Majalisar wakilan Najeriya ta yi ƙudurin ƙara kujeru domin mata da masu buƙata ta musamman
Majalisar wakilan Najeriya ta gabatar da wani ƙudiri domin yin gyara ga sashe na 49 na kundin tsarin mulkin ƙasar na shekarar 1999.
Ƙudurin na neman a samar da ƙarin kujeru na musamman ga mata da masu buƙata ta musamman.
Sai dai wasu ƙungiyoyin na masu buƙata ta musamman suna ganin ba kafa dokar ba ce matsala, inda suke fargabar ko an gabatar da ƙudurin, ta kuma zama doka, da wahala ta yi ƴansiyasar ƙasar su yi amfani da ita, ko kuma a bari ta yi tasiri, har su anfama.