shekarar 2022.
Wakilin BBC ya ce lauyoyin gwamnati sun zargi tsohon shugaban da ƙarfafa gwiwar dubban magoya bayansa, wajen mamaye gine-ginen gwamnati tare da lalata su, mako guda bayan shugaba Lula da Silva ya kama aiki.
A gefe guda kuma Lauyan Mista Bolsonaro ya ce ba zai halarci zaman kotun ba.
Ya kuma musanta shirin juyin mulki tare da jaddada cewa ba shi da hannu a tarzomar. Idan aka same shi da laifi zai iya fuskantar ɗaurin shekaru har 43 a gidan yari.

Asalin hoton, BBC Pidgin
Wasu ƴan jam'iyyar PDP da ake ganin ƴan tsagin Ministan Abuja, Nyesom Wike ne sun gudanar da wani taro a daren jiya Litinin a Abuja, inda suka fitar da wasu sharuɗa da suka ce a cika kafin babban taron jam'iyyar, wanda za a yi a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamban bana a birnin Ibadan na jihar Oyo.
A wata sanarwa da suka fitar a yau Talata, mutanen waɗanda suka kira kansu da suna Eminent Leaders and Concerned Stakeholders of the PDP, sun ce sun amince da tsarin rabon muƙaman jam'iyyar, amma suka ce ba za su aminta da ƙara rarraba muƙaman ba zuwa jihohi, bayan rabon a tsakanin yankunan.
Haka kuma sun ce duk da sun amince a bar shugabancin jam'iyyar a arewa, suna so ne shugaban ya fito daga yankin arewa ta tsakiya.
Sauran sharuɗan su ne:
Sanarwar ta ƙara da cewa idan har aka yi adalci, jam'iyyar PDP za ta magance matsalolin da take fuskanta sannan ta dawo da ƙarfinta.

Asalin hoton, NAFDAC NIGERIA
Hukumar kula da inganci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC, ta gargaɗi ƴan ƙasar kan amfani da wasu allurai da ta ce ta gano jabu ne aka haɗa ana sayarwa a kasuwanni da kantunan magunguna a faɗin ƙasar, inda ta buƙaci mutane su kula.
NAFDAC ta bayyana haka ne a wata sanarwar gargaɗi da ta fitar a shafinta na X, inda ta bayyana cewa ba a yi wa alluran rajista da hukumarsu ba.
Ta ce akwai allurar Gold Vision Oxytocin mai ɗauke da lambar rajista NAFDAC ta bogi ta A4-9566, wadda ta ce ana haɗawa a kamfanin Anhui Hongye Pharmaceutical Co., Ltd da ke titin Fengyang ta Gabas a lardin Anhui da ke ƙasar China, amma kamfanin Gold Vision Medicals da ke titin Range Avenue a jihar Enugu ta kudancin Najeriya ke kasuwancinsa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya isa Beijing, babban birnin ƙasar China domin halartar wani babban faretin soji da ƙasar take yi.
Taron faretin mai suna ranar nasara, za a yi shi ne a ranar Laraba, wanda zai zama silar haɗa Kim da takwaransa na China Xi su taru a rumfa ɗaya, sannan zai haɗa Putin na Rasha da wasu shugabannin duniya.
A yau Talata ne Kim ya isa birnin Beiging a jirgin ƙasa mai sulke, bayan ya bar ƙasarsa a ranar Litinin.
Wannan ne karo na farko da shugaban Koriya ta Arewa zai halarci taron faretin na nasarar China tun daga shekarar 1969, inda zai shiga cikin takwarorinsa na ƙasashen duniya 26 da za su haɗu domin tayar China murna.
A taron na shekarar 2015 ne Koriya ta Arewa ta aika wakilin gwamnatin ƙasar mai suna Choe Ryong-hae.

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, APC
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yaba da jajircewar mataimakinsa, Kashim Shettima, wanda ya bayyana da mutum mai amana da gaskiya da yake jin daɗin aiki da shi.
A wata sanarwa da ya fitar kan taya mataimakin nasa murnar cika 59 a duniya, Tinubu ya ce, "tun da na sanka har zuwa yanzu, ba ka nuna gajiyawa wajen aiki tuƙuru domin sake gina ƙasarmu. A dukkan muƙaman da ka riƙe a baya, ka nuna jajircewa wajen aiwatar da abubuwan da suka dace duk runtsi duk wahala."
Tinubu ya ce yana godiya bisa irin goyon bayan da yake samu daga Shettima, "lokacin da na zaɓe ka a matsayin mataimakina, na san ban yi zaɓen tumun-dare ba, na san na ɗauko nagartacce wanda Najeriya za ta yi alfahari da shi. Kullum a aikinka na mataimaki, kana ƙoƙari wajen kawo shawarwari da tsara sababbin abubuwa da za su taimaka mana wajen sauke nauyin da muka ɗauka."
"Ban yi ba kuskure ba wajen zaɓenka a matsayin mataimaki. Tare da kai mun fara aikin dawo da martabar Najeriya ta hanyar gyare-gyare da matakan da muka fara ɗabbaƙawa a shirinmu na Renewed Hope Agenda," in ji shi, inda ya ƙara da cewa alaƙarsu ta wuce maganar aiki kawai.
Tinubu ya ce suna samun nasarori da yawa tare, "ka sake nuna mana irin nasarorin da za a samu idan aka sadaukar kai tare da haɗin kai wajen ciyar da ƙasa gaba, wanda shi ne abin da ya kama masu zama shugabanni za su koya."

