Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gyokeres zai bi Amorim United, Madrid za ta kashe maƙudan kuɗi kan Enzo Fernandez
Sporting ta cimma yarjejeniya da Manchester United kan Ruben Amorim, Steven Gerrard yana fuskantar matsin lamba kan Al-Ettifaq, yayin da Barcelona ke zawarcin Rafael Leao.
Sporting ta cimma matsaya kan barin kocinta Ruben Amorim ya bar kungiyar ya koma Manchester United a lokacin hutun kasa da kasa na watan Nuwamba. (Telegraph )
United za ta biya diyya don baiwa wasu ma'aikatansa damar tafiya tare da shi zuwa Old Trafford. (ESPN)
Dan wasan gaban Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 26, da dan wasan tsakiya na kasar Denmark Morten Hjulmand, mai shekara 25, ba su ji dadin shawarar Amorim ta barin Sporting ba bayan da suka ki amincewa da tayin barin kungiyar da kansu a bazara. (Ojogo Portuguese)
Sai dai akwai yiwuwar Gyokeres zai bi Amorim a Manchester United idan har za a iya cimma yarjejeniya. (Football 365)
Dan wasan gaban Bayern Munich da Jamus Jamal Musiala, mai shekara 21, ya ce yana zaune hankali kwance a a kulob din na Bundesliga duk da alakanta shi da Manchester City da ake yi. (Goal)
Manchester United na iya yin hamayya da Liverpool kan dan wasan bayan Wolves dan kasar Algeria Rayan Ait-Nuri mai shekaru 23. (GiveMeSport)
Brentford za ta bukaci fan miliyan 60 kan dan wasan gaban Kamaru Bryan Mbeumo, mai shekara 25, a kasuwar musayar 'yan wasa a watan Janairu, yayin da itama Arsenal ke zawarcinsa. (Football Insider)
Steven Gerrard na fuskantar kora daga mukaminsa na kocin Al-Ettifaq, bayan da kungiyar ta Saudiyya ta yi rashin nasara a gasar cin kofin kasar da aka yi a makon nan. (Sun)
Aston Villa na tattaunawa da dan wasan gaban Ingila Morgan Rogers, mai shekara 22, kan sabuwar yarjejeniya. (Athletic)
Real Madrid na tunanin dauko dan wasan tsakiyar Faransa Aurelien Tchouameni, mai shekara 24. (Relevo)
Real Madrid za ta biya fam miliyan 84 don siyan Enzo Fernandez ko kuma ta ba Chelsea Tchouameni a matsayin wani bangare na cinikin dan wasan tsakiyar Argentina mai shekara 23. (Fichajes/TeamTalk)
Barcelona na sa ido kan halin da Rafael Leao ke ciki a AC Milan da nufin daukar dan wasan na Portugal mai shekara 25 a bazara. (Sports Espanya)
Liverpool ta bayyana dan wasan bayan Bournemouth da Hungary Milos Kerkez, mai shekara 20, a matsayin daya daga cikin wadanda take nema a matsayin lamba uku (TeamTalk)
Athletic Bilbao na fatan kulla sabuwar yarjejeniya da dan wasan Spain Nico Williams, mai shekara 22, yayin da Barcelona ke zawarcinsa. (Sports Espanya)
Getafe na zawarcin dan wasan bayan Tottenham Sergio Reguilon, mai shekara 27, wanda kwantiraginsa zai kare a watan Yunin 2025. (Fichajes Spanish)