Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi da Ahmad Bawage
Ƴanbindiga sun kashe aƙalla mutum 14 a Kamaru
Asalin hoton, Getty Images
Wasu ƴanbindiga sun kashe aƙalla mutum 14 a arewa maso yammacin Kamaru, inda rabi daga cikinsu suka kasance mata da ƙanana yara.
Wani jami'i a yankin ya ce harin ya afku ne da sanyin safiyar yau Laraba, a wani yanki da masu magana da harshen inglishi suka fi rinjaye. Babu ƙungiyar da ta fito ta ɗauki alhakin kai harin.
An kashe duban fararen hula a tsawon shekaru goma da suka wuce, bayan da ƙungiyoyin ƴan-aware suka kaddamar da bore don neman kafa ƙasar masu magana da ingilishi, inda suka ce gwamnati ta mayar da su saniyar ware.
Sadio Mane ya ɗauki kwallo ya nufi ragar Masar tun take wasa, sai dai ɗan wasan Masar Hossam Abdelmaguid ya kaɗe kwallon, inda ta daki Mane ta kuma fita.
An take wasa tsakanin Senegal da Masar
Senegal da Masar sun fara fafatawa a wasan daf da karshe na gasar cin kofin Afirka.
Wace ƙasa ce za ta kai wasan karshe?
Ƴan wasan tawagar Masar
Asalin hoton, BBC Sport
Yan wasan tawagar Senegal
Asalin hoton, BBC Sport
Senegal da Masar na shirin karan-batta
Asalin hoton, Getty Images
Senegal da Masar na shirin fafatawa a wasan daf da karshe na gasar cin kofin Afirka a birnin Tangier na Moroko.
Ƙasashen biyu ba su sake haɗuwa ba tun wasan karshe na gasar 2021 - wanda aka buga a ƙasar Kamaru - lokacin da Senegal ta samu nasara da ci 4-2 a bugun fenariti bayan tashi wasa babu ci.
Nasarar ta dakile yunkurin Masar na son lashe gasar karo na takwas, abin da suka ƙasa cimmawa a gasar 2023 lokacin da suka fita a zagayen ƴan 16.
Shin tawagar ta Masar za ta iya ɗaukar fansa a yau?
Najeriya da UAE sun soke wa juna haraji kan kayayyaki
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za ta soke haraji kan kayayyaki 6,243 da ake shigowa da su daga Haɗadɗiyar Daular Larabawa (UAE), yayin da UAE ta soke haraji kan kayayyaki 7,315 da ake shiga da su ƙasar daga Najeriya, a matsayin wani ɓangare na sabon yarjejeniyar kasuwanci.
Ma’aikatar masana’antu da kasuwanci da zuba jari ne ta bayyana hakan a takardar yarjejeniya tsakanin Najeriya da UAE Da aka rattaɓawa hannu a watan Janairu 2026.
Ma’aikatar ta ce yarjejeniyar za ta “Sauƙaƙa samar da jari,” wanda ke nuna babban mataki a yunkurin Najeriya na fitar da kayayyakin da ba mai ba da kuma shirye-shiryen bunƙasa tattalin arziki.
Ƙasashen biyu sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar a ranar 13 ga Janairu 2026, bayan tattaunawa wanda ministar masana'antu da zuba jari, Jumoke Oduwole ta jagoranta, tare da goyon bayan ma’aikatar Shari’a da Hukumar Kula da Haraji ta Najeriya.
Ukraine na shirin kwashe yara daga ƙauyuka yayin da Rasha ke tsananta hare-hare
Ukraine ta bayar da umurnin kwashe yara da iyaye daga wasu ƙauyuka biyar, a yayin da Rasha ke ci gaba da kai hare-hare ƙasar.
Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce dakarun ƙasar sun Ƙwace ikon ƙauyen Komarivka na yankin Sumy a Ukraine a yau Laraba.
Hakan na zuwa ne kwana guda bayan harin Rasha da jirgi mara matuƙi ya katse wutar lantarki a gidaje fiye da 100, a yayin da ake cikin yanayi na tananin sanyi.
Wasu sassan babban birin ƙasar sun kasance babu naurar ɗumama gida tsawon mako guda, saboda katsewar lantarki sakamakon hare haren Rasha.
