Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 14/11/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, Ahmad Bawage da Abdullahi Bello Diginza

  1. Shugaban Faransa Macron ya ce ba zai lamunci ƙyamar Yahudawa ba

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce ƙasar ba za ta amince da ƙyamar Yahudawa ko tashin hankali ba, yayin da yake shirin halartar gasar wasan ƙwallon ƙafa tsakanin ƙasar da Isra'ila.

    Aƙalla ƴansanda 4000 ne ke aikin sintiri saboda fargabar abin da zai iya biyo baya sakamakon rikicin Isra'ila a Gaza da Lebanon.

    Za a fafata gasar ne mako guda bayan ƴansanda sun kama mutane da dama a Amseterdam yayin da ƴan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ajax suka kara da takwararta ta Isra'ila Maccabi Tel Aviv.

    Bayan kammala wasan, samari sun fantsama kan tituna suna kai wa magoya bayan Maccabi hari.

    An zargi wasu magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Maccabi da lalata kaya tare da yi wa Larabawa kalaman ɓatanci.

  2. An kashe mutum fiye da 1500 da sace fiye da 2000 a Najeriya - NHRC

    Hukumar kare haƙƙin bil-adama ta Najeriya, wato NHRC, ta bayyana cewa, tsakanin watan Janairu zuwa Satumba na wannan shekara, an sami aukuwar sace-sacen jama'a kusan 2000, aka kuma halaka wasu kusan 1500 a sassan kasar.

    Jami'an hukumar ne suka bayar da wannan rahoto, a wajen wani taron tuntuɓa na kuniyoyin farar hula, kan halin da ake ciki game da batutuwan da suka shafi al'amuran kare hakkin bil'adama a kasar, wanda hukumar ta shirya tare da hadin gwiwar ƙungiyar tarayyar Turai, kuma aka gudanar yau a babban birnin tarayya Abuja.

    Rahoton ya ce an sace mutum 1712 sannan an kashe mutum 1463 a wurare daban-daban na Najeriya, daga watan Janairu zuwa watan Satumba na bana.

    Hukumar kare haƙƙin bil'adaman ta Najeriya ta kuma yi tsokaci, cewa an sami ƙaruwar adadin yara ƙanana da ake yi watsi da su a rariya, inda a cikin watan Satumban da ya gabata aka lissafa aukuwar hakan har sau 2723.

    Dangane da kisan jama'a da kan auku a Najeriyar kuwa, hukumar kare haƙƙin bil'adaman ta ƙasar ta danganta hakan da ƙarin ɗibar yara da ta ce ƙungiyoyin 'yan ta'adda suke yi, kuma suke tafka ta'asa a kasar.

    Alkaluman da hukumar kare haƙƙin bil-adaman ta Najeriyar ta gabatar a wajen wancan taro dai sun fayyace ƙamarin munin aukuwar tashe-tashen hankula da keta haƙƙokin bil'adama da ke aukuwa a sassan ƙasar.

    Ƙungiyar dai ta bayyana al'amarin da wani abu da ke ci gaba da zama babban ƙalubale, kuma yana nan yana dakon a shawo kansa.

  3. Isra'ila na aikata laifukan yaƙi a Gaza - HRW

    Kungiyar Kare Hakkin ɗan Adam ta Human Rights Watch ta ce yadda Isra'ila ta tilasta wa Falasɗinawa a Gaza barin muhallansu, daidai yake da aikata laifukan yaki da cin zarafin ɗan'adam.

    A wani rahoto, kungiyar kare hakkin dan Adam din mai cibiya a New York ta ce akwai yiwuwar sauyin wurin zaman na dindindin ne.

    Ƙungiyar ta kuma bayyana abin a matsayin yunkurin shafe wata kabila daga doron ƙasa. Zargin da Isra'ila ta yi watsi da shi.

    Abin da sabon rahoton Human rights Watch ya mayar da kai a kan sa shi ne, umarnin sauyawa mutane gurin zama da sojin Isra'ila suka dinga bayarwa akai-akai a Gaza, wanda ya sa kusan mutane miliyan biyu suka rasa muhallansu.

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Isra'ila ba tayi martani game da batun ba.

  4. An zargi ƴansanda da musgunawa masu haƙar ma'adinai a Afrika ta Kudu

    Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam ta Afrika ta Kudu ta ce za ta binciki yansanda game da tilasta wa masu haƙar ma'adinai su fito ta hanyar hana su abinci da ruwa.

