Hatsarin jirgin ƙasa a Thailand ya kashe mutum 22

Asalin hoton, Nakhon Ratchasima provincial government
Ƴansanda a Thailand sun tabbatar da cewa mutum 22 ne suka mutu yayin da 79 suka jikkata inda mutane takwas daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali bayan da wata ƙatuwar ƙugiya ta aikin layin dogo ta faɗa kan wani jirgin ƙasa a arewa maso gabashin Bangkok, babban birnin ƙasar.
Rahotanni farko sun nuna alamun cewa ana amfani da ƙugiyar ne wajen ginin gadar jirgin ƙasa mai gudun tsiya, a lokacin da ta faɗa kan jirgin.
Hotuna da bidiyoyi da ke yawo a kafafen yaɗa labarai na ƙasar sun nuna wasu sassan taragon jirgin ƙasa na cin wuta, yayin da wasu taraguna suka kauce daga layin dogo.
Hukumomi sun ce ana ci gaba da bincike da kuma aikin ceto, yayin da bayanai ke ci gaba da fitowa game da wannan mummunan hatsari.