'Turji ya kori mazauna ƙauyuka aƙalla 28 a Sokoto'
Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a jihar Sokoto sun tabbatar da cewa aƙalla ƙauyuka sama da 28 sun zama kufai sakamakon ci gaba da hare-haren ƴan bindiga, musamman a yankunan da ake dangantawa da fitaccen jagoran ƴan bindiga Bello Turji, a yankinTidibale da wasu wurare da ke kewaye da shi a ƙaramar hukumar Isa.
Majiyoyi sun bayyana cewa mazauna ƙauyukan sun tsere ne bayan wani gargaɗi da ake zargin Bello Turji ya yi, inda ya umarci al’umma da su fice daga ƙauyukansu ko kuma su fuskanci kisa.
Ana danganta Turji da kisan mutane da dama da hare-hare masu muni kan fararen hula da jami’an tsaro a jihohin Sokoto da Zamfara.
Bayanan da BBC ta tattaro sun nuna cewa ƴan gudun hijra da suka fito daga yankin da lamarin ya shafa na cikin zullumi da fargaba, bayan rasa matsugunnansu.
Yawancinsu sun nemi mafaka ne a makarantun gwamnati a ƙaramar hukumar Isa da wasu ƙananan hukumomi makwabta.
Wani ɗan gudun hijra da ke sansani ya shaida wa BBC cewa,
“Sun kashe wasu, sun tafi da wasu, sannan suka yi mana gargaɗi cewa idan suka dawo suka tarar da mu, za su kashe kowa.”
Shugaban rundunar Adalci ta Ƙasa reshen jihar Sokoto, Bashar Altine Guyawa, ya ce yayin gargaɗin da Bello Turji ya yi wa mutanen Tidibale, an kashe mutum biyu da suka yi masa gardama.
“A lokacin da ƙaramar hukumar mulki ta samu labarin faruwar lamarin, nan take ta aike da motoci domin kwashe al’ummomin yankin zuwa cikin garin Isa,” in ji shi.
A nasa ɓangaren, mai bai wa gwamnan Sokoto shawara kan harkokin tsaro, Kanal Ahmad Abdul Usman (mai ritaya), ya ce gwamnatin jihar ta samu labarin abin da ya faru, amma har yanzu tana jiran cikakken rahoto daga jami’an tsaro da ke aiki a yankin tun bayan faruwar lamarin.
Jihar Sokoto dai ta daɗe tana fama da hare-haren ƴan bindiga, inda Bello Turji ke ci gaba da zama babban barazana ga tsaron jihar da ma jihohin da ke maƙwabtaka da ita a yankin arewa maso yammacin Najeriya.
Iran za ta hanzarta shari’ar masu zanga-zanga da aka kama
Asalin hoton, Getty Images
Iran ta ce za ta gaggauta sauraron shari'ar mutanen da aka kama a lokacin zanga-zangar ƙin jinin gwamnati, a yayin da ake ci gaba da yin jana'izar masu zanga-zangar.
Iyalan wani mutum mai suna Erfan Soltani, wanda aka kama a zanga-zangar a birnin Karaj, sun ce an faɗa musu cewa akwai yiwuwar a yanke masa hukuncin kisa a yau.
Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama da ke Amurka mai suna Hrana, ta ce fiye da mutum 2,500 aka kashe a zanga-zangar, ciki har da yara 12.
Kafar talabijin ta Iran ta nuna bidiyon yadda taron mutane ke halartar jana'izar jami'an tsaro fiye da 100.
Trump ya sha alwashin ɗaukar mataki mai tsauri idan Iran ta kashe masu zanga-zanga.
Kowa ya zuba ido yana jiran ganin me shugaba Trump ke nufi da taimako na nan tafe.
Mallakar Greenland zai ƙarfafa ayyukan ƙungiyar NATO - Trump
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce idan Amurka ta mallaki yankin Greenland, hakan zai ƙarfafa ayyukan ƙungiyar NATO.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Trump ya ce Amurka na buƙatar mallakar yanƙin saboda tsaron ƙasarsa.
Ya ce ba zai amince da wani mataki ba, illa na Amurka ta mallake Greenland ɗin.
Sai dai kuma Denmark da Greenland sun jaddada cewa a tsaye suke kan matsayarsu.
A gefe guda kuma Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya yi gargaɗin cewa Amurka za ta fuskanci hukuncin da bata taɓa fuskanta ba, idan ta ƙwace yankin.
Hakan na zuwa ne sa'oi kafin ganawar da ministocin harkokin wajen Greenland da Denmark za su yi da mataimakin shugaban Amurka JD Vance da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio kan makomakar Greenland.
