Mateta ya bukaci barin Crystal Palace, Crystal Palace

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan tawagar Faransa, Jean-Philippe Mateta ya sanar da Crystal Palace cewa yana son barin ƙungiyar, sakamakon da yake ta samun masu son zawarcinsa daga wasu ƙungiyoyin Premier League da na Turai.
Mateta yana da yarjejeniyar watai 18 da ta rage masa a Selhurst Park, kuma a halin da ake ciki ba zai sanya hannu kan ci gaba da taka leda a ƙungiyar ba.
Babbar ƙungiyar Italiya, Juventus tana ta ƙoƙarin ɗaukar ɗan wasan a wannan watan, amma har yanzu ba su cimma matsaya ba da Palace wadda take nukatar kusan fam miliyan 40.
Aston Villa, wadda ta dade tana sha’awar Mateta, ita ma ta nuna sha’awar ɗaukar shi a wannan watan.
Da yake magana a makon da ya gabata, kocin Palace Oliver Glasner ya ce suna nan suna jiran tayi mai tsoka da za a yi wa Mateta.
Palace, wadda ta lashe FA Cup a watan Mayu, ta sayar da fitaccen ɗan wasan, Eberechi Eze ga Arsenal kan fara kakar bana, sannan kuma ta sayar da kyaftin, Marc Guehi a wannan watan Janairu, wanda ya koma Manchester City kan fam miliyan 20.
Glasner, wanda ya sanar a makon da ya gabata cewa zai bar Palace a ƙarshen kakar bana, ya yi suka ga shugabancin Palace bayan shan kashi a hannun Sunderland ranar Asabar, inda ya ce an “yi watsi da ƙungiyar” ta hanyar tsarin ɗaukar ‘yan wasan ƙungiyar ɗin.
Palace ta fice daga gasar FA Cup a hannun wadda da ba ta cikin manyan ƙungiyoyin Ingila, Macclesfield, a farkon wannan watan, a ɗaya daga cikin manyan abubuwan mamaki a tarihin gasar.


















