Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Beckham ya zama biloniya na farko daga Burtaniya a fannin wasanni

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 11 zuwa 16 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Wa zai lashe kofin Premier League a bana?

  2. , Man City da Palace

    Crystal Palace ta zura kwallaye biyu a kowanne daga cikin wasanninta huɗu a baya bayan nan da ta buga a waje da Manchester City, amma ta ci wasa ɗaya daga cikinsu ta yi canjaras ɗaya aka doke ta biyu.

    Ƙungiyar da ta fi kusa da yin hakan a tarihin Premier League ita ce Tottenham Hotspur, wadda ta zura ƙwallaye biyu ko fiye da haka a wasa biyar a jere a filin Etihad.

  3. , Man City da Palace

    Crystal Palace ma tana da wasan ƙarshe a UEFA Conference League da ke tafe, kuma kocinta Oliver Glasner ya yi sauye-sauye huɗu a wasan da ta yi canjaras da Everton.

    Jean-Philippe Mateta ne zai jagoranci gurbin cin ƙwallaye, yayin da yake neman zura kwallarsa ta 50 a gasar Premier League.

    Sauran ƴan wasan da za a fara wasannin da su sun haɗa da Yeremy Pino da Will Hughes da Jefferson Lerma.

    A gefe guda kuma, Jørgen Strand Larsen da Ismaïla Sarr da Daichi Kamada da Adam Wharton basa cikin ƴan wasa 11 na farko.

    Jerin ƴan wasan Crystal Palace:

    Dean Henderson, Daniel Muñoz, Maxence Lacroix, Chris Richards, Canvot, Tyrick Mitchell, Lerma, Pino, Hughes, Johnson da Mateta.

  4. , Man City da Palace

    Manchester City ba ta yi rashin nasara ba a wasa 16 da ta buga a gida afilinta na Etihad, inda ta ci 13 ta kuma canjaras uku, kuma ita ce ke fara zura ƙwallo a raga a dukkan waɗannan wasanni.

    Haka kuma City ba ta sha kashi ba a wasannin dare 23 a jere a Premier League, tun bayan rashin nasara a hannun Aston Villa a Disamba 2023.

  5. Haaland da Cherki na benchi, Man City v Crystal Palace

    Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya nuna cewa hankalinsa na kan wasan ƙarshe a FA Cup da za su buga da Chelsea a ranar Asabar, bayan da ya yi sauye-sauye yan wasa shida a karawar da ta doke Brentford a wasan da ya gabata.

    Manyan ƴan wasa kamar Erling Haaland da Rayan Cherki da Jérémy Doku da Nico O'Reilly suna zaman benci da kuma Nathan Aké da Tijjani Reijnders.

    A maimakon haka, Guardiola ya saka Omar Marmoush da Phil Foden da Savinho da Abdukodir Khusanov da Rayan Aït-Nouri daga ƴan wasa 11.

    Haka kuma Joško Gvardiol ya dawo cikin ƙungiyar, bayan da ya yi jinya tun daga ranar 4 ga watan Janairu sakamakon karya ƙafa.

    Sai dai ɗan wasan tsakiya Rodri har yanzu bai murmure ba.

    Jerin ƴan wasan Manchester City:

    Gianluigi Donnarumma, Matheus Nunes, Khusanov, Marc Guéhi, Gvardiol, Aït-Nouri, Bernardo Silva, Foden, Antoine Semenyo, Savinho da kuma Marmoush.

  6. , Man City da Palace

    Manchester City ba ta sha kashi a wasanni takwas na dare ba da ta buga da Crystal Palace a gasar Premier League ta yi nasara biyarda canjaras uku, tun bayan da Palace ta doke ta 2-0 a gida a Oktoba 2021.

  7. Yadda teburi yake, Man City v Crystal Palace

  8. Manchester City da Crystal Palace, Premier League

    Manchester City za ta buga wasan mako na 36 a Premier League da Crystal Palace a Etihad ranar Laraba.