An amince da sabon kundin tsarin mulki a Guinea-Bissau
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojojin da ke mulkin Guinea-Bissau ta amince da sabon kundin tsarin mulki a ranar 13 ga Janairu, kamar yadda jaridar O Democrata ta bayar da rahoto.
Sabon kundin tsarin mulkin zai bai wa shugaban ƙasa ƙarin iko, inda zai zama shugaban gwamnati.
Shugaban ƙasa ne yanzu zai iya naɗa firaminista da ministoci, da sauran jami’an gwamnati – ayyukan da a baya majalisar dokoki da firaminista ne ke gudanarwa.
Masu lura da al’amura sun ce sabon kundin tsarin mulkin na nufin hana matsalolin siyasa da suka sha faruwa a Guinea-Bissau sakamakon tsarin mulkin shekarun baya.
Rundunar sojin Nijar ta ce ta kashe ƴanbindiga da dama a Tillaberi
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Nijar ta sanar da cewa ta halaka yan bindiga da dama a cikin Jihar Tillaberi a ƙarƙashin wani farmaki na musamman da ta kira “Opération Borkono”.
A yayin farmakin ne kuma sojojin suka ƙwato dabbobi da dama da maharan suka yi awon gaba da su yayin hare-haren da suke kai wa garuruwa.
Rundunar ta kuma ce ta tarwatsa wata mahaƙar zinariya da ke zama maɓuyar yan bindiga, inda aka rufe rijiyoyin haƙar zinariyar da maharan ke amfani da su.
Wannan farmaki na zuwa ne a daidai lokacin da Nijar ke fama da matsalar tsaro.
Sojojin sun bayyana cewa irin waɗannan matakai na musamman za su ci gaba don tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Mene ne zai faru a wasan Moroko da Najeriya?
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Zaftarewar ƙasa ta kashe mutum 18 a DR Congo
Asalin hoton, Getty Images
Zaftarewar ƙasa ta rutsa da wani ɓangare na ƙauyen Burutsi da ke yankin Kashebere na gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, inda aƙalla mutum 18 suka rasa rayukansu a lardin North Kivu.
A halin da ake ciki, ana gudanar da aikin ceto domin gano waɗanda abin ya rutsa da su.
Zaftarewar ƙasar ta faru ne sakamakon ruwan sama mai ƙarfi a ranar Talata yayin da mazauna yankin ke barci.
Gidaje da dama sun ruguje inda rufin ƙarfe na kan wasu gidade ne kawai ake iya gani a wasu wurare.
Wani jami’in yankin ya ce laka mai kauri da duwatsu na kawo cikas ga aikin ceto, yayin da ake kula da waɗanda sukia jikkata a cibiyar kiwon lafiya dake kusa.
Haka kuma mazauna suna tono tarkace domin ceto waɗanda suka tsira ko kuma su gano gawawwaki.
Zaftarewar ƙsar ta katse babbar hanyar zuwa babban birnin lardin, Goma yayin da yankin tsaunukan gabashin DRC ke fuskantar haɗarin zaftarewar ƙasa musamman a lokacin damina.
Duk jami'in gwamnatin Kano da aka matsa masa, ya koma APC - Kwankwaso
Asalin hoton, Kwankwaso/x
Jagoran jam'iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya shawarci magoya bayansa da ke aiki a gwamnatin jihar Kano da su sanya hannu kan duk wata takarda da ke buƙatar amincewar su ta sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da siyasar Kano ta ɗauki ɗumi, musamman bayan bayanai sun fito kan cewa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, na shirin sauya sheƙa daga jam'iyyar NNPP zuwa APC.
A wani bidiyo da ya wallafa a shafin Facebook, Kwankwaso ya yi zargin cewa gwamnatin Kano na matsa wa shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli da masu riƙe da muƙamai su bayyana aniyarsu ta sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.
Ya ce: “Gwamnati ta fito da wani tsari na takura wa ciyamomi da kansiloli da sakatarori da sauran masu riƙe da muƙami wajen rubuta sunansu don nuna ko suna goyon bayan Kwankwasiyya ko Gandujiyya.”
Kwankwaso ya bayyana rashin gamsuwarsa da abin da ke faruwa, amma ya jaddada cewa talakawa sun nuna goyon baya ga jam’iyyarsa a baya duk da waɗannan ƙalubale.
