Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Beckham ya zama biloniya na farko daga Burtaniya a fannin wasanni

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 11 zuwa 16 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Ko Tottenham za ta kai bante a Premier league?, Premier League

  2. Sweden ta saka Isak da Gyokeres a shirin zuwa gasar kofin duniya, Gasar kofin duniya

    An sanya ɗan wasan, Arsenal Viktor Gyokeres da kuma na Liverpool, Alexander Isak cikin tawagar Sweden domin gasar cin kofin duniya 2026 FIFA World Cup.

    Sai dai gasar ta bana da za a yi a Canada da Mexico da Amurka ɗan ƙwallon Tottenham, Dejan Kulusevski, ba zai samu bugawa ba, sakamakon jinya.

    Kocin Sweden Graham Potter ya ce ya sha wahala kafin ya yanke shawarar cire ɗan wasan mai shekaru 26 mai taka leda a Premier League..

    Isak mai shekaru 26 shi ma ya sha fama da jinya a wannan kakar, kuma ya fara wasannin lig guda takwas ne, tun bayan komawarsa Liverpool kan fara kakar bana, kan kuɗin fam miliyan 125 daga Newcastle United.

    Gyokeres da Isak na daga cikin ƴan wasa 11 da ke taka leda a Birtaniya da aka saka a tawagar, ciki har da masu tsaron gida Viktor Johansson na Stoke City da kuma Jacob Widell Zetterstrom na Derby County.

    Haka kuma akwai masu tsaron baya, Hjalmar Ekdal na Burnley da Gabriel Gudmundsson na Leeds United da Victor Lindelof na Aston Villa FC.

    An kuma saka ƴan wasan tsakiya, Yasin Ayari na Brighton & Hove Albion da Lucas Bergvall na Tottenham, tare da ɗan wasan Newcastle, Anthony Elanga da mai taka leda a Celtic, Benjamin Nygren.

    Sweden tana rukuni na F, kuma za ta fara da wasan da Tunisia a Monterrey a Mexico ranar 14 ga watan Yuni, kafin ta buga sauran wasanni biyu a Amurka da Netherlands a Houston ranar 20 ga watan Yuni, sannan da Japan a Dallas bayan kwanaki biyar tsakani.

    Ƴan wasan Sweden da aka bayyana:

    Masu tsaron raga: Viktor Johansson (Stoke City), Kristoffer Nordfeldt (AIK), Jacob Widell Zetterstrom (Derby County).

    Masu tsaron baya: Hjalmar Ekdal (Burnley), Gabriel Gudmundsson (Leeds United), Isak Hien (Atalanta), Emil Holm (Juventus), Gustaf Lagerbielke (Braga), Victor Lindelof (Aston Villa), Erik Smith (St. Pauli), Carl Starfelt (Celta Vigo), Elliot Stroud (Mjallby), Daniel Svensson (Borussia Dortmund).

    Masu buga tsakiya: Taha Ali (Malmo), Yasin Ayari (Brighton), Lucas Bergvall (Tottenham), Jesper Karlstrom (Udinese), Ken Sema (Pafos), Mattias Svanberg (Wolfsburg), Besfort Zeneli (Union St-Gilloise).

    Masu cin ƙwallaye: Alexander Bernhardsson (Holstein Kiel), Anthony Elanga (Newcastle United), Viktor Gyokeres (Arsenal), Alexander Isak (Liverpool), Gustaf Nilsson (Club Brugge), Benjamin Nygren (Celtic).

  3. Ingila ta fitar da jerin ƴanwasa na farko da za ta je da su kofin duniya, Fifa World Cup

    Thomas Tuchel ya miƙa jerin ƴan wasan wucin gadi na tawagar Ingila, domin zaɓar waɗanda za su buga gasar kofin duniya 2026 FIFA World Cup, inda ake ƙyautata zaton Luke Shaw da Danny Welbeck da Alex Scott suna cikin waɗanda ake sa rai.

    An kuma fahimci cewa mai tsaron bayan Real Madrid, Trent Alexander-Arnold, ya shiga cikin jerin sunayen farko.

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA, ta ba ƙasashen da za su shiga gasar damar miƙa jerin ƴan wasa 55 kafin ƙarfe 12 na daren Litinin, gabanin fara gasar ranar 11 ga Yuni.