    Cikin kwanakin nan an tilasta wa ɗaruruwa su fito amma wasu sun ƙi fitowa saboda fargabar kame da fidda su daga ƙasar, abin da ya sa suka zauna a ƙarƙashin ƙasa tsawon wata ɗaya.

    Ana tunanin da dama daga cikinsu ƴan ci-rani ne daga maƙwabtan ƙasashe.

    Wannan na zuwa ne bayan mahukunta sun datse shigar da abinci da ruwa isa ga dubbana masu hakar ma'adinai da ake kira zama-zamas, gwamnati ta ce ba za a taimakwa wdanda ake zargi da aikata laifi ba.

    Rahotannin da ba a tantance ba sun ce wasu daga cikinsu sun mutu yayin da wasu ke jinya.

    An ƙiyasta haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba, inda mutane ke kwashe makonni a ƙarƙashin ƙasa suna neman ɓurɓushin zinare da demon na haifarwa da asarar kuɗaɗen shiga.

  5. Yadda ƴan bindiga suka sace ɗalibai a Katsina

    Wasu ƴan bindiga haye kan babur sun yi garkuwa da wasu yara maza ɗalibai guda biyu da ke kan hanyarsu ta zuwa ƙaramar makarantar sakandire da ke garin Babban Duhu a ƙaramar hukumar Safana da ke jihar Katsina.

    Wani malamin makarantar wanda ba ya son a ambaci sunansa ya shaida wa BBC cewa al’amarin ya faru ne da safiyar yau ɗin nan, inda ƴanbindigar suka yi awon gaba da yaran guda huɗu kafin daga bisani yara biyu su tsere.

    Malamin ya ƙara da cewa "har kawo yanzu ba bu labarin cewa ƴanbindigar sun kira iyalan yaran domin neman kuɗn fansa."

    Babu wani bayani da ya nuna cewa jami'an tsaro sun bi ƴanbindigar domin ceto yaran guda biyu da suka yi garkuwa da su. Sai dai jami'an tsaro da gwamnati sun sha fadin cewa suna samun nasara a kan ƴanbindigar.

  6. Harin Isra'ila ya kashe mutane da dama da jikkata wasu a Siriya

    Kafar yaɗa labaran Siriya ta ce an kashe mutane da dama yayin da wasu suka jikkata sakamakon harin da Isra'ila ta kai wa rukunin wasu gidaje da ke Damascus, babban birnin Syria.

    Rahotannin sun ce ɗaya daga cikin gidajen yana a Mazzeh, yankin da ya kasance hedikwatar hukumomin tsaro da ofisoshin jakadanci da na MDD.

    Ɗayan gidan kuma yana Qudsuya da ke kudancin babban birnin ƙasar.

    Gidan rediyon sojin Isra'ila ya ce cibiyar mayakan Falasɗinawa aka kai wa harin.

    Isra'ila dai ta sha kai wa ƙungiyoyin da ke da alaƙa da Iran da kuma Hezbollah a Siriya hare-hare a lokuta da dama.

  7. An samu ƙarin waɗanda suka kamu da ciwon suga - Bincike

    Masu bincike sun ce an samu ƙarin waɗanda suka kamu da ciwon suga daga shekara ta 1990.

    Binciken ya nuna cewa an samu ƙarin daga kashi 7 zuwa kashi 14 na manya da suka kamu da ciwon.

    Zuwa yanzu akwai mutane miliyan 800 da suka kamu da ɗaya daga cikin nau'ukan ciwon suga.

    Masu binciken sun gano cewa cutar na haifar da yanke gaɓa da ciwon zuciya da ciwon ƙoda da rashin gani da kuma mutuwa.

    Sun ƙara da cewa mutanen da suka fi kamuwa da cutar sun fito ne daga ƙasashe masu tasowa, inda samun magani ya ke da matuƙar wahala.

    Waɗanda suka gudanar da binciken sun ƙara da cewa abinci marasa inganci ne sahun gaba cikin abubuwan da ke haifar da ciwon suga tsakanin manya.

  8. UEFA ta fara bincike kan raflin Premier da aka dakatar

    Hukumar alƙalan wasa ta PGMOL ta ce tana ɗaukar sabbin zarge-zargen da ake yi wa rafalin gasar Premier David Coote da 'matuƙar muhimmanci.'

    An dakatar da Coote daga aikinsa har sai an gudanar da bincike kan wani bidiyo da ya fito a farkon wannan makon, inda alƙalin wasan mai shekaru 42 ya furta ƙalaman ɓatanci kan tsohon kocin Liverpool Jurgen Klopp.

