Ku San Malamanku tare da Malam Junaidu Abubakar Sadiq

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

A wannan makon, filin Ku San Malamanku, ya tattaunawa da Malam Junaidu Abubakar Sadiq.

An haifin malamin a garin Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya a shekarar 1992.

Malamin, wanda shi ne limamin masallacin Al-Irfan kuma manajan daraktan Al Fayda Tidjaniya TV, ya shaida wa BBC cewa "mun taso ne a gida na karatu: iyayenmu da kakaninmu almajirai ne, musamman kakana As-Sheikh Ibrahim Mushaddidu Jos shi ne ya karantar da mahaifina.

Ya ce ya soma karatu ne a wurin mahaifinsa kuma daga bisani ya sanya shi a makarantar Nizamiyyat - inda a nan ne ya yi nazare ya yi kuma firamare a markazus-sakaful Islam, kana ya yi sakandare a Kulliyatu Ibn Abbas, karkashin kulawar makarantun Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Malam Junaidu Abubakar Sadiq ya kara da cewa a can ya ssauke Alkur'ani sanna ya yi NCE a reshen Makarantar Sa'adatu Rimi da ke Bauchi.

Kazalika malamin ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar Jos.

A fannin karatun zaure, Malam Junaidu ya ce ya yi karatu a wurin Sheikh Aminu Jibril Bauchi da Malam Ibrahim Zafi da sauran manyan malamai da ke Bauhci da wasu jihohin.