Najeriya ta kai zagaye na biyu bayan cin Tunisiya 3-2

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku bayanai kan wasan Najeriya da Tunisia a gasar kofin nahiyar Afirka ta 2025 da ake yi a Moroko.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Tunisiya tana da ƴan wasa fitattu - Chelle

    Erik Chelle

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin tawagar na Super Eagles, Erik Chelle ya amnice cewa Tunisia tawaga ce mai karfi kuma ya kammala duk shirye-shiryen da suka kamata don tabbatar da cewa sun yi nasara.

    Najeriya da Tunisia duk sun lashe wasanninsu na farko a wannan gasa inda Najeriya ta doke Tanzaniya da ci biyu da daya, ita kuma Tunisia ta doke Uganda da ci uku da daya.

    .

  2. An je hutun rabin lokaci, Najeriya 1-0 Tunisiya

  3. Osimhen ya ci wa Najeriya ƙwallo, Najeriya 1-0 Tunisiya

    Osimhen

    Asalin hoton, Getty Images

    Daga gefen hagu ne Lookman ya samu ƙwallo ya kuma bugo cikin gidan Tunisiya, inda Osimhen ya yi tsalle ya sa kai ta faɗa raga.

    Ƙwallon farko da ya ci kenan a Afcon a Morocco.

  4. , Najeriya 0-0 Tunisiya

    Tunisiya ta samu kwana ta hannunWilfred Ndidi ta kuma buga bata yi ƙyau ba, amma Najeriya ta cire ƙwallon ba tare da wani haɗari ba.

  5. , Najeriya 0-0 Tunisiya

    Wilfred Ndidi na Najeriya ya buga ƙwallo da kafar hagu amma ta yi sama ta fita waje.

  6. Tunisiya ta zubar da itma tata damar, Najeriya 0-0 Tunisiya

    Daga wajen Ali Abdi na Tunisiya ya buga ƙwallo da karfi da kafar hagu daga wajen da'ira ta 18 ta Najeriya, amma ta yi sama ta kuma yi faɗi ta yi waje.

  7. Super Eagles ta zubar da dama, Najeriya 0-0 Tunisiya

    Ƙwallo ce mai ƙyau Semi Ajayi ya sa mata kai a tsakiyar gidan Tunisia ta hannun hagu daga ƙwallon da ya samu ta wajen Ademola Lookman.

  8. Najeriya ce ke rike da wasan ita ce kan gaba a taka leda, Najeriya 0-0 Tunisiya

    Kawo yanzu an kusan cimma minti 30 da take leda, amma Super Eagles ce kan gaba a yawan taka leda da kaso 72.4 cikin 100, yayin da Tunisiya take da 27.6 cikin 100, amma har yanzu ba ci a wasan na hamayya.

  9. , Najeriya 0-0 Tunisiya

    Victor Osimhen na Super Eagles ya samu bugun tazara daga ɓangaren hagu.

  10. , Najeriya 0-0 Tunisiya

    Onyemaechi, wanda ke buga gurbin Zaidu Sanusi ya yi tsalle sama domin taɓa ƙwallo a lokacin kuma sai ya hau kan ɗan wasan Tunisiya, Mastouri, nan take alkalin wasa ya busa cewae an yi keta.

  11. Najeriya ta ci ƙwallo an ce da satar gida, Najeriya 0-0 Tunisiya

    Osimhen ya ci wata ƙwallo, amma an ce ya yi satar gida kenan ba a karɓa ba.

  12. Najeriya ta buga kwana, Najeriya 0-0 Tunisiya

    Tawagar Najeriya ta buga kwana ta hannun Lookman ta kuma je wajen Osimhen ya sa kai amma ba tayi yadda yake so ba, babu wani haɗari a gidan Tunisiya.

