Kocin Brazil, Carlo Ancelotti, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa akwai yiwuwar ya tsawaita kwantiraginsa har zuwa shekarar 2030, duk da cewa wannan na iya zama aikinsa na ƙarshe a matsayin koci.
Ancelotti ya je Brazil ne da tarihin lashe Champions League sau biyar a matsayin koci, tare da ɗaukar kofunan lig a manyan ƙasashen Turai biyar, da kuma yin suna wajen iya sarrafa manyan ƴan wasa cikin nutsuwa.
Sai dai shekara guda bayan karɓar ragamar tawagar Brazil, ya fahimci cewa wannan aiki ya bambanta — ba kamar yadda ake shan wahalar horar da kungiya a kullum ba, sai dai cike yake da matsin lamba ga al’ummar da ke matukar ƙaunar ƙwallon ƙafa.
A yanzu, ɗan ƙasar Italy yana jin daɗin aikin horar da tawagar ƙasa, kuma ya ce batun tsawaita kwantiraginsa har zuwa 2030 ya kusa kammala.
Ancelotti ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekara ɗaya ne lokacin da ya zama kocin Brazil a watan Mayun bara, amma yanzu ana sa ran zai ci gaba da aikin bayan FIFA World Cup a Amurka da Canada da kuma Mexico..
Rahotanni sun ce Ancelotti na fuskantar matsin lamba wajen zaɓen tawagar Brazil da zai da su kofin duniya, musamman saboda yawaitar raunuka da kuma rashin tabbas kan lafiyar Neymar.
Kocin ya kuma jaddada muhimmancin aikin horaswa, yana cewa dole ne koci ya iya zama jagora, mai ba da shawara, da kuma wanda ƴan wasa za su iya yarda da shi.