Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 02/09/2025

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. Yau Shugaban Rasha zai gana da takwaransa na China

    China

    Asalin hoton, Sputnik/Pool via Reuters

    A yau Talata ne ake sa ran shugaban China Xi Jinping zai gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a birnin Beijing na ƙasar China.

    Tattaunawar ta biyo bayan ganawar da suka yi a gefen taron kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai a birnin Tianjin, na Chinan shekaran jiya Lahadi.

    A yayin wannan taro, Mr Xi ya soki abin da ya kira "Ɗabi'ar cin zarafi" daga wasu kasashe, wani zunde da ake ganin ya yi wa Amurka.

    A nasa bangaren shugaba Putin ya kare matakin Rasha na kaddamar da hari a Ukraine, inda ya bayyana kasashen Turai a matsayin kanwa uwar gami.

  2. Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna zai koma aiki nan da kwana 10 – Minista

    Jirgi

    Asalin hoton, BBC Hausa

    Ministan sufurin Najeriya, Sa'idu Ahmed Alkali ya ce nan da kwana goma jirgin ƙasan Abuja-Kaduna da ya lalace zai koma aiki.

    A makon jiya ne dai jirgin ƙasan ya kauce hanya, inda ya tunsture a kusa da tashar Asham bayan ya taso daga Abuja zai tafi Kaduna ɗauke da mutum 618, ciki har da har da fasinja 583 da ma'aikatan jirgin ƙasan guda 15 da ma'aikacin jinya 1 da masu goge-goge 11, sannan aƙalla fasinja bakwai ne suka ji rauni.

    A wata ziyara da ministan sufurin ya kai wajen da jirgin ya kauce hanya a jiyar Litinin, ya yaba da ƙoƙarin jami'an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki bisa ƙoƙarin da suka yi wajen tabbatar da tsaron fasinjojin da sauran ma'aikatan jirgin har aka kwashe su.

    "A lokacin da jirgin ya tuntsure, jirgin yana tafiya ne da tarago guda bakwai. Tuni mun kwashe guda huɗu, sannan muna ƙoƙarin kwashe sauran. Muna sa ran nan da kwana biyu za mu kwashe sauran taragon, sannan in sha Allah nan da kwana goma jirgin ƙasa zai koma aiki kamar yadda ya saba," in ji ministan.

  3. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da safiyar Talata daga nan sashen Hausa.

    Da fata za ku kasance tare da mu domin ci gaba da samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Ku kasace tare da mu.