Labarin wasanni daga 18 zuwa 30 ga watan Janairun 2026
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Lahadi 18 zuwa 30 ga Janairun 2026
Rahoto kai-tsaye
Mohammed Abdu
, Daga Jaridu
Asalin hoton, Getty Images
Crystal Palace ta yi watsi da tayin farko na Juventus kan ɗanwasan gaba na Faransa Jean-Philippe Mateta. (Calciomercato - in Italian)
Barcelona na hangen ɗauko kocin Arsenal Mikel Arteta ko na Paris St-Germain Luis Enrique domin jagorantar ƙungiyar a nan gaba, amma tana son Hansi Flick ya ci gaba da aikinsa har tsawon lokaci. (Diario Sport - in Spanish)
Bournemouth da West Ham na son ɗanwasan Real Betis da Spain Pablo Garcia, mai shekara 19, kuma a shirye suke su biya fam miliyan 26. (Fichajes - in Spanish)
Da ƙyar ne Glasner zai kammala kakar nan a Palace - Shearer, Crystal Palace
Asalin hoton, Getty Images
Tsohon ɗan wasa, Alan Shearer ya ce zai yi mamaki matuka
idan Oliver Glasner bai bar aikin kociyan Crystal Palace a makon da muka shiga
ba.
Wannan ya biyo bayan furucin Glasner da ya ce yana jin an yi
watsi da shi da ƴan wasan ƙungiyar gabaki daya daga bangaren shugabanci.
Palace ta sha kashi 2–1 a gidan Sunderland ranar
Asabar a Premier League, kuma yanzu sun shafe wasa goma a jere ba tare da nasara ba.
Swantek ta kai zagaye na biyu a Australian Open, Australian Open
Asalin hoton, Getty Images
A rana ta biyu a gasar Australian Open, Iga Swiatek ta doke Yuan Yue a wasa da ta fuskanci kalubale.
Tsohon zakaran gasar, Stan Wawrinka, ya tsallaka zuwa zagaye na biyu a karon ƙarshe da yake buga Australian Open.
Ita kuwa Coco Gauff, ta yi waje da Kamilla Rakhimova da cin 6–2, 6–3.
Dukkan ƴan Birtaniya biyu, Fran Jones da Jacob Fearnely, sun kasa kaiwa zagaye na biyu.
Afcon: CAF za ta yanke hukunci bayan kallon bidiyon wasan karshe, Afcon Morocco 2025/26
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF) ta ce za ta duba dukkan bidiyon wasan ƙarshe a gasar cin kofin Afirka (AFCON) da aka buga daren jiya Lahadi, kafin ta yanke hukunci kan yiwuwar ɗaukar mataki kan tawagar Senegal da ta lashe kofin.
Yawancin ƴan wasan Senegal sun fice daga filin wasa a matsayin zanga-zanga bayan da aka bai wa Morocco bugun fenariti.
Shugaban FIFA, Gianni Infantino, ya yi Allah-wadai da halayen ƴan wasan Senegal da wasu daga cikin masu horas da su, inda ya ce tashin hankali da ficewa daga fili ba su da gurbi a harkar ƙwallon ƙafa.
A ƙarshe dai Senegal ta yi nasara da ci 1–0 bayan ƙarin lokaci. Wannan ne karo na biyu da Senegal ke lashe kofin AFCON a tarihinta, bayan na farko a 2021.
Hukumar ƙwallon ƙafar Afirka ta yi tur da halayyar ƴan wasan Senegal
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar
kula da ƙwallon ƙafa ta Afirka, CAF ta nuna rashin jin daɗin kan abin da ya
faru a lokacin wasan ƙarshe na Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka ta 2025 da aka gudanar
ranar Lahadi a Moroko.
Ƴan
wasan Senegal sun fusata da alƙalin wasa Jean-Jacques Ndala bayan ya bai wa
Moroko bugun fenariti a filin wasa na Yarima Moulay Abdellah da ke Rabat, a
ƙasar Moroko.