    Yanzu Tuchel zai rage jerin ƴan wasa 26 na ƙarshe da za su wakilci Ingila a gasar da za a gudanar a Amurka da Canada da kuma Mexico.

    Har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga hukumar ƙwallon kafar Ingila kan jerin ƴan wasan na ƙwarya-kwarya, amma hukumar na shirin bayyana su ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu.

    Alexander-Arnold da Shaw da Welbeck da Scott duk ba sa cikin jerin ƴan ƙwallon Tuchel na baya-bayan nan domin wasannin sada zumunci da Uruguay da Japan — amma har yanzu suna da damar shiga cikin waɗanda za su wakilci Ingila a gasar kofin duniya a bana.

  4. , Daga Jaridu

    Kocin Barcelona Hansi Flick ya amince da sabon kwantiragin da zai ci gaba har zuwa 2028, tare da zaɗin tsawaitawa na tsawon shekara guda. (Mundo Deportivo)

    Ana sa ran Manchester United za ta yi hidima a kasuwar musayar ƴan wasa yayin da take zawarcin ƴan wasa aƙalla biyar da suka haɗa da ƴan wasan tsakiya uku da na baya na gefen hagu da kuma ɗan wasan gaba. (Sun)

    Masu tsaron gida biyu na gasar Ligue 1 sun tabbata a matsayin waɗanda za su iya maye gurbin Emi Martinez, inda Aston Villa ta ke nazari kan ɗan wasan Lens Robin Risser da Guillaume Restes na Toulouse - dukansu matasan Faransa ne masu shekara 21. (Foot Mercato)

    Ɗan wasan tsakiya na Sporting da Portugal Francisco Trincao, mai shekara 26, yana jan hankalin Liverpool da Chelsea. (Caught Offside)

    Ɗan wasan Sunderland da DR Congo Noah Sadiki, mai shekara 21, bai yanke hukuncin barin filin wasan Stadioum of Light ba a bana. (Voetbal Nieuws)

  5. Har yanzu da sauran kalubale a karawa biyun da ta rage a Premier League, Premier League

    Watakila Pep Guardiola yake canje-canjen ƴan wasa sakamakon cunkoson wasannin da suka rage masa kafina kammala kakar nan - har da wasankarshe a FA Cup da Chelsea.

    Guardiola ya ce bai fitar da rai ba kan lashe kofin Premier League, duk da nasarar da Arsenal ta samu 1-0 a gidan West Ham da yanzu aka samu tazarar maki biyar tsakaninsu.

    Kociyan ɗan kasar Sifaniya, har yanzu yana da wasa ɗaya kwantai, yana buƙatar Arsenal ta ɓatar da maki, ko City za ta samu damar tarar da Arsenal, kuma ranar Laraba za a kara tsakanin City da Palace a gasar ta Premier League.

    Guardiola ya ce yana sa ran Crystal Palace za ta yi wahalar doke wa, duk da cewa tana matsayi na 15 a teburin, kuma ba ta yi nasara ba a wasa huɗu da ta buga a baya-bayan nan a gasar.

    “Suna da wasan ƙarshe a gasar zakarun Turai,” in ji shi, yana nufin wasan ƙarshe a UEFA Europa Conference League Final da Palace za ta buga da Rayo Vallecano ranar 27 ga Mayu.

    “Wataƙila suna fama da yawan buga wasanni, suna bukatar sauye-sauye, kuma kociyansu, Oliver Glasner zai bae ƙungiyar a karshen kakar bana, amma suna da ƙwarewa.”

    Guardiola ya kuma ce ɗan wasan City, Rodri da kuma Abdukodir Khusanov suna samun sauƙi sosai, amma bai bayyana ko za su buga karawar da Crystal Palace ba.

  6. Real Madrid na daf da bai wa Mourinho aikin kociyan Real Madrid, Real Madrid

    Jose Mourinho na cikin matakin ƙarshe a tattaunawa, domin zama sabon kocin Real Madrid, shekara 13 bayan wa’adinsa na farko a Santiago Bernabeu.

    Mai shekaru 63, shi ne wanda ke kan gaba da za a baiwa aikin horar da Real Madrid — kuma a halin yanzu shi kaɗai ne ɗan takarar da Real Madrid ke tattaunawa da shi kan kulla yarjejeniya.

    Zai maye gurbin Alvaro Arbeloa, wanda aka ba aikin a watan Janairu, bayan tafiyar Xabi Alonso.