    A wasan farko da suka fafata a cikin Disamba, City ce ta yi nasara 3-0 a Selhurst Park, inda Erling Haaland ya ci biyu da kuma Phil Foden.

    City tana mataki na biyu a teburin Premier League da maki 74, yayin da Palace mai maki 44 tana ta 15 a kasan teburin Premier League.

  9. Barkanmu da kasance a shirin kawo wasan Man City da Palace kai tsaye, Man City v Crystal Palace

  10. Morocco za ta buga wasa uku na sada zumunta uku kafin gasar kofin duniya, Gasar kofin duniya

    Morocco ta tabbatar da cewa za ta buga wasan sada zumunci uku kafin gasar cin kofin duniya da za a fara a watan gobe, domin bai wa sabon kocinta ƙarin lokaci tare da ƴan wasan tawagar.

    Morocco, wadda ta ba mutane mamaki da ta kai wasan kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Qatar shekaru huɗu da suka wuce, ta naɗa Mohamed Ouahbi a matsayin sabon koci a watan Maris bayan murabus ɗin Walid Regragui.

    Ouahbi ya jagoranci wasanni biyu kacal tun bayan karɓar aikin, inda ya yi canjaras da Ecuador sannan ya samu nasara a kan Paraguay bayan makonni kaɗan da kama aiki.

    Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Morocco ta ce tawagar za ta buga wasa da Burundi ranar 26 ga watan Mayu, kafin daga bisani ta kara da Madagascar ranar 2 ga watan Yuni a Rabat, inda magoya baya za su samu damar yi wa tawagar bankwana kafin zuwa buga babbar gasar tamaula ta duniya.

    Da zarar ta isa Amurka, inda sansaninta zai kasance a Basking Ridge, Morocco za ta kammala shirye-shiryenta da wasa da Norway ranar 7 ga watan Yuni a New York.

    Rahotanni sun ce ana sa ran Morocco za ta fara shirye-shiryenta ranar 22 ga watan Mayu, amma ba za ta sanar da sunayen ƴan wasan tawagar ba sai bayan mako guda.

    An sanya Morocco a rukuni na uku a gasar cin kofin duniya, inda za ta kara da Brazil ranar 13 ga watan Yuni a New York, sannan da Scotland ranar 19 ga watan Yuni a Boston, kafin daga bisani ta fafata da Haiti ranar 24 ga watan Yuni a Atlanta.

  11. Amurka ta musanta cewar ta ƙi bai wa wasu ƴan wasan Iraqi biza, Gasar kofin duniya

    Fadar White House ta musanta rahotannin da ke cewa Amurka ta ƙi bai wa ƴan wasa biyar na tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Iraq biza kafin gasar kofin duniya da za a fara a watan gobe.

    Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta aika da sanarwa ranar Laraba zuwa Front Office Sports domin mayar da martani kan rahotannin da suka yaɗu a intanet game da ƴan wasa biyar, ciki har da mai takaleda a Luton Town, Ali Al-Hamadi.

    Sanarwar ta ce: “A yanzu babu wata matsala da aka sani da ta shafi ƴan wasan Iraq. Muna ci gaba da tuntuɓar juna da FIFA, kuma za mu ci gaba da bai wa waɗannan ‘ƴan wasa fifiko bisa umarnin shugaban ƙasa, domin tabbatar da an gudanar da gasar mai kayatarwa da tsaro.”

    Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Iraq ma ta ƙaryata jita-jitar da ta bazu a kafafen sada zumunta ranar Talata.

    Ta bayyana cewa: “Labarin ba gaskiya ba ne. Magana ita ce duk Ƴan wasan tawagar ƙasa sun samu bizar shiga Amurka.”

    Kamfanin labarai na Iraq, The New Region, ya ruwaito cewa ana kuma ci gaba da shirye-shiryen samun bizar shiga Canada na gaba kaɗan.

    Iraq tana rukuni mai ƙarfi a gasar cin kofin duniya ta wannan bazara a Arewacin Amurka, tare da Faransa da Senegal da kuma Norway.