    Hukumar ƙwallon ƙafar Turai Uefa ma ta ƙaddamar da nata binciken tare da dakatar da Coote.

    A ranar Laraba, jaridar Sun ta buga hotuna da ta ce an ɗauka a lokacin gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana, inda ake zargin cewa sun nuna Coote yana shakar wata farar hoda da naɗaɗɗiyar takardan kuɗin Amurka.

  9. Me ya sa APC ke son a hana ƙananan hukumomin Kano kuɗin wata-wata?

    A jihar Kano dai ana ci gaba da zaman doya da manja tsakanin APC da NNPP inda kowannensu ke ƙoƙarin ganin ya shiga gaba a harkokin siyasar jihar mai yawan al’umma a arewacin Najeriya.

    Dambarwar baya-bayan nan dai ta faru ne bayan da jam’iyyar APC a jihar ta Kano ta nemi kotu ta dakatar da hukumomin gwamnatin tarayya daga bai wa ƙananan hukumomin jihar kason kuɗinsu na wata-wata.

    Wannan kuma zuwa ne bayan da wata kotu ta bayar da umarnin hana duk wata hukuma ko wani yunƙurin dakatar da kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar.

    Tun kafin zaɓen ƙananan hukumomin jihar dai ake ta kai ruwa rana tsakanin APC da NNPP wanda har kotu ta bayar da umarnin ka da a gudanar da zaɓen amma daga bisani wata babbar kotun jiha ta bada umarnin a yi zaɓen.

  10. Wani mutum ya mutu a yunkurin kai hari kotun kolin Brazil

    Wani mutum ya mutu a ƙoƙarin kai hari kotun kolin Brazil a Brasilia, babban birnin ƙasar bayan da ababen fashewa da ke jikinsa suka tashi.

    Ƴansanda sun bayyana sunan mutumin da ya kai harin a jiya Laraba da Francisco Wanderley Luiz, wanda ya kasa samun nasara a zaɓen kananan hukumomi da aka gudanar karkashin jam'iyyar Liberal ta tsohon shugaban ƙasar Jair Bolsonaro.

    An samu gawarsa a wajen ginin kotun jim kaɗan bayan tashin wasu bama-bamai a yankin.

    Shaidu sun ce sun gan shi yana harba abubuwan fashewa kafin su tashi. Sai dai babu wanda ya jikkata a lamarin, a cewar jami'ai.

    An rufe kan hanyar da za ta kai yankin yayin da jami'ai ke aikin sintiri.

    Babban lauyan gwamnatin ƙasar, Jorge Messias, ya yi Alla-wadai da harin inda ya sha alwashin gudanar da bincike kan lamarin.

  11. Guguwa mai karfin gaske ta nufi Philippines

    Ana cikin shirin ko-ta-kwana a Philippines, kafin isar wata guguwa mai karfin gaske.

    Guguwar da aka yi wa lakabi da Usagi, ita ce ta biyar da ta faɗa wa yankin cikin makonni uku.

    Dubban mazauna birnin Luzon mai tashar ruwa sun fice daga gidajensu tare da komawa sansanonin da gwamnati ta samar.

    Hukumar yanayi ta Philippines ta yi gargaɗin guguwar za ta yi gudun sama da kilomita 180 cikin sa'a ɗaya, lamarin da ke babbar barazana ga mazauna yankunan da abin zai shafa.

    Guguwar farko da aka yi ta ɗaiɗaita yawancin sassan lardin Luzon , inda aka yi hasashen cewa wata guguwar za ta isa birnin Manila a karshen mako.

  12. An ɗaure matasa biyu kan zargin yin kalaman ɓatanci ga shugaban Uganda da matarsa

    Wata kotu a Uganda ta ɗaure wasu matasa biyu kan zargin zagin shugaban ƙasar Yoweri Museveni, da matarsa Janet Museveni da kuma ɗansa janar Muhoozi Kainerugaba a shafin TikoTok.

    Kotun ta tura matasan David Ssengoz da kuma Lucky Choice zuwa gidan yarin Kigo har zuwa raar Laraba mai zuwa kafin a sake gurfanar da su.

    An zarge su da ɓata suna da kuma yin kalaman ƙiyayya kan shugaban ƙasar da matarsa da kuma ɗansa.

    Sai dai matasan sun musanta zargin bayan bayyana a gaban kotu ranar Litinin.

    A watan Satumba ne mai magana da yawun 'yan sandan ƙasar, Rusoke Kituuma ya yi gargaɗin cewa zagin shugaban ƙasa babban laifi ne a Uganda.