    Shugaban Real Madrid, Florentino Perez, ya fara tunanin yiwuwar dawo da Mourinho kwanaki biyu bayan Xabi Alonso ya bar ƙungiyar, yayin tattaunawar farko da wakilan kocin ɗan Portugal.

    Mourinho yana kocin Benfica a yanzu haka, wanda ya kulla yarjejeniyar kwantiragin shekara biyu a watan Satumbar bara, sai dai a ranar Litinin ya shaida wa manema labarai cewa bai shirya yin magana game da makomarsa ba tukuna.

    Watakila wasan ranar Asabar da Estoril Praia shi ne na ƙarshe da zai ja ragamar Benfica daga nan ya koma Sifaniya.

    Mourinho ya taɓa horar da Real Madrid tsakanin 2010 zuwa 2013, inda ya lashe La Liga da Copa del Rey da kuma Supercopa de España.

  7. Ko West Ham za ta faɗi daga Premier League a bana?, Premier League

  8. Ramos zai sayi Sevilla ƙungiyar da ya fara tamaula tun yana yaro, La Liga

    Tsohon ɗan wasan tawagar Sifaniya, Sergio Ramos na daf da sayen tsohuwar ƙungiyarsa, Sevilla, bayan da shi da kamfanin masu zuba jari na Five Eleven Capital suka cimma yarjejeniya da manyan masu hannun jarin ƙungiyar, kamar yadda kafafen yaɗa labaran Sifaniya suka ruwaito a ranar Talata.

    Jaridar El Pais ta ce yarjejeniyar, wadda ta kai kusan euro miliyan 400 (dala miliyan 470), ta shafi kaso 80 cikin 100 na jimillar hannun jarin ƙungiyar, inda aka ƙiyasta kowanne kaso da euro 3,500.

    Ana buƙatar amincewar La Liga da kuma Hukumar Wasanni ta Ƙasar Sifaniya kafin a kammala cinikin.

    Sevilla ta ci gaba da kasancewa a La Liga tun kakar wasa ta 2001-02, amma ƙungiyar daga yankin Andalusia tana fafutukar kauce wa faɗuwa rukuni a wannan kakar, saboda rashin samun ƙyaƙƙyawan sakamako.

    Ƙungiyar, wadda ta lashe UEFA Europa League a kakar 2022-23, tana matsayi na 13 a teburin gasar La Liga, amma tana da tazarar maki uku kacal daga yankin ƴan karshen teburi, yayin da wasanni uku suka rage. A kakar da ta gabata ma ta gama a matsayi na 17 ne da maki ɗaya kacal sama da yankin faɗuwa.

    Ramos, wanda ya lashe FIFA World Cup tare da Sifaniya da kuma kofunan nahiyar Turai guda biyu, ya fara buga wasa a matasan Sevilla kafin ya koma Real Madrid a shekarar 2005, inda ya taimaka musu wajen lashe manyan kofuna 22.

    Ɗan wasan mai shekaru 40 ya koma Sevilla a shekarar 2023 domin buga kakar wasa guda ɗaya, kuma ƙungiya ta ƙarshe da ya takawaleda ita ce Monterrey ta Mexico.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce ya tuntuɓi Sevilla da Five Eleven Capital domin jin karin bayani daga gare su.

  9. Flick na daf da rattaba kwantiragin ci gaba da horar da Barcelona, Barcelona

    Hansi Flick ya ce zai saka hannu kan tsawaita kwantiragin ci gaba da horar da Barcelona har zuwa karshen kakar 2028, bayan da ya lashe La Liga a ranar Lahadi kuma na biyu a jere.

    Flick, wanda kwantiraginsa zai ƙare a watan Yunin 2027, ana sa ran zai sanya hannu kan ƙarin shekara guda, tare da damar sake tsawaita zamansa kaka ɗaya.

    Ƙungiyar ta haɗa maki 91 da babu wata ƙungiya da za ta iya riskarta, yayin da wasanni uku suka rage a kammala kakar bana, bayan da ta doke babbar abokiyar hamayyarta Real Madrid.

  10. Dzeko zai shiga jerin masu shekara 40 da suka buga kofin duniya, Gasar kofin duniya

    Tsohon ɗan wasan Manchester City, Edin Džeko na shirin shiga cikin jerin fitattun ƴan kwallo masu shekara 40 ko fiye da haka da suka buga a gasar cin kofin duniya, bayan da aka saka shi cikin tawagar Bosnia and Herzegovina da za ta bana.