    An tsara Iraq za ta buga wasanni a Foxborough ranar 16 ga watan Yuni da Norway, sannan a Philadelphia ranar 22 ga watan Yuni da Faransa, kafin daga bisani ta kara da Senegal a Toronto ranar 26 ga watan Yuni.

  12. Ƴar wasan tennis ta ɗaya a Burtaniya, Emma Raducanu za ta koma buga wasa a gasar Strasbourg Open bayan da aka yi mata alfarma shiga wasannin, yayin da take ci gaba da atisaye taka rawar gani a gasar French Open.

    Raducanu mai shekara 23 ta janye daga gasar Italian Open saboda matsalar rashin lafiya a farkon wannan watan, kuma ba ta sake fafatawa ba tun bayan rashin nasara a zagaye na uku a hannun Amanda Anisimova a gasar Indian Wells ranar 8 ga watan Maris.

    Gasar da ake bugawa a kan taɓo a Strasbourg za ta fara ne ranar Lahadi, mako guda kafin fara gasar French Open a ranar 24 ga watan Mayu.

    Wadda ta lashe gasar US Open ta shekarar 2021 tana matsayi na 30 a duniya a yanzu.

    An kuma bai wa Raducanu katin gayyata a gasar WTA 500 ta Strasbourg a bara, inda ta doke ƴar wasa waddake cikin manya 20 na farko a tennis, Daria Kasatkina, kafin daga bisani ta sha kashi a hannun, Danielle Collins.

  13. An rage farashin motocin zirga-zirga zuwa filayen gasar kofin duniya a New York, Gasar kofin duniya

    An rage farashin motocin ɗaukar magoya baya zuwa ɗaya daga cikin filayen wasan gasar cin kofin duniya bayan korafe-korafen magoya baya.

    Ingila za ta kara da Panama a MetLife Stadium ranar 27 ga watan Yuni, kuma tun farko an sanya kudin motar dala 80 ga magoya bayan da za su tashi daga Grand Central Terminal ko tashar motocin Port Authority Bus Terminal a New York.

    Gwamnar jihar New York, Kathy Hochul, ta bayyana a shafukan sada zumunta cewa yanzu an rage kuɗin tikitin motar zuwa dala 20 domin tabbatar da cewa gasar cin kofin duniya ta kasance “mai saukin zuwa kallo ga kowa da kowa”.

    Tun da farko magoya bayan Ingila sun nuna rashin jin daɗinsu kan tsadar kudin sufuri, inda wani ya ce kudin jirgin kasa daga Boston da New York zuwa wasannin ya fi abin da ya biya wajen kallon wasan karshe na UEFA Euro 2024 Final a Berlin.

    Gwamna Hochul ta kuma bayyana cewa kashi 20 cikin 100 na tikitin motocin za a ware su ga mazauna New York saboda su ne “ke taimakawa wajen karbar bakuncin duniya baki daya.”

  14. Gwarzuwar gasar French Open sau huɗu, Iga Swiatek, ta nuna yadda take fatan dawowa kan ganiya da ƙwarin gwiwa, bayan wata gagarumar nasara da ta kai ta wasan kusa da na ƙarshe a Italian Open.

    ‘Yar ƙasar Poland mai shekara 24 ta yi sama da awa guda da ta doke Ba’amurkiya mai matsayi na biyar, Jessica Pegula da ci 6-1 6-2 a ranar Laraba.

    Tun bayan da ta ɗauki tsohon kocin Rafael Nadal, wato Francisco Roig, a watan da ya gabata, tare da neman shawarwari daga Nadal a filin atisaye, Swiatek tana fara komawa matakin da ya sa ake jin tsoronta sosai a baya.

    Daga abin da aka gani yanzu, ƴar wasan mai matsayi na huɗu a duniya tana sake tabbatar da kanta a matsayin wadda aka fi sa ran lashe kambun French Open da za a fara a wata mai zuwa.