Wannan
ya kai ga ficewar wasu daga cikin ƴan wasan daga fili, bayan alƙalin ya
tabbatar da matakin nasa bayan sake duba abin da ya faru a faifai.
A
cikin wata sanarwa da CAF ta fitar yau Litinin a shafinta na intanet, ta ce “CAF
ta yi tur da wasu munanan ɗabi’un wasu ƴan wasa da jami’ai a lokacin wasan
ƙarshe na Gasar Cin Kofin Afirka tsakanin Senegal da Moroko a birnin Rabat, a
daren da ya gabata.
Sanarwar
ta ƙara da cewa “Hukumar CAF na duba dukkanin hotunan bidiyon wasan kuma za ta
miƙa lamarin ga hukumomin da suka gabata domin ɗaukar matakin da ya dace a kan
duk wanda aka samu da laifi.”
Daga
baya ƴan wasan na Senegal sun koma filin wasa, inda aka ci gaba da karawar har
lokacin da aka tashi, inda Senegal ɗin ta lashe kofin bayan doke mai masaukin
baƙi Moroko da ci 1-0.
Akwai abin da muka rasa a yanzu a Liverpool - Van Dijk, Liverpool
Asalin hoton, Getty Images
Kyaftin ɗin Liverpool, Virgil van Dijk, ya ce akwai “wani abu da suka rasa” a cikin ƙungiyarsu bayan sun tashi 1–1 da Burnley da ke fama da matsala a wasan Premier League da suka kara ranar Asabar a Anfield.
Liverpool, mai rike da kofin gasar, wadda ta yi canjaras huɗu a jere Premier League, magoya bayanta sun yi ta yi ƴan wasa ihu bayan tashi daga karawar.
Florian Wirtz ne ya ci wa Liverpool ƙwallon farko — mintuna 10 baya Dominik Szoboszlai ya ɓarar da fanariti — amma Marcus Edwards ne ya farke wa Burnley.
“Fushi da takaici shi ne kalmar da take zuciyata,” in ji Van Dijk..
“Muna da sauran awa 48 domin mu tantance kanmu tare da kociyoyinmu, za mu yi nazari, sannan dole ne mu ɗauki mataki.
“Zan ce a halin yanzu akwai wani abu da muka rasa, kuma muna son mu san ko menene.”
Wannan ne karo na farko tun kakar 1980–81 da Liverpool ta kasa doke kowacce daga cikin ƙungiyoyin da hau Premier League a wasannin da ta yi da su a Anfield.
A halin yanzu tana da tazarar maki bakwai a bayan Aston Villa da ke matsayi na uku, wacce kuma tana da wasa ɗaya ranar Lahadi da Everton a Villa Park..
Liverpool za ta fuskanci wasa mai matukar wahala a gasar Champions League da Marseille ranar Laraba, kuma Van Dijk mai shekaru 34 ya ce Liverpool na bukatar inganta wasanninta sosai.
Liverpool na shiga wasan tana matsayi na tara a teburin Champions League, inda ƙungiyoyi takwas ne kai tsaye ke zuwa zagayen gaba.
Marseille na karkashin jagorancin tsohon kocin Brighton, Roberto de Zerbi, kuma Van Dijk ya ce yana sa za su fuskanci kalubale a karawar.
Wa zai lashe Afcon tsakanin Mane ko Hakimi?, Afcon Morocco 2025/26
Asalin hoton, Getty Images
Morocco za ta yi ƙoƙarin kawo ƙarshen jiran da ta yi na shekara 50 tana dakon kambun nahiyar Afrika na biyu a lokacin da za ta kara da Senegal a wasan ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka na 2025 a ranar Lahadi.
Amma kuma Atlas Lions za su yi ƙoƙarin samun kyakkyawan sakamako bayan ɗimbin jarin da ƙasarsu ta sanya a fannin harkar ƙwallon ƙafa.