    Ɗan wasan tawagar Kamaru, Roger Milla ya taka leda kuma ya ci ƙwallo a gasar ta 1994.

    Haka kuma akwai masu tsaron raga shida da suka yi hakan — Essam El Hadary na Masar, wanda yake da shekara 45 a gasar cin kofin duniya a 2018, Faryd Mondragón na Colombia da Pat Jennings na Ireland ta Arewacin da Peter Shilton na Ingila da Dino Zoff na Italiya da Ali Boumnijel na Tunisia.

    Ana kuma sa ran Luka Modrić mai shekara 40 da Cristiano Ronaldo mai shekara 41 za su taka leda ga ƙasashensu, Croatia da Portugal a gasar ta bana.

  11. Marie-Louise Eta ta lashe wasa a karon farko a matakin kociyar Bundesliga, Bundesliga

    Marie-Louise Eta ta yi murnar samun nasararta ta farko tun bayan zama mace ta farko da ta jagoranci ƙungiya a babbar gasar tamaula ta Jamus, bayan da FC Union Berlin ta doke FSV Mainz 05 da ci 3-1 ranar Lahadi.

    Eta, wadda nadinta ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, ta karɓi ragamar ƙungiyar a matsayin kociyar wucin gadi a watan Afrilu, bayan korar Steffen Baumgart. Za ta ci gaba da jagorantar ƙungiyar har zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana, kafin ta koma tawagar mata a kakar tamaula mai zuwa.

    Bayan shan kashi a wasanni biyu na farko da ta jagoranta, Union Berlin ta samu maki ɗaya a wasan da ta buga da FC Köln a farkon wannan watan.

    Union Berlin za ta kara da FC Augsburg ranar Asabar a wasanta na ƙarshe na kakar nan.

  12. Holger Rune ya janye daga gasar Hamburg Open da kuma French Open, yayin da yake ci gaba da murmurewa, kamar yadda ɗan ƙasar Denmark ɗin ya bayyana ranar Litinin.

    Dan wasan mai shekaru 23 an yi masa tiyata a watan Oktoba. Daga cikin manyan nasarorinsa a gasar Grand Slam akwai kai wa zagayen kwata-fainal a French Open sau biyu a jere a shekarun 2022 da 2023, da kuma kai wa kwata-fainal a Wimbledon Championships a shekarar 2023.

    An sa ran Rune zai koma fafatawa a wannan watan a Hamburg, amma ya yanke shawarar kada ya yi gaggawar dawowa wasa a filayen kan taɓo.

    Gasar Hamburg ATP 500 ta kan taɓo za a fara daga 17 zuwa 23 ga watan Mayu, yayin da babban jadawalin French Open zai fara ranar 24 ga watan Mayu.

  13. Ƙungiyoyin Turai 4 da suka lashe kofunan gasannin ƙasashensu, Gasar kofin duniya

    Fitattun ƴan Najeriya da masoya ƙwallon a ƙasar na ci gaba da taya ɗan wasan ƙasar, Victor Osimhen murnar jagorantar ƙungiyarsa ta Galatasaray S.K. wajen lashe kofin gasar Turkiyya.

    Cikin wani saƙo da tsohon ɗantakarar shugaban ƙasar, Peter Obi ya wallafa a shafinsa na X, ya taya Osimhen murlar lashe babbar gasar tamaula ta Turkiyya, bayan da ya ci ƙwallo biyu a wasan da ya bai wa ƙungiyar nasara. Latsa nan domin ci gaba da karanta labarin

  14. Marmoush zai kara yin fice a sauran wasan Man City a kakar nan, Manchester City

    Pep Guardiola ya bayyana cewa Omar Marmoush zai taka muhimmiyar rawa a wasannin da suka rage wa Manchester City a kakar nan

    City na da sauran wasa huɗu kafin kakar nan ta karkare, ciki har da wasan ƙarshe a FA Cup da Chelsea a Wembley - kenan cikin kwana 12, ƙungiyar za ta yi fatan lashe dukkan wasannin da suka rage mata.

    Ɗan wasan tawagar Masar, Marmoush bai samu damar taka leda sosai ba a wannan kakar, inda ya fara da karawa bakwai a Premier League. Sai dai ya nuna ƙwarewarsa lokacin da ya zura ƙwallo a raga a wasan da City ta doke Brentford 3-0, wanda ya shiga canjin ɗan wasa a ranar Asabar.