  15. , Daga Jaridu

    Manchester United na duba yiwuwar zawarcin ɗan wasan tsakiyar Real Madrid ɗan ƙasar Uruguay Federico Valverde, mai shekara 27. (Star)

    Paris St-Germain ta sanya ɗan wasan gaban Atletico Madrid da Argentina Julian Alvarez, mai shekara 26, a cikin jerin sunayen ƴan wasan da za ta yi zawarci a bazara mai zuwa. (ESPN)

    Manchester United ta ƙara ƙaimi wurin zawarcin ɗan wasan Atalanta dan ƙasar Brazil Ederson, mai shekara 26, da kuma dan wasan tsakiyar West Ham da Portugal, Mateus Fernandes, mai shekara 21. (Sky Sports)

    Ben White na iya watsi da tayin Everton a bazara idan ɗan wasan , mai shekara 28, ya samu tabbacin ci gaba da taka leda a Arsenal. (Football Insider)

    Real Madrid ba ta da tabbacin ko za ta fara batun sayen ɗan wasan bayan Como da Sifaniya Jacobo Ramon a bazara, don haka Chelsea za ta iya samun damar sayen ɗan wasan mai shekara 21. (Sun)

  16. Ben White baya son a yi masa tiyata, domin ya buga gasar kofin duniya, Arsenal

    Mai tsaron bayan Arsenal, Ben White ba zai bukaci a yi masa tiyatar gwiwa ba — amma ana sa ran ba zai samu damar shiga tawagar Ingila ba a gasar cin kofin duniya.

    A ranar Talata ne Arsenal ta tabbatar da cewa White ya samu “mummunar rauni” yayin nasarar da suka yi da ci 1-0 a kan West Ham United ranar Lahadi a gasar Premier League.

    White ba zai buga wasa uku na ƙarshe da Arsenal za ta yi ba, wasannin da ka iya sa ta lashe kofin Premier League da kuma fafatawar karshe a Champions League ba.

    Sai dai, rahotanni sun nuna cewa ɗan wasan mai fama da raunuka ba za a yi masa tiyata ba.

    Wannan labari zai zama abin farin ciki ga White da Arsenal, domin ana fatan zai iya dawowa kafin shirye-shiryen kakar wasa mai zuwa.

    Amma ana ganin wannan rauni zai kawo ƙarshen burin White mai shekaru 28 na zuwa gasar cin kofin duniya, bayan da kwanan nan ya dawo buga wa Ingila wasa bayan shekara huɗu da aka daina gayyatarsa tawagar ƙasa, wanda ya buga wasan da ta i da Uruguay da kuma Japan.

    Kocin Ingila Thomas Tuchel zai sanar da sunayen ƴan wasan da za su buga wa ingila gasar cin kofin duniya cikin kwanaki 12 masu zuwa, yayin da wasan farko na Ingila za ta kara shi ne da Croatia ranar 17 ga watan Yuni.

    Rashin Ben White zai jefa kocin Arsenal Mikel Arteta cikin matsalar wajen zaɓin wanda zai maye gurbinsa a wasan Premier League da Burnley da Crystal Palace, yayin da take neman kawo ƙarshen jiran shekaru 22 ba tare da lashe kofin Premier League ba.

    Haka kuma, tana da wasan ƙarshe a Champions League da Paris Saint-Germain a wannan watan, yayin da Jurrien Timber ma ke jinya.

    Timber ya shafe watanni biyu baya buga wasa saboda matsalar ƙugu, kuma har yanzu ba a san ko zai iya dawowa kafin ƙarshen kakar wasa ba.

  17. Mafarkin Kulusevski na zuwa gasar kofin duniya a bana na dusashewa, Gasar kofin duniya

    Kocin Sweden, Graham Potter ya bayyana cewa ɗan wasan, Tottenham Dejan Kulusevski, yana samun sauki daga raunin da yake jinya, kuma yana shirin dawowa atisaye kafin fara kakar wasa mai zuwa.