  13. Osimhen ya samu damar cin ƙwallo amma ta yi sama, Najeriya 0-0 Tunisiya

    Najeriya ta samu dama mai ƙyau bayan da Adams ya buga ƙwallo cikin da'ira ta 18 ta Tunisia, kuma Victor Osimhen ya sa kai amma ta yi sama da yawa ta fita waje, bugun falan ɗaya

  14. , Najeriya 0-0 Tunisiya

    Har yanzu wasa bai fara ɗaukar zafi ba, kowa yana ɗari-ɗari da tsoron yin kuskure kenan ba a fara kai hare-hare masu zafi ba.

  15. Ba ma tsoron kowa a wannan gasar- kyaftin din Super Eagles

    Kyaftin din twagar kwallon kafar Najeriya, wilfred Ndidi ya yi kukan kura cewa yan wasan Najeriya sun shirya tsaf domin ganin sun lashe gasar cin kofin Nahiyar Afrika ta bana.

    Yayin da ya ke jawabi a taron manema labarai gabannin wasansu na biyu a matakin rukuni da za su fafata da Tunisia a birnin Fez, Ndidi ya yi nuni da cewa yan Najeriya na bakin cikin rashin samun gurbi a gasar cin kofin.duniya da za a yi a badi inda ya kara da cewa abin da za su iya yi don sharewa yan Najeriya hawaye shi ne lashe wannan gasar.

    Yayin da ya ke tsokaci kan wasansu da Tunisia, kyaftin din ya yi bayanin cewa yan wasan ba su tsoron kowace tawaga ya kuma bugi kirji cewa rashin nasarar da suka yi a lokacin da suka kara da Tunisia a gasar 2019 ba zai girgiza su a kokarin da suke yi na yin nasara a wannan sasan ba wanda hakan zai ba su damar hayewa saman teburin rukunin .

  16. An take leda Najeriya 0-0 Tunisiya

    Tawagar Najeriya ta saka riga da wando da safa ruwan ganye, wato kore, ita kuwa Tunisiya ta saka farar riga da farin wando da kuma farar safa.

  17. An shiga filin wasa

    Ƴan wasan tawagar biyu wato Najeriya da na Tunisiya sun shiga cikin fili ana kuma taken kasashen biyu daf ake a take leda.

    Wasa ne na hamayya da zai yi zafi, kuma duk wadda ta yi nasara ta haɗa maki shida a wasa biyu, kenan ta kai zagaye na biyu kenan.

  18. Ƴan Super Eagles 11 da za su fara fuskantar Tunisiya

    Afcon

    Asalin hoton, BBC Sport

  19. Ƴan wasan Tunisiya 11 da za a fara wasa da su

    Afcon

    Asalin hoton, BBC Sport

  20. Senegal na daf da samun tikitin zagaye na biyu a Afcon

    Afcon

    Asalin hoton, Backpage Pix

    Sadio Mané ne farke wa Senegal ƙwallo, yayin da suka tashi 1-1 da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ranar Asabar, lamarin da ya sa suka ci gaba da zama a saman rukunin na huɗu a wasannin Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) da ake bugawa a Morocco.

    Cedric Bakambu ne ya fara ci wa Kongo a minti na 61, amma Mané ya farke bayan mintuna takwas tsakani, kuma da na 51 da ya zura a raga a tarihin bugawa kasarsa tamaula, inda Senegal ke daga cikin manyan tawagogin da ake ganin za su iya lashe gasar da ake yi a Morocco.

    Kasashen biyu suna da maki hudu daga wasanninsu bibiyu a cikin rukuni, kuma alamu na nuna za su kai zagaye na biyu cikin ruwan sanyi, bayan da kowaccensu ke da wasa na ƙarshe a rukunin da za ta buga ranar Talata.

    Senegal na gaban DR Kongo a jadawalin rukuni ne saboda yawan cin kwallaye, bayan da suka doke Botswana da ci 3-0 a wasansu na farko ranar Litinin, yayin da DR Kongo ta yi nasara a kan Benin da ci 1-0 a dai ranar