China ta kori kociyanta, Ivankovic bayan kasa samun shiga kofin duniya a 2026
China ta kori, Branko Ivankovic bayan da kasar ta kasa samun tikitin shiga gasar kofin duniya da za a yi a 2026 a Amurka da Canada da kuma Mexico.
Ɗan kasar Croatia, mai shekara 71 ya ja ragamar China ta kare a mataki na biyar a rukuni na uku.
Ivankovic, wanda ya horar da Iran zuwa gasar kofin duniya a Jamus a 2006, ya fara aikin kociyan China a Fabrairun 2024, bayan maye gurbin Aleksandar Jankovic.
Ya kai China mataki na uku a Asia World Cup qualifying.
Hukumar ƙwallon kafa ta China ta ce Dejan Djurdjevic, wanda ya kai kasar kwata fainal a Asian Games ta matasa ƴan kasa da shekara 20 da aka yi a Fabrairu, zai yi aikin rikwan ƙwarya.