    Guardiola ya ce yana sa ran Marmoush da sauran ƴan wasan da ba sa fara wasa akai-akai, za su kasance cikin shiri idan aka nemi gudummawarsu a koda yaushe.

    Marmoush yana sha zama a benci ne saboda kasancewar Erling Haaland, wanda ya ci ƙwallonsa ta 50 a bana yana kan ganiya.

  15. , Daga Jaridu

    Yanzu dai ta tabbata cewa kungiyoyin Firimiya na - Arsenal, da Liverpool, da kuma Manchester United suna da damar samun dan bayan Italiya Andrea Cambiaso, bayan da Juventus ta ce za ta iya sakin dan wasan mai shekara 26 a bazaran na. (Teamtalk)

    Har yanzu Atletico Madrid tana son sayen dan wasan tsakiya na Wolves, Joao Gomes, amma kuma ta ce ba za ta biya sama da yuro miliyan 40 ba a kan dan Brazil din mai shekara 25.(Marca)

    Dan wasan tsakiya na Scotland Bailey Rice, mai shekara 19, na shirin barin Rangers a bazaran nan kuma Aston Villa na daga kungiyoyin Firmiya da suke son sayenshi. (Football Insider)

    Ipswich Town na tattara sunayen masu horarwa ko da kociyanta Kieran McKenna zai samu aikin horad da wata kungiya a gasar Firmiya a bazaran nan. (Sun)

  16. Sabbin ƴan wasa huɗu sun lashe La Liga a karon farko a Barcelona, La Liga

    Har yanzu Barcelona na ci gaba da murnar lashe kofin La Liga karo na biyu a jere, bayan nasarar da ta samu a El Clásico a filin Spotify Camp Nou a kan Real Madrid.

    Wannan ne karon farko da sababbin ƴan wasa huɗu — Joan Garcia da Marcus Rashford daJoão Cancelo da kuma Roony Bardghji — suka lashe gasar La Liga a rayuwarsu.

    Uku daga cikinsu sun shiga Barça kan fara kakar bana. Ta ɗauki Joan Garcia domin ƙarfafa matsayin mai tsaron raga, sannan ta sayi matashin ɗan wasa Roony Bardghji saboda bajintarsa. Haka kuma ta ɗauki aron Marcus Rashford daga Manchester United..

    A wannan kakar, matasa huɗu — Jofre Torrens, Toni Fernández, Xavi Espart da Tommy Marqués — sun fara bugawa Barcelona wasansu na farko, kuma sun taimaka wajen samun wannan nasara.

    Sauran matasan daga makarantar koyon tamaula taƙungiyar, wato Álvaro Cortés da Eder Aller, duk da cewa ba su fara bugawa ƙungiyar wasan farko ba, sun yi atisaye tare da manyan ƴan wasan a mafi yawan kakar nan, kuma ana ɗaukarsu cikin waɗanda suka taka rawa a wannan nasara.

  17. West Ham za ta bi bahasin dalilin soke ƙwallon da ta ci Arsenal, Premier League

    West Ham United na shirin tuntuɓar kwamitin alkalai na Professional Game Match Officials Limited (PGMO) kan jin dalilin soke ƙwallon da suka ci a ƙarshen lokaci a wasa da Arsenal.

    A ranar ta Lahadi West Ham ta ci ƙwallon da take tunanin za ta taimaka mata tsira daga faduwa a gasar bana, wanda Callum Wilson ya zura a raga.

    To sai dai an soke ƙwallon, bayan da alakalin wasa ya je yaduba lamarin ya kuma soke sakamakon, saboda Pablo Fornals na West Ham ya yi wa mai tsaron ragar Arsenal, David Raya keta.

    West Ham ta damu da aka soke ƙwallon, shi ya sa take son a fayyace mata daliln hakan, wadda take ta ukun karshen teburi a kakar bana.

    Haka kuma ƙungiyar za ta nemi saukin tattaunawa da aka yi tsakanin tsakanin alkalin wasa, Chris Kavanagh da jami’in da ya kula da VAR, Darren England.