Ya ce umarnin da ya bai wa mabiyansa na sanya hannu a irin waɗannan takardun, na da nufin sauƙaƙa musu nauyi da kare su daga matsin lamba, domin kada su shiga mawuyacin hali a siyasa.
Adadin mutanen da suka mutu a hatsarin jirgin ƙasa a Thailand ya kai 28
Asalin hoton, Reuters
Adadin mutanen da suka mutu a hatsarin jirgin ƙasa a Thailand ya haura zuwa 28 bisa ga sabbin bayanai daga ofishin lafiya na lardin.
Haka kuma, mutum 64 ne suka ji rauni sakamakon hatsarin, wanda bakwai daga cikinsu suna cikin mauwyacin hali.
Ana ci gaba da aikin ceto a wurin hatsarin, inda jami’an agaji ke kokarin ceto wadanda suka maƙale da kuma tabbatar da lafiyar waɗanda suka ji jikkata
Ba za mu fitar da bayanai kan hare-haren Amurka a Sokoto ba - Ƴansanda
Asalin hoton, US Defence Department
Rundunar ƴansandan Najeriya ta bayyana cewa tana da bayanai kan hare-haren da Amurka ta kai kan ’yanbindiga a arewa maso yammacin jihar Sokoto, amma ba za ta fitar da su ga jama’a ba.
Kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Channels.
Hundeyin ya ce: “A matsayinmu na rundunar ƴansanda, mun san wasu abubuwa game da hare-haren, amma ba za mu yi magana a kai ba."
Ya kuma ƙara da cewa an tura jami’an ƴansanda domin tabbatar da tsaro a yankunan da hare-haren suka shafa, musamman bayan samun rahotannin cewa wasu fararen hula na iya samun rauni ko rasa rayukansu ta hanyar ta'ammali da makaman da aka jefa waɗanda ba su fashe ba.
Asalin hoton, Benjamin Hundeyin/Facebook
A ranar 25 ga Disamba, 2025 ne Amurka ta kai hare-hare kan ƴanbindiga a Sokoto, inda Ma’aikatar Tsaron Amurka ta bayyana cewa “ƴanbindiga masu alaƙa da IS da dama” sun rasa rayukansu a hare-haren da aka gudanar tare da sahhalewar gwamnatin Najeriya.
A jiya Talata ne rundunar sojin Amurka a nahiyar Afirka (Africom) ta sanar cewa ta miƙa wa Najeriya kayan aikin soja domin tallafa wa yaki da matsalar tsaro.
Hotunan yadda ake aikin ceto bayan hatsarin jirgin ƙasa a Thailand
Ga wasu hotuna da ke nuna yadda masu aikin ceto ke aiki tuƙuru a wurin da jirgin ƙasa ya yi hatsari a Thailand wanda ma’aikatar kare bala’o’i da rage illolinsu ta ƙasar ta wallafa a yau.
Ƴansanda da ma’aikatan lafiya suna aiki tare suna taimaka wa waɗanda abin ya shafa, tare da share hanyar domin sauƙaƙa ayyukan gaggawa.
Hukumomi sun ce aikin ceto na ci gaba, yayin da ake tattara bayanai kan musabbabin hatsarin da kuma adadin waɗanda abin ya shafa.
Asalin hoton, Department of Disaster Prevention and Mitigation
Asalin hoton, Department of Disaster Prevention and Mitigation
Asalin hoton, Department of Disaster Prevention and Mitigation
Asalin hoton, Department of Disaster Prevention and Mitigation
Venezuela ta fara sakin ƴan Amurka da ta ɗaure
Asalin hoton, EPA
Amurka ta ce Venezuela ta fara sakin ƴan ƙasarta da ta ɗaure sama da mako ɗaya bayan da Amurkar ta shiga kasar ta kama Shugaba Nicolas Maduro ta yi gaba da shi.
Wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ya bayyana matakin a matsayin abu mai muhimmanci.
A makon da ya gabata, Shugaba Trump ya ce ya dakatar da hare-hare kashi na biyu lokacin da ya ji cewa Caracas na bayar da haɗin kai game da sakin fursunonin siyasa.
Hukumomin Venezuela sun yi alƙawarin sakin Amurkawan a matsayin wani mataki na neman zaman lafiya da Amurka.
Yawancin waɗanda aka tsare, an kama su ne a lokacin zanga-zangar ƙin amincewa da sake zaɓen Maduro a 2024, kan zargin gagarumin magudi a zaben.