A wasan da za a yi a birnin Rabat (19:00 agogon GMT) za a ga manyan tawagogin ƙwallon ƙafa biyu na Nahiyar, inda ƴan Arewacin Afirka ke matsayi na 11 a duniya, sai kuma Teranga Lions a matsayi takwas a ƙasa da su.
Chelsea a shirye take ta lale fam miliyan 43 domin ɗauko ɗanwasan baya na Faransa Jeremy Jacquet, amma Rennes ta nace sai an biya ta fam miliyan 52 (£52m). (RMC Sport - in French)
Napoli na son karɓo ɗanwasan gaba na Jamhuriyyar Ireland Evan Ferguson, mai shekara 21, wanda ke taka leda a matsayin aro a Roma daga Brighton, idan har ɗanwasan gaba na Netherlands Noa Lang, mai shekara 26, ya tafi. (Corriere dello Sport - in Italian)
Bournemouth ta yi nisa da tattaunawa da Lazio kan karɓar aron golan Girka Christos Mandas. (Sky Sports)
Newcastle ta shigar da buƙatarta kan ɗanwasan baya na Netherlands da Inter Milan Stefan de Vrij, mai shekara 33. (Football Insider)
Aston Villa ta tattauna da Club Brugge kan batun sayen Raphael Onyedika, mai shekara 24, amma Galatasaray ce kan gaba wajen buƙatar ɗanwasan tsakiyar na Najeriya. (Sacha Tavolieri)
Watakila Tottenham ta kori Thomas Frank, Tottenham
Asalin hoton, Getty Images
Kocin Tottenham, Thomas Frank, na fuskantar matsin lamba a ƙungiyar, inda ake tunanin ko lokaci ya yi da za a kawo karshen wa’adinsa na watanni bakwai da ya shafe yana jagoranci.
Dan asalin Denmark ya fara aikinsa a Tottenham ne da rashin sakamako masu kyau tun bayan naɗa aikin kan fara kakar bana.
BBC Sport ta fahimci cewa a kalla wani mamba daga cikin shugabannin zartarwa ya fito fili yana goyon bayan ra’ayin kawo karshen wa’adin Frank a ƴan makonnin baya-bayan nan.
Duk da cewa ƙungiyar na ci gaba da marawa Frank baya ga matsalolin da Tottenham ke fuskanta a wannan kakar, rashin nasarar da suka sha a gida a hannun West Ham ranar Asabar ya sanya matsayinsa cikin hadari, yayin da manyan shugabannin ƙungiyar ke duba ko ya dace su dauki mataki nan take ko kuma su ba shi dama ya gyara lamura.
Wannan rashin nasara ta bar Tottenham a matsayi na 14 a teburin Premier League, inda suka samu ci wasa bakwai kacal daga 22 da suka buga a kakar bana, kuma manyan magoya baya sun riga sun dawo daga rakiyar tsohon kociyan Brentford.
Frank ya koma Tottenham ne a watan Yuni, bayan sallamar Ange Postecoglou.
Tottenham ta yi nasara ɗaya kacal a wasa takwas da suka gabata, kuma ta fita daga dukkan gasar kofuna na cikin gida.
A halin yanzu tana matsayi na 11 a gasar Champions League, kuma za ta kara da Borussia Dortmund a wannan makon a wasa mai matukar muhimmanci ga burinta na tsallakawa zuwa zagayen na biyu a gasar ta zakarun Turai.
