Nigeria 1-1 South Africa: Wasan neman shiga Kofin Duniya

Wannan shafi na kawo muku rahotonni kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni na ranar 6 ga watan Yuni, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Najeriya ta kai hari, Nigeria 0-1 South Africa

    Kyaftin Najeriya, Wilfred Ndidi, ya ɗaɗata ƙwallo daga wajen yadi na 18, amma gola Romwen Williams ya cafke ta.

  2. An kusa ƙara wa Najeriya, Nigeria 0-1 South Africa

    Ɗan wasan gaba na Afirka ta Kudu, Zwane ya kusa ƙara wa Najeriya ba don Nwabali ya fito ya tare shi ba. Da kyar Bassey ya fitar da ƙwallon zuwa bugun kwana.

  3. Yalon kati ga Afirka ta Kudu, Nigeria 0-1 South Africa

    An bai wa Modiba na Afirka ta Kudu katin gargaɗi.

  4. GOAL, '29 Nigeria 0-1 South Africa

    Zwane ya yi kwance-kwance, ya yayyaga 'yan bayan Najeriya kuma ya jefa ƙwallon a ragar Nwabali ba tare da wata matsala ba.

    Ƙwallo ce mai ƙayatarwa domin sai da ya bayar da mutum biyu kafin ya shauɗa ta raga, kuma duk da Nwabali ya kai mata cafka hakan bai sauya komai ba.

  5. Najeriya ta samu bugun tazara, Nigeria 0-0 South Africa

    Najeriya za ta buga bugun tazara mai haɗari bayan an kayar da Lookman

  6. An bugo wa Najeriya tirke, Nigeria 0-0 South Africa

    Themba Zwane na Afirka ta Kudu ya ɗaɗa ƙwallo mai haɗari daga bugun tazara kuma ta bigi tirken sama ta yi waje.

    Wasan ya fara zafi da gaske

  7. Katin gargaɗi ga Najeriya, Nigeria 0-0 South Africa

    An bai wa Osayi Samuel katin gargaɗi saboda ƙeta.

  8. Bugun tazara mai haɗari ga Afirka ta Kudu, Nigeria 0-0 South Africa

    Osayi Samuel ya kayar da ɗan wasan Afirka ta Kudu a kusa da da'irar yadi na 18 na Najeriya.

  9. Satar gida, Nigeria 0-0 South Africa

    Ɗan wasan Afirka ta Kudu, Rayners ya yi satar gida - amma ba don haka ba da tuni labari ya sha bamban.

  10. Lookman ya ɗaɗa ƙwallo, Nigeria 0-0 South Africa

    Ademola Lookman na Najeriya ya ɗaɗa ƙwallo daga ɓangaren hagu, amma ta yi faɗi zuwa waje.

  11. Afirka ta Kudu ta yi satar gida, Nigeria 0-0 South Africa

    Ɗan wasan Afirka ta Kudu ya yi satar gida

  12. An take wasa, Nigeria 0-0 South Africa

  13. 'Yan wasan da Afirka ta Kudu za ta fara da su, Nigeria v South Africa

    Gola

    Williams

    'Yan baya

    Mudau, Ngezana, Mvala, Modiba, Mokuena

    'Yan tsakiya

    Sithole, Zwane, Tau

    'Yan gaba

    Mokwana, Rayners

  14. 'Yan wasa 11 da Najeriya za ta fara da su, Nigeria v South Africa

    Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta fitar da jerin 'yan wasan da za ta fara fuskantar Afirks ta Kudu da su. Su ne:

    Gola

    Nwabali

    'Yan Baya

    Tanimu, Ajayi, Bassey, Samuel

    'Yan tsakiya

    Ndidi, Iwobi, Bashiru

    'Yan gaba

    Lookman, Iheanacho, Onuachu

    'Yan benci:

    Moffi, Boniface, Onyeka, Abdullahi, Chukwueze, Awaziem, Olawoyin, Ismaila, Onyedika.

    Najeriya

    Asalin hoton, NFF

  15. Atasayen Super Eagles na ƙarshe, Nigeria v South Africa

    Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta kammala atasayen tunkarar Afirka ta Kudu a wasan neman shiga Kofin Duniya na 2026 a safiyar yau.