    An cire Kulusevski daga tawagar Sweden ta gasar cin kofin duniya ranar Talata, bayan shekara guda yana jinya saboda raunin gwiwar dama.

    A watan Maris, bayan da Kulusevski ya sake yin wata tiyata ta biyu kan matsalar gwiwar da ta daɗe tana damunsa, ya bayyana cewa “gwiwata tana cikin ƙoshin lafiya yanzu” kuma yana fatan zai iya buga wa Sweden gasar kofin duniya, amma Potter ya kawo ƙarshen wannan fatan a hukumance a wannan makon.

    Babban kocin Tottenham, Roberto De Zerbi ya nuna shakku game da yiwuwar Kulusevski ya halarci gasar cin kofin duniya tun ranar Alhamis da ta gabata, amma ya bayyana cewa ɗan wasan zai koma ƙungiyar a wannan watan domin ci gaba da yin atisaye.

    Tottenham har yanzu tana fafutukar kaucewa daga faɗuwa a Premier League, kuma duk da cewa Kulusevski ba zai samu buga dukkan kakar 2025-26, akwai ƙyaƙƙyawan fata cewa zai murmure kafin fara kakar wasa mai zuwa.

  18. , Daga Jaridu

    Ɗan wasan Belgium Youri Tielemans, mai shekara 29, zai iya barin Aston Villa a ƙarshen kakar wasa ta bana. (Football Insider)

    Ɗan wasan gaba na Ingila Jarrod Bowen, mai shekara 29, zai iya ci gaba da zama a West Ham ko da kuwa ƙungiyar ta faɗo daga gasar Premier. (Teamtalk)

    Porto na da sha'awar ɗaukar Robert Lewandowski a kan cinikin kyauta a wannan bazarar amma har yanzu akwai yiwuwar ɗan wasan na Poland mai shekara 37 zai iya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da Barcelona. (Florian Plettenberg)

    Duk da cewa ya taimaka wa Nottingham Forest wurin guje wa faɗawa gasar Championship, akwai yiwuwar ƙungiyar za ta iya sallamar koci Vitor Pereira ta kuma maye gurbinsa da kocin Fulham Marco Silva a bazara. (Teamtalk)

    Kocin Bournemouth Andoni Iraola ya fice daga cikin masu takarar karɓar ragamar Manchester United yayin da a ke daf da naɗa Michael Carrick a matsayin koci na din-din-din a Old Trafford, wanda hakan ya sa Iraola ya samu damar tattauna guraben aiki a Crystal Palace da Chelsea. (Mail)

    Chelsea ta fara tattaunawa da tsohon kocin Real Madrid Xabi Alonso, kuma ta tuntuɓi Andoni Iraola da Marco Silva. (Times)

  19. Mahukuntan Man United za su bayar da shawarar naɗa Carrick, Manchester United

    Ana sa ran Michael Carrick, zai samu goyon bayan manyan jami’an Manchester United, domin a ba shi aikin kocin kungiyar na tsawon lokaci, inda za a miƙa sunansa ga Sir Jim Ratcliffe.

    Carrick mai shekara 44, an dade ana kallonsa a matsayin wanda ya fi kusa da samun aikin tun bayan da ya jagoranci United zuwa samun gurbin buga gasar Champions League ta kakar wasa mai zuwa, yayin da yake aikin rikon ƙwarya a matsayin babban koci.

    Tun farko United ta shirya jinkirta yanke hukunci kan wanda zai gaji, Ruben Amorim, wanda aka kora a watan Janairu.

    Sai dai, kamar yadda The Athletic ta ruwaito, ana ganin babban jami’in gudanarwa, Omar Berrada da daraktan ƙwallon ƙafa, Jason Wilcox sun yanke shawarar cewa Carrick ne ya dace da aikin, kuma za su sanar da Ratcliffe matsayinsu a wannan makon.