, Daga Jaridu
Asalin hoton, Getty Images
Aston Villa da Tottenham da Manchester United na rubibin ɗanwasan baya na Juventus Pierre Kalulu, mai shekara 25. (Calciomercato - in Italian)
Manchester United na son ɗauko ɗanwasan tsakiya na Portugal Ruben Neves, mai shekara 28, amma Al-Hilal na son fam miliyan 20. (Football Insider)
Liverpool ta sa wa ranta ɗanwasan tsakiya na Real Madrid da Faransa Eduardo Camavinga, mai shekera 23. (Fichajes - in Spanish)
West Ham na tattaunawa da Barcelona kan yiyuwar sayen Marc-Andre ter Stegen, mai shekara 33, amma ga alama golan na Jamus na shirin zuwa Girona. (Teamtalk)
Ɗanwasan gaba na Ingila Jadon Sancho, wanda ke taka leda a matsayin aro a Aston Villa, zai iya sake komawa Borussia Dortmund karo na uku inda ƙungiyar ta Jamus ke son ɗauko shi idan har kwangilar shi ta kawo ƙarshe a Manchester United. (Fichajes - in Spanish)
Jerin kasashen da suka lashe gasar cin kofin Afirka a tarihi, Afcon Morocco 2025/26
1982: Ghana 1 Libya 1 -- Fenariti. Ghana ta ci 7-6
1984: Cameroon 3 Nigeria 1
1986: Egypt 0 Cameroon 0 -- Fenatiti. Masar ta ci 5-4
1988: Cameroon 1 Nigeria 0
1990: Algeria 1 Nigeria 0
1992: Ivory Coast 0 Ghana 0 -- Fenariti. Ivory Coast ta ci 11-10
1994: Nigeria 2 Zambia 1
1996: South Africa 2 Tunisia 0
1998: Egypt 2 South Africa 0
2000: Cameroon 2 Nigeria 2 -- Fenariti. Kamaru ta ci 4-3
2002: Cameroon 0 Senegal 0 -- Fenariti. Kamaru ta ci 3-2
2004: Tunisia 2 Morocco 1
2006: Egypt 0 Ivory Coast 0 -- Fenariti. Masar ta ci 4-2
2008: Egypt 1 Cameroon 0
2010: Egypt 1 Ghana 0
2012: Zambia 0 Ivory Coast 0 -- Fenariti. Zambia ta ci 8-7
2013: Nigeria 1 Burkina Faso 0
2015: Ivory Coast 0 Ghana 0 -- Fenariti. Ivory Coast ta ci 9-8
2017: Cameroon 2 Egypt 1
2019: Algeria 1 Senegal 0
2022: Senegal 0 Egypt 0 -- Fenariti. Senegal ta ci 4-2
2024: Ivory Coast 2 Nigeria 1
Wa zai lashe na bana?
Kociyan Senegal ya koka da rashin tsaro ga tawagar kasar, Afcon Morocco 2025/26
Asalin hoton, Getty Images
Kocin tawagar Senegal ya soki karancin tsaro ga ƴan wasansa lokacin da suka isa Rabat, babban birnin Morocco, gabanin wasan karshe na ranar Lahadi da za su buga da mai masaukin baƙi, Morocco a gasar cin kofi nahiyar Afirka.
Bidiyoyi da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda ƴan wasan Senegal suna cikin firgishi a lokacin da dubban magoya baya ke son zuwa wajen motarsu. Pape Bouna Thiaw ya wannan abin bai kamata ba, domin babu jami'an tsaro kuma komai zai iya faruwa.
Har yanzu masu shirya gasar ba su fitar da wata sanarwa ba kan lamarin.
Senegal da Morocco ba su taba haduwa da juna ba a gasar Kofin Afirka ta Kwallon Kafa a baya ba.