    Daga ƙarshe Arsenal ta yi nasara da ci 1-0, wanda ya sa ta ƙara tazarar maki biyar tsakaninta da Manchester City mai biye da ita. Wannan sakamakon ya kuma ƙara sanya makomar West Ham cikin haɗari, domin tana matsayi na 18, yayin da Tottenham ke sama da ita da maki ɗaya kafin karawarsu da Leeds United ranar Litinin.

  18. , Daga Jaridu

    Manchester United ta yi watsi da maganganun da ake yi cewa za ta bar dan wasanta na gaba na gefe Amad Diallo, dan Ivory Coast, mai shekara 23 ya bar kungiyar a bazaran nan. (Teamtalk)

    Liverpool ta tattauna da Real Madrid a kan dan takaitaccen aikin da Xabi Alonso ya yi da kungiyar ta Sifaniya, a shirin da kungiyar ta Firimiya ke yi na duba yuwuwar bai wa tsohon dan wasan nata na tsakiya aikin kociya. (AS )

    Everton na tattaunawa da John Stones a kan yuwuwar komawar dan bayan na Ingila mai shekara 31, kungiyar idan ya bar Manchester City a bazaran nan. (Football Insider)

    Newcastle ta kusa rike matashin dan wasan tsakiya na Ingila Lewis Miley mai shekara 20 na tsawon lokaci inda take dab da cimma yarjejeniya da shi ta kwantiragi na tsawon shekaru. (Sun)

  19. Liverpool ta fitar da hoton wani abin da za ta gina don tunawa da marigayi ɗan wasanta Diogo Jota da ɗan’uwansa Andre Silva bayan rasuwarsu a lokacin bazarar da ta gabata.

    Jota mai shekara 28 da Andre Silva mai shekara 25, wanda ke buga wa Penafiel wasa a rukuni na biyu a Portugal, sun mutu ne a wani hatsarin mota a ranar 3 ga Yuli a yankin Zamora a ƙasar Spain.

    Abin tunawar yana ɗauke da siffar zuciya mai lankwasawa, wanda ke nuni da yadda Jota ke murnar cin ƙwallo. Haka kuma yana ɗauke da lambobin rigunansu 20 da 30, tare da kalmomin waƙar Jota da magoya bayan Liverpool ke rerawa a minti na 20 a kowane wasa.

    An sanya wa abin tunawar suna “Forever 20”, kuma Liverpool ta ce tana girmama rayuwar Jota da Andre Silva, dangantakarsu ta ƴan’uwa da kuma ƙauna da girmamawar da iyalai da abokan wasa da magoya baya a duniya.

    Za a kafa abin tunawar a filin Anfield a titin 97 Avenue. An kuma sake amfani da kayayyakin girmamawa da magoya baya suka ajiye a wajen Anfield, bayan mutuwar Jota, inda aka haɗa su cikin dutsen ginin abin tunawar.

    Liverpool ba ta sanar da ranar ƙaddamar da abin tunawar ba tukuna, amma ta ce za ta bayyana ranar nan gaba.

    Jota ya koma Liverpool daga Wolverhampton Wanderers a shekarar 2020, inda ya zura ƙwallo 65 a wasa 182 da ya buga wa ƙungiyar. Ya taimaka musu lashe Premier League da FA Cup da kuma kofunan EFL Cup guda biyu a lokacin da yake Merseyside.

  20. Dybala zai buga wa Roma wasan karshe a Serie A ranar Lahadi, Roma

    Ɗan wasan tawagar Argentina, Paulo Dybala ya ce karawar hamayya ta Serie A da za su buga da S.S. Lazio ranar Lahadi na iya zama na ƙarshe a gida da zai buga wa AS Roma, saboda har yanzu ƙungiyar ba ta tuntube shi domin tattauna makomarsa ba.

    Mai shekara 32, wanda ya shafe shekara bakwai a Juventus FC, ya koma Roma a shekarar 2022, kuma ya taimaka musu kai wa wasan ƙarshe a wasan karshe a Europa League a kakarsa ta farko.

    Sai dai Dybala ya sha fama da jinya a wannan kakar, sannan an yi masa tiyata a watan Maris, lamarin da ya sa ya rasa kusan watanni huɗu bai taka leda ba.

    Dybala ya bayar da ƙwallo aka zura a raga a wasan da Roma ta doke Parma Calcio 1913 da ci 3-2, wanda ya sa take maki iri ɗaya da AC Milan a mataki na huɗu a kan teburi, domin neman gurbin Champions League a baɗi.