  13. Mun samu nasarar fara haƙo ɗanyen mai ganga miliyan ɗaya da dubu ɗari takwas a rana - NNPCL

    Kamfanin mai na Najeriya NNPCL ya ce ya samu nasarar kai ga haƙo ɗanyen mai ganga miliyan ɗaya da dubu ɗari takwas a kowacce rana.

    Shugaban Kamfanin Malam Mele Kyari ne ya bayyana hakan a yau Alhamis, yayin taron manema labarai da ya gudana a Abuja.

    Ya ce alƙaluman da aka samu sun haɗa daga watan Yuni zuwa Nuwamban da muke ciki.

    Kamfanin wanda cikin shekaru 15 da suka gabata ya yi ta fama da rashin taron na masu ruwa da tsaki, ya mayar da hankali ne kan harkokin kasuwancin masu zuba jari kuma hakan ya ja raguwar yawan gangar man da yake samarwa a kowacce rana.

    Malam Mele ya ce suna ta fafutukar ganin yadda za su haɓaka yawan man da ake haƙowa domin ci gaban ƙasar da kuma saukakawa al'umma.

    "An taɓa haƙo ganga miliyan biyu da dubu ɗari biyar a sehkarun baya, amma daga nan aka yi ta fama da rashin saka jari da kuma rashin tsaro har ta kai man da kae haƙo wa ya yi ƙasa zuwa ganga miliyan ɗaya da dubu ɗari huɗu a wannan shekara," in ji shi.

    Ya ce hakan ne ya sa suka tashi da yin aiki tukuru don samo bakin zaren matsalar.

    "Amma zuwa watan Yuni mun ka zuwa ganga miliyan ɗaya da dubu ɗari takwas," in ji Kyari.

    Ya ce nasarar za ta sa a samu ƙarin arziki a ƙasar da haraji da sauransu.

    "A iya sanina babu dogayen layukan mai ba a Najeriya. Cire tallafi ne ya janyo aka samu sauki," in ji shugaban na NNPCL.

    A ɗaya gefen, Malam Lawal Musa babban mai ba da shawara kan kasuwancin NNPCL, ya ce an samu ƙaruwar yawan gas ɗin da ake haƙowa a kasar.

    NNPCL ya ce cikin shekaru biyu da suka gabata, ya cire haramtattun bututan layin mai daga jikin nasa da ya kai 5,800.

  14. Ana hasashen jam'iyyar Republican za ta karɓe ikon majalisar wakilan Amurka

    Ana hasashen cewa jam'iyyar Republican za ta karɓe ikon majalisar wakilan Amurka, a cewar kafar yaɗa labarai ta CBS.

    Amma ta yaya? an yi hasashen cewa za su lashe kujeru da suka kai 218, inda ake sa ran kujerun za su kai 220 zuwa 222.

    Zuwa yanzu, jam'iyyar Democrat ta samu kujeru 208, inda ya rage guda tara.

    Wannan na nufin Donald Trump na da iko da duka majalisun dokokin ƙasar yanzu, inda ya riga ya samu iko da majalisar dattawa.

  15. Yadda ƙishirwa ke kashe 'yan Sudan ta Kudu saboda gaurayar ruwa da fetur

    Gurɓacewar muhalli babbar matsala ce da ke tagayyara sassan duniya, musamman a nahiyar Afirka.

    Al'ummomin da ke zaune a yankunan da ke da albarkatun man fetur sun daɗe suna kokawa kan yadda haƙar albarkatun man ke lalata ruwan sha, da hana su kamun kifi, da sauran wasu harkoki.

    Irin wannan yanayin ne wata al'umma a ƙasar Sudan ta Kudu - ƙasa mafi sabunta a duniya - ta tsinci kanta, inda wasu ke mutuwa saboda ƙishirwa.

  16. An kashe mutum bakwai a zanga-zangar bayan zaɓe a Mozambique

    Aƙalla mutum bakwai ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a zanga-zangar da ta ɓarke bayan zaɓen da aka gudanar ranar 13 ga watan Nuwamba a lardin Nampula da ke arewacin ƙasar Mozambique.

    Wata ƙungiyar kare hakkin fararen hula ta bayyana cewa zuwa yanzu alkaluman waɗanda suka mutu a rikicin da ya fara tun 21 ga watan Okotoba, ya kai aƙalla mutum 47.

    Ƙungiyar ta ce ƴansanda sun harbe masu zanga-zanga a lardin Namicopo da ke birnin Nampula mai yawan jama'a.