Asalin hoton, Nader Khan lost his sons and daughters in law to the earthquake
A daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar aikin ceto domin zaƙulo waɗanda baraguzai ya rufe a sanadiyar girgizar ƙasa ta Afghanistan, waɗanda suka tsira sun fara bayyana yadda suka tsallake rijiya ta baya.
An ai kai yawancin waɗanda ibtila'in ya shafa ne zuwa asibitin Jalalabad, inda ɗaruruwan waɗanda suka ji rauni suke jinya.
Mir Zaman ya bayyana wa BBC cewa da hannunsa ya zaro gawar ƴaƴansa daga baraguzai.
"Cikin duhu ne domin babu wutar lantarki, sai wani ya ara min fitila na hake, sai na yi amfani da shebir da diga na haƙo gawarwakinsu. Babu wanda zai taimaka maka saboda kowa ta kansa yake yi. A ƙauyenmu akwai mutane da dama da suka mutu, kuma har yanzu akwai wasu a ƙarƙashin garaguzan ginin."
Ya ƙara da cewa akwai iyalan da dukkansu ne suka rasu a girgizar ƙasar.
A asibitin Nangrahar da ke Jalalabad, Nader Khan wanda ya tsira ya fashe da kuka a lokacin da yake bayyana yadda ya rasa ƴaƴansa biyu da jikoki biyu.
Khan mai shekara 60 ya ce za samu sanarar ceto jikokin nasa, amma kuma sai suka ɓace masa.
"A lokacin ceto su ne na ji rauni a kai da bayana, sai ya zama ba zan iya yunƙurawa ba, haka nan dole na haƙura. Yanzu ban san inda gawarwakin ƴaƴana yake ba," in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin sojin Burkina Faso a ƙarƙashin jagorancin Faso Ibrahim Traore ta sanar da haramta auren jinsi a ƙasar baki ɗaya.
Wannan na zuwa ne kimanin shekara guda bayan an amince da wani daftarin dokoki da aka yi garambawul a kan dokokin iyalin ƙasar, inda a ciki aka ƙara auren jinsi.
Ƙasar da ke yankin Sahel ta kasance a cikin ƙasashen Afirka 22 a cikin 54 da suka amince da auren jinsi, lamarin da ke ɗaukar hukuncin kisa ko zaman gidan kaso mai tsaro a wasu ƙasashen.
A jiya Litinin ne gwamnatin ƙasar ta amince da sabuwar dokar wadda ta haramta auren na jinsin.
A sabuwar dokar, wanda aka kama da auren jinsi zai iya fuskantar zaman gidan yari na shekara biyar, kamar yadda ministan shari'a na ƙasar Edasso Rodrigue Bayala ya sanar a kafar gwamnatin ƙasar ta RTB.
A bara ma dai maƙwabciyar ƙasar, Mali ta yi dokar haramta auren jinsi.

Asalin hoton, Getty Images
Ana ci gaba da aikin ceto dubban mutanen da girgizar kasa ta afkawa a lardin Kunar da ke gabashin Afghanistan shekaran-jiya Lahadi.
Da yawa sun kwana a filin Allah, bayan an ciro su daga cikin laka da gidajen duwatsu da aka gina a cikin kwaruruka.
Jiragen sama masu saukar ungulu sun yi jigilar wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Jalalabad. Hukumomin Taliban sun ce sama da mutane dari takwas ne aka tabbatar sun mutu.
Sun bukaci agajin kasa da kasa, ko da yake rokon nasu ya zo ne a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke fuskantar karancin kudade.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya ce an fara samar da dala miliyan biyar a matsayin agajin farko.

Asalin hoton, Getty Images
Wani jirgin kasa mai sulke dauke da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya tsallaka iyakar China a kan hanyarsa ta zuwa Beijing babban birnin kasar.
Ana sa ran zai bi sahun wasu shugabannin kasashen duniya kusan ashirin a faretin sojan da za a yi gobe Laraba a birnin Beijing, don tunawa da ranar da Japan ta miƙa wuya, shekaru 80 da suka gabata, wanda ya kawo ƙarshen yaƙin duniya na biyu.
Ana sa ran nisan tafiyar zai kai awa 20 daga Pyanyong babban birnin Koriya ta Arewar zuwa Beijing, domin jirgin na tafiyar kilomita 60 ne kacal a awa guda saboda nauyinsa.
Masu sharhi na ganin irin wannan balaguro da shugaban na Koriya ta Arewa ke yi a matsayin wani kokari na nuna izza da buwayarsa ga duniya.
Wani wakilin BBC a Koriya Ta Kudu mai makwabtaka, ya ce bayyanar Mista Kim tare da shugabannin China, da Rasha da sauran shugabannin duniya na iya ba shi damar ci gaba da ɗaga kafaɗarsa ga ƙasa kamar Amurka.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da madatsun ruwa ta Najeriya wato Nigeria Hydrological Services Agency (NiHSA) ta yi gargaɗin cewa aƙalla jihohin arewacin Najeriya guda 18 ne ke fuskantar barazanar ambaliya a mako biyu na farkon watan Satumban nan da aka shiga.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X, ta ce jihohin Najeriya 29 ne tare da Babban Birnin Tarayya Abuja suke fuskantar barazanar ta ambaliya a tsakanin 1 zuwa 15 ga watan Satumba.
Hukumar ta ce ambaliyar za ta iya shafar ƙananan hukumomi 107, da garuruwa 631, sannan aƙalla manyan titunan ƙasar 50 za su fuskanci tsaiko.
Daga cikin jihohin da suka fi shiga barazanar, akwai Borno da Zamfara da Jigawa da Kebbi da Yobe da Filato da Gombe da Taraba da Sokoto, sannan akwai jihar Kaduna barazanar ba ta ƙarfi sosai.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X