, Daga Jaridu
Asalin hoton, Getty Images
Arsenal na nazarin ɗauko ɗanwasan baya na Jamus da Eintracht Frankfurt Nathaniel Brown da kuma ɗanwasan tsakiya na Ivory Coast Ousmane Diomande. (Caught Offside)
Liverpool ta mayar da hankali kan buƙatar ɗanwasan baya na Inter Milan da Italiya Alessandro Bastoni, mai shekara 26, bayan gaza samun ɗanwasan Crystal Palace' Marc Guehi da ke shirin zuwa Manchester City. (Teamtalk)
Juventus ta matsa kan ɗanwasan ɗanwasan gaba na Crystal Palace Jean-Philippe Mateta, mai shekara 28, inda ta tattauna da wakilan ɗanwasan na Faransa a ranar Juma'a. (Mail)
Najeriya ce ta uku a Afcon karo na takwas jimilla, Afcon Morocco 2025/26
Asalin hoton, Getty Images
Najeriya ta kammala gasar cin kofin Afirka a Morocco a matsayi na uku bayan doke Masar a bugun fenariti a wasan neman mataki na uku da na huɗu, bayan da suka tashi babu ci ranar Asabar.
Mai tsaron ragar Najeriya, Stanley Nwabali, ya yi bajinta a bugun daga kai sai mai tasron raga, wanda ya buge fenaritin Mohamed Salah da Omar Marmoush na Masar, hakan ya sa Najeriya ta samu nasara da cin 4–2.
Da wannan sakamakon na nufin cewa Najeriya ta lashe dukkan wasa takwas na neman matsayi na uku da ta taba bugawa a Afcon — wani tarihi da babu wata kasa da ta yi a tarihin gasar.
Masu masaukin baki, Morocco, za su kara da Senegal a wasan karshe da za a buga a Rabat a daren Lahadi.
''Waɗanda ba sa ƙyaunar Real Madrid ne suka yi mata ihu''
Asalin hoton, Getty Images
Sabon kocin Real Madrid, Alvaro Arbeloa, ya ce zanga-zangar magoya baya a filin Bernabeu ta fito ne daga “mutanen da ba sa son” ƙungiyar, bayan da ta doke Levante, inda hakan ya sa ta rage tazarar maki tsakani da Barcelona mai jan ragamar teburin La Liga zuwa ɗaya kacal.
Magoya bayan Madrid sun ɗaga fararen kyalle kafin a fara wasan ranar Asabar, sannan suka rika yin ihu da bushe-bushe suna nuna rashin jin daɗi ga ƴan wasa — musamman Jude Bellingham da Vinicius Jr da Federico Valverde — tare da shugaba, Florentino Perez.
“Ina sane da tushen waɗannan kiraye-kirayen. Sun fito ne daga mutanen da ba sa son Real Madrid,” in ji Arbeloa.
“Abin alfahari ne samun shugaba wanda shi ne mutum mafi muhimmanci a tarihin wannan Real Madrid, tare da Santiago Bernabeu.
Tsohon ɗan bayan Liverpool da Real Madrid — wanda ya maye gurbin Xabi Alonso a matsayin koci a ranar Litinin — shi ma an yi masa ihu a lokacin gasar La Liga.
“Kullum ina girmama Bernabeu, ni ma an yi mini ihu sau da yawa. Wannan makon abin takaici ne a gare mu, kuma magoya baya suna da hakkin bayyana fushinsu,” Arbeloa ya kara da cewa.
“Ba na ganin za a ci gaba da yi wa Vini ihu nan gaba. Ina girmama magoya bayan Bernabeu. Bukatunsu da matsin lambar da suke yi suna karfafa gwiwar ƴan wasa a koda yaushe.”
Bayan rashin nasara da Real Madrid ta yi a gasar Copa del Rey a hannun ƙungiyar da ke mataki na biyu Albacete a ranar Laraba, Arbeloa ya dawo da Mbappe da Bellingham cikin jerin ƴan wasan farko a wasansa na farko a La Liga tun bayan maye gurbin Xabi Alonso.
Barkanmu da shiga sharhi da bayanan wasanni
Jama'a barkanmu da shiga shirin sharhi da bayanan wasanni kai tsaye tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw.
Za ku iya tafka muhawara a shirin ko bayar da gudunmuwa a BBCHausa Facebook.