Ambaliya na ci gaba da ɗaiɗaita birnin Malaga na Sifaniya
An tafka ruwan sama da ba a taɓa ganin irin sa ba cikin shekaru 35 a yankin Malaga na Sifaniya.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke fama da zagaye na biyu na ambaliyar ruwa cikin ƙasa da makonni uku.
Koguna sun cika sun batse, lamarin da ya tilastawa dubbai fice wa daga gidajensu.
A daren jiya an kwashe mutane 3000 daga gidajensu a yankin gaɓar teku, inda ambaliyar ta shafe titunan birnin Malaga.
Sai dai lamarin bai yi munin wanda aka gani a Valencia makonni biyu da suka wuce ba, inda sama da mutane 220 suka mutu.