Babu wata matsala tsakanina da Lukman, in ji Victor Boniface

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan gaba na Najeriya Victor Boniface ya ce babu wata matsala tsakaninsa da abokin wasansa Ademola Lukman bayan Atalanta ta doke Bayer Leverkusen a wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai ta Europa League.
Lukman ne ya ci wa Atalanta ƙwallayen uku rigis da ta doke Leverkusen a wasan da suka buga a watan Yuni, wanda shi ne karon farko da duka 'yan wasan na Najeriya suka buga wasan ƙarshe a gasar zakarun Turai.
Sai dai bayan da Boniface ya gaza buga wa Najeriya wasa a gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2023 saboda rauni, yanzu 'yan wasan biyu sun haɗu a sanasanin Super Eagles ɗin domin buga wasan neman shiga Kofin Duniya na 2026.
"Ɗan Najeriya ne shi, ni ma ɗan Najeriya ne. Ɗan'uwana ne shi, ya je ne don ya yi nasara ni ma na je don na yi nasara, ba abin da ya dame ni," kamar yadda Boniface ya shaida wa BBC.
"Amma dai a ƙarshe su ne suka yi nasara kuma ina taya shi murna."
Anjima a yau Najeriya za ta buga wasan farko cikin biyu tare da Afirka ta Kudu a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom, inda za ta buga na biyun da Benin a Ivory Coast ranar Litinin.

