Najeriya ta kai zagaye na biyu bayan cin Tunisiya 3-2

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku bayanai kan wasan Najeriya da Tunisia a gasar kofin nahiyar Afirka ta 2025 da ake yi a Moroko.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Teburin rukuni na uku kafin wasan Najeriya da Tunisia, Najeriya da Tunisiya

    Afcon

    Asalin hoton, BBC Sport

  2. Bajintar da Tunisiya ke yi a Afcon

    Afcon

    Asalin hoton, Getty Images

    • Tunisiya ta fara gasar da nasara 3–1 a kan Uganda.
    • Ellyes Skhiri ne ya ci kwallon farko a Tunisiya, wadda ita ce ta 100 da suka ci a wasannin AFCON.
    • Tunisiya ta zama kasa ta shida da ta kai ga zura kwallaye 100 a raga a AFCON, daga baya Aljeriya ta zama ta bakwai da yin wannan bajintar.
    • Ƙwallon da Skhiri ya ci bayan minti 10 na nufin cewa Masar ta ci (22) da Najeriya (16) kaɗai ne suka fi Tunisiya mai (12) yawan cin ƙwallaye a cikin minti 10 da farko wasa a AFCON.
    • Wannan shi ne karon farko da Tunisiya ta ci ƙwallo a cikin minti 10 na farko da fara wasan farko a rukuni tun lokacin Issam Jemâa a karawa da Senegal a 2008.
    • Skhiri ya ci ƙwallonsa ta farko a AFCON ne a wasansa na 16 a gasar.
    • Elias Achouri ya ci ƙwallo ta huɗu da ta biyar a tarihin wasanninsa a Tunisia.
    • Achouri ya zama ɗan Tunisiya na farko da ya ci ƙwallo biyu a wasa ɗaya a AFCON tun bayan Wahbi Khazri a fafatawa da Mauritania a 2021.
    • Nasarar da suka samu a kan Uganda ta kawo ƙarshen wasa huɗu ba tare da nasara ba ga Tunisiya a AFCON, wadda ta yi canjaras biyu aka doke ta biyu daga ciki.
    • Haka kuma ta kawo ƙarshen wasa huɗu ba tare da nasara ba a wasannin rukuni a AFCON, tun bayan da ta doke Mauritania a 2021.
  3. Wasu ƙwazon da Super Eagles ke yi a Afcon, Najeriya da Tunisia

    Afcon

    Asalin hoton, ge

    • Super Eagles ta fara da cin Tanzania 2–1 a wasan farko a rukuni a Morocco.
    • Kenan karo na 14 da take fara yin nasara a wasan farko a cikin rukuni a Afcon.
    • Ba a doke Najeriya ba a wasa bakwai baya a cikin rukuni a Afcon, ta yi nasara shida da canjaras ɗaya, tun bayan da Madagascar ta yi nasara a kanta a 2019.
    • Super Eagles ta yi nasara uku a Afcon a karawar cikin rukuni da cin kodai ƙwallo ɗaya ko tazarar ɗaya.
  4. Sau nawa aka kara tsakanin Najeriya da Tunisia?

    Afcon

    Asalin hoton, Getty Images

    Sun fuskanci juna sau 21 jimilla, inda Najeriya ta ci wasa biyar, Tunisia ta yi nasara shida da canjaras 10, Najeriya ta ci ƙwallo 21 aka zura mata 26 a raga a tsakaninsu.

    Wannan shi ne karo na bakwai da za su kara a Afcon:

    Najeriya ta samu nasara uku, Tunisia tana da ɗaya da canjaras biyu, Super Eagles ta ci ƙwallo tara aka zura mata biyar a raga a tsakaninsu.

    Tarihin fafatawar da suka yi a Afcon:

    Ranar 16 ga watan Maris 1978, Accra

    • Najeriya 2-0 Tunisia

    Super Eagles ce ta yi ta uku, wadda aka baiwa ƙwallo 2-0, bayan da Tunisia ta ƙi karasa wasan tun daga minti na 42 a lokacin suna 1-1.

    Ranar 23 ga watan Janairun 2000, Legas wasan cikin rukuni

    • Najeriya 4-2 Tunisia

    Ranar 11 ga watan Fabrairun 2004, Radès (Zagayen daf da karshe)

    • Tunisia 1-1 Najeriya

    (Tunisia ta yi nasara 5–3 a bugun fenariti)

    Ranar 4 ga watan Fabrairun 2006, Port Said (Zagayen kwata-fainals)

    • Najeriya 1-1 Tunisia

    (Najeriya ta yi nasara 6–5 a bugun fenariti)

    Ranar 17 ga watan Yulin 2019, Cairo (Wasan neman mataki na uku)

    • Tunisia 0-1 Najeriya

    (Ighalo ne ya ci ƙwallon a minti na uku da take leda)

    Ranar 23 ga watan Janairun 2022, Garoua (Zagayen tawaga 16)

    • Najeriya 0-1 Tunisia

    (Msakni ne ya ci ƙwallon a minti na 47)

  5. Benin ta ci wasa a karon farko a Afcon

    Afcon

    Asalin hoton, Getty Images

    Yohan Roche ne ya zura kwallon da ta ba Benin nasara ta farko a tarihin wasannin Kofin Nahiyar Afirka (AFCON), bayan ta doke Botswana da ci 1-0 a rukuni na huu a birnin Rabat ranar Asabar.

    Wannan nasarar ta bai wa Benin maki uku daga wasanninsu biyu a rukuni, bayan da aka yi kunnen doki tsakanin Senegal da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.

    Benin ta ci ƙwallon a minti na 28 lokacin ta hannun Roche.

    A ƙarshe Benin ta yi bikin samun nasara a gasar nahiyar ne a karon farko daga 16 da suka halarta tun bayan fara shiga Afcon a 2004, duk da cewa sun kai matakin kwata fainal a shekarar 2019.

    A tarihin wasanninsu na AFCON, sunyi kunnen doki biyar tare da shan kashi karo 10.

  6. Afcon 2025: Najeriya za ta kara da Tunisia, Najeriya da

    Afcon 2025

    Asalin hoton, Getty Images

    Super Eagles za ta buga wasa da Tunisia a karawa ta bibiyu a rukuni na uku ranar Asabar a gasar cin kofin Afirka da ake buga wa a Morocco.

    Dukkan tawagaogin biyu na fatan kaiwa zagaye na biyu a babbar gasar tamaula ta Afirka da za su kece raini a Complexe Sportif de Fes in Fes.

    Super Eagles ta yi nasarar doke Tanzania 2-1, yayin da Tunisia ta ci Uganga 3-1 a wasannin farko a karawar rukuni na uku.

    Shin sau nawa kasashen suka fuskanci juna a tsakaninsu?

  7. Barkanmu da shiga sharhi da bayanan wasanni

    Jama'a barkanmu da shiga shirin sharhi da bayanan wasanni kai tsaye tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw.

    Za ku iya tafka muhawara a shirin ko bayar da gudunmuwa a BBCHausa Facebook.