    Idan Ratcliffe ya amince, United za ta fara tattaunawa da Carrick kafin a tabbatar da makomarsa.

    Carrick ya ci wasa 10 cikin 15 da ya jagoranta, inda ya yi rashin nasara biyu daga ciki, lamarin da ya taimaka wa United hawa matakina uku a kan teburin Premier League daga ta bakwai tare da samun tikitin komawa buga gasar Champions League.

    Tun bayan naɗin Carrick a ranar 13 ga watan Janairu, babu wata ƙungiyar Premier League da ta tara maki fiye da 33 da Manchester United ta samu.

    Carrick ya jagoranci nasara a kan masu fatan kofin bana, kamar Manchester City da Arsenal, inda ya ci dukkan wasanninsa huɗu na farko da fara aikin.

    Wasa bakwai da ya yi a jereyana cin wasa yazo karshe ne a cikin watan Maris, amma daga baya ya samu nasarori masu muhimmanci a kan abokan hamayya wajen neman gurbin Champions League kamar Aston Villa da Chelsea da kuma Liverpool sun tabbatar da komawar United zuwa babbar gasar zakarun Turai.

    United na cikin rikici lokacin da aka kori Amorim, inda sakamako marasa kyau da saɓani kan dabarunsa da tsarin wasansa suka haddasa tsamin dangantaka tsakaninsa da jami’an ungiyar a ƙarshen zamansa na watanni 14.

    Sai dai Carrick, wanda ya taba horar da Man United na ɗan lokaci, bayan korar Ole Gunnar Solskjaer a 2021, ya daidaita al’amuran ya kuma burge mutane kan yadda ya mayar da ƙungiyar kan ganiya.

    Ya kuma samu yabo, saboda ƙoƙarinsa wajen bunƙasa matasa a Manchester United.

    Carrick ya sha jaddada cewa yana son yanke hukunci na dogon lokaci — har ma yana cikin tattaunawar sayen sababbin ƴan wasa — kuma wasu daga cikin ƴan wasan United sun nuna goyon bayansu a ba shi aikin dindindin.

    United ta kuma duba wasu masu horar da tamaula, kamar kocin tawagar Ingila, Thomas Tuchel da Luis Enrique na Paris Saint-Germain.

    Ƙungiyar da Carrick ke jan ragama za ta kammala kakar 2025-26 da wasa da Nottingham Forest a Old Trafford ranar Lahadi 17 ga watan Mayu, sannan ta je Brighton a ranar ƙarshe ta kakar wasa, 24 ga watan Mayu.

  20. , Daga Jaridu

    Juventus na tunanin ɗaukar aron dan wasan gaban Chelsea Nicolas Jackson. Ɗan wasan na Senegal, mai shekara 24, yana zaman aro ne a Bayern Munich amma ba zai ci gaba da zama da zakarun Jamus a kakar wasa mai zuwa ba. (Bild)

    Ƙungiyoyin Premier uku da suka haɗa da Liverpool da Newcastle, da Everton sun nuna sha'awa kan ɗan wasan gaban Ingila Jarrod Bowen, mai shekara 29, ko da kuwa West Ham ta kauce wa faɗawa matakin gasar Championship. (Mail)

    Liverpool na sha'awar ɗaukar ɗan wasan Monaco Magnes Akliouche, mai shekara 24, inda ɗan wasan na Faransa ke da farashin kusan fam miliyan 50. Shi ma abokin wasansa Lamine Camara yana jan hankalin ƙungiyar ta Anfield, amma za ta iya fuskantar hamayya daga Newcastle kan ɗan wasan tsakiyar Senegal mai shekara 22. (L'Equipe).

    Da alama Real Madrid za ta buƙaci sayar da ƴan wasa kafin ta kawo wasu sabbin fuskoki, inda ake ganin ɗan wasan tsakiyar Sifaniya Dani Ceballos, mai shekara 29, zai iya shiga cikin waɗanda za ta yi ƙoƙarin sallama a bazara mai zuwa. (The Athletic)