    Rahotanni sun ce kashe mutanen ya sa mazauna Namicopo fara farautar ƴansandan da ake zargi da aikata kisan.

    Lamarin ya kai ga jikkata wani jami'in ɗan sanda ɗaya.

    Dubban mutane ne suka fita kan titunan birane da kuma garuruwa don yin Alla-wadai da zargin tafka maguɗi a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar 9 ga watan Oktoba.

  17. 'Yadda ciwon suga ya sauya min rayuwa'

    Duk shekara a rana irin ta yau – ta Wayar da Kai Kan Ciwon Suga – duniya kan mayar da hankali kan ƙalubalen da masu cutar ke fuskanta. A wannan shekarar, hankula sun koma kan Afirka, nahiyar da cutar ke ƙara ƙamari.

    Taken ranar ta wannan shekara shi ne “Kawo Ƙarshen Ƙalubale, Cike Gurbi” wato Breaking Barriers, Bridging Gaps a Turance, kuma an ƙirƙire shi ne da zimmar inganta hanyoyin samun magani ga miliyoyin masu cutar.

    Mutane da dama da ke fama da matsalar na kokawa kan irin wahalhalu da suke fuskanta, musamman wajen sayen magani.

    Wani mai fama da lalurar da ke zaune a jihar Nasarawa ta tsakiyar Najeriya, Zubairu Tanko Sulaiman, ya bayyana wa BBC irin halin da ya shiga sakamakon kamuwa da cutar.

  18. Liverpool na tattaunawa da Salah kan sabon kwantiragi

    Mahukuntan ƙungiyar Liverpool na tattaunawa da Mohammed Salah kan yiwuwar amincewa da sabon kwantiragi.

    Sai dai ba a cimma matsaya tsakanin Salah da mahukuntan ba kawo yanzu.

    Ƙungiyoyi da dama a Turai da kuma Saudiyya na ci gaba da zawarcin ɗan wasan na ƙasar Masar.

  19. Ƴan bindiga sun kashe sojojin Najeriya biyu a jihar Abia

    Rundunar sojin Najeriya ta Operation UDO KA ta ce an kashe jami'ai guda biyu a wani shingen bincike a kan hanyar Umuahia-Owerri da ke jihar Abia.

    Wata sanarwa da Laftanar Kanar Jonah Unukhalu na rundunar ya fitar, ya ce lamarin ya afku ne ranar Laraba, inda ya ce suna zargin ƴan awaren Biafra da kuma takwarorinsu na ESN da kai harin.

    Sanarwar da sojojin suka fitar ta ce dakarun sun samu nasarar daƙile harin da aka kai, abin ya sa wasu daga cikin maharan suka tsere da raunuka har da barin motocinsu a wurin.

    "Abin takaici shi ne yayin artabu da waɗanda suka kai harin, sojojin mu biyu suka mutu," in ji sanarwar sojojin.

    Wannan shi ne hari na biyu kan shingen binciken sojoji a jihar ta Abia, tun bayan wanda ya lakume rayukan sojoji biyar a watan Mayu.

  20. Nijar ta buƙaci Rasha ta saka hannun jari a fannin samar da ma’adinan Uranium

    Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun buƙaci kamfanonin Rasha da su saka hannun jari a fannin samar da ma’adinan Uranium da sauran albarkatun ƙasa.

    Ministan ma'adinan ƙasar Usman Abarshi, shi ya yi wannan kira a daidai lokacin da ake ci gaba da takaddama tsakanin Nijar da kamfanin Orano na ƙasar Faransa.

    Kamfanin na Orano ya dakatar da fitar da sinadarin Uranium a ƙasar ne a watan da ya gabata yayin da dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da gwamnatin mulkin sojin Nijar ɗin.

    Ministan ya ce sun riga sun gana da kamfanonin ƙasar Rasha domin su zo su zuba jari a fannoni daban-daban.

    Kalaman na minista na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashe da dama ke yanke hulɗar dangantaka da Faransa, inda wasu suka ga Rasha da sauran ƙasashe.

    Gwamnatin mulkin sojin Nijar ɗin ta sha alwashin yin garambawul ga dokokin da kamfanonin ƙasashen waje ke aiki da su wajen haƙo albarkatun uranium a ƙasar.

    Tun da farko dai, kamfanin na Orano ya yi Alla-wadai da matakin janye masa izinin haƙar ma'adinai da gwamnatin mulkin sojin Nijar ta yi a watan Yuli, inda ya kasance ɗaya daga cikin manyan wurare da kamfanin yake aiki a duniya.