    Nan gaba kaɗan za a take wasan fallen farko a garin Uyo na Najeriya, kafin ta ziyarci Afirka ta Kudu a 2025.

    Super Eagles

    Asalin hoton, NFF

    Super Eagles

    Asalin hoton, NFF

  16. Atasayen Bafana Bafana na ƙarshe

    Bafana Bafana

    Asalin hoton, SAFA

    'Yan wasan tawagar Bafana Bafana ta Afirka ta Kudu sun yi atasayensu na ƙarshe a safiyar yau kafin karawar da za su yi da Najeriya.

    Awa biyu da rabi kawai suka rage kafin fafatawar da za a yi a filin wasa na Godswill Akpabio da ke birnin Uyo na jihar Akwa Ibom.

    Bafana Bafana

    Asalin hoton, SAFA

  17. Jamie Vardy ya tsawaita zamansa a Leicester City

    Jamie Vardy

    Asalin hoton, Reuters

    Ɗan wasan gaba na Leicester City Jamie Vardy ya saka hannu kan yarjejeniyar ƙarin shekara ɗaya da ƙungiyar mai buga gasar Premier League.

    Vardy ya fara taka wa Leicester leda tun 2012 kuma ya ci ƙwallo 190 cikin wasa 464.

    Ɗan wasan mai shekara 37 ya lashe kofin Premier da ƙungiyar a kakar 2015-16.

    "Na daɗe ina faɗa cewa shekaru lamba ce kawai," a cewar kyaftin ɗin na Leicester.

    "Ina jin ƙafafuwana lafiya ƙalau shi ya sa na yanke shawarar cigaba har sai sun ce: 'Shikenan, an gama'. Na san irin wannan ranar na zuwa amma dai ba yanzu ba."

    Tsohon ɗan wasan Ingilan ya kuma lashe kofin FA, da Community Shield, da kofin Championship biyu a Leicester, wanda ya bai wa ƙungiyar damar haurowa gasar Premier League a kaka mai zuwa.

  18. Murnar doke Mali..., Mali 1-2 Ghana

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
  19. Masar ta doke Burkina a wasan neman zuwa Kofin Duniya, Egypt 2-1 Burkina Faso

    'Yan wasan Masar

    Asalin hoton, @EgyptNT_EN

    Tawagar The Pharaohs ta Masar ta doke Burkina Faso a wasan neman gurbin gasar Kofin Duniya ta 2026 a daren jiya.

    Ɗan wasan gaba Trezeguet ne ya ci wa Masar ƙwallayen biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci, inda Lassina Traore ya farke wa Burkina ƙwallo ɗaya jim kaɗan bayan dawowa daga hutun.

    Da wannan sakamako, Masar ta ci gaba da zama a mataki na ɗaya da maki 9, sai Guinea-Bissau ta biyu da maki biyar, da kuma Burkina a mataki na uku da maki huɗu.

    Ranar Litinin Masar ɗin za ta shawo ta da Guinea-Bissau a wasa na biyu na wannan zagayen.

  20. Ghana ta ƙara matsa ƙaimi a yunƙurin zuwa Kofin Duniya, Mali 1-2 Ghana

    'Yan wasan Ghana

    Asalin hoton, Black Stars

    Ghana ta doke Mali 2-1 a wasan neman shiga gasar Kofin Duniya ta 2026 da suka buga ranar Alhamis da dare.

    Kamory Doumbia ne ya fara ci wa Mali ƙwallo ana dab da tafiya hutun rabin lokaci, kafin Ernest Nuamah ya farke ta minti 13 da dawowa daga hutun.

    Sai bayan minti huɗu da cikar lokaci tauraron ɗan wasa Jordan Ayew ya ci wa Ghana ƙwallon nasarar, abin da ya sa magoya baya ɓarkewa da sowar murna.

    Sakamakon ya mayar da Ghana ta biyu a saman teburi da maki shida, yayin da Mali ke biye mata da maki huɗu. Sai kuma Comoros ta ɗaya mai maki shida kafin ta buga wasanta da Madagascar a yammacin yau.

    Sai a ranar Litinin Ghana za ta karɓi baƙuncin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a wasa na gaba a birnin Kumasi.