Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labaran abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni

Wannan shafi ne da zai kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 28 ga watan Yuni zuwa Juma'a 5 ga watan Yulin 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da Umar Mikail

  1. Thomas Partey zai bar Arsenal idan kwantiraginsa ya ƙare a farkon wannan makon bayan ɗan wasan Ghana mai shekara 32 ya kasa amincewa da sabuwar yarjejeniya da ƙungiyar ta arewacin Landan. (Athletic)

    Manchester United na ci gaba da zawarcin ɗan wasan Fiorentina da Italiya Moise Kean mai shekara 25, mai shekara 25, wanda ke ɗauke da farashin fam miliyan 44, a ƙunshe a cikin kwantiraginsa. (Corriere dello Sport)

    Arsenal na shirin hamayya da Chelsea da Liverpool, da kuma Manchester United wajen zawarcin ɗan wasan Eintracht Frankfurt ɗan kasar Faransa Hugo Ekitike mai shekara 23. (Sport Bild)

    Borussia Dortmund da Bayer Leverkusen da Eintracht Frankfurt da RB Leipzig da kuma Stuttgart na cikin jerin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan tsakiyar Manchester City da Ingila James McAtee mai shekara 22 . (Times)

  2. Gyokeres ya sanar da Sporting yana son motsawa

    Wannan ba labarin da ya shafi Gunners bane, amma za ta yi sha'awar jinsa.

    Ɗan wasan tawagar Sweden, mai shekara 27, Viktor Gyokeres ya sanar da Sporting cewar yana son barin ƙungiyar kan fara kakar 2025/26.

  3. Botafogo ta kori kociyanta, Renato Paiva

    Botafogo ta kori kociyanta, Renato Paiva bayan da aka fitar da ita daga Club World Cup da ake yi a Amurka, duk da ta doke mai rike da Champions League, Paris St Germain a wasannin cikin rukuni.

    Ƙungiyar da Paiva ya horar ta yi ban kwana da Club World Cup zagayen ƴan 16, bayan da takwararta daga Brazil, Palmeiras ta yi nasarar cin 1-0, kuma wata huɗu da ya fara jan ragama.

    Botafogo ta ja hankalin masu bibiyar tamaula, sakamakon da ta yi nasara a kan PSG da cin 1-0 a wasannin cikin rukuni da doke Seattele Sounders, wadda ta yi ta biyu a rukuni na biyu, duk da rashin nasara a hannun Atletico Madrid..

    Ƙungiyar ta godewa mai horarwar bisa nasara a kan PSG da kai wa zagayen ƴan 16 a Copa Libertadores da kuma Copa do Brasil.

  4. Wane gurbin Chelsea za ta yi amfani da Joao Pedro da Jamie Gittens

    Wani batun da ake ga Chelsea, wadda ta kammala kulla yarjejeniyar sayen Joao Pedro da Jamie Gittens, ana tunanin gurbin da za a yi amfani da su, bayan da ƙungiyar Stamford Bridge take da masu buga gaba da yawa.

    Jerin ƴan wasan gaba da Chelsea take da su:

    • Cole Palmer
    • Christopher Nkunku
    • Tyrique George
    • Pedro Neto
    • Noni Madueke
    • Raheem Sterling
    • Joao Felix
    • Nicolas Jackson
    • Liam Delap
    • Armando Broja
    • Marc Guiu
    • David Datro Fofana
    • Estevao Willian*
  5. Dortmund ta amince da tayin £55m da Chelsea ta yi wa Gittens

    Borussia Dortmund ta amince da tayin da Chelsea ta yi kan £55m, domin sayen Jamie Gittens, zai kuma je a auna koshin lafiyarsa a ƙungiyar dake buga Premier League.

    Mai shekara 20 ɗan wasan tawagar Ingila, ya amince da tayin kwantiragin kaka bakwai tun farko cikin watan Yuni.

    Ranar 10 ga watan Yuni, Dortmund ta ƙi amincewa da tayin £55m, wadda take za ta sallamar a £60m.

    Ana sa ran shi ne zai maye gurbin Jadon Sancho, wanda ya koma Manchester United, bayan buga wasannin aro, inda Chelsea za ta biya £5m.

  6. PSG ta kai kwata fainal bayan doke Inter Miami, PSG 4-0 Inter Miami

  7. Ronaldo ya ce ya zaɓi ya huta maimakon buga Club World Cup

    Cristiano Ronaldo ya ce ya zaɓi ya huta, maimakon ya buga Club World da ake a Amurka, wanda ya saka hannu a kan ɗan karen kwantiragi mai tsoka, domin ci gaba da taka leda a Al-Nassr.

    Ƙungiyar dake buga babbar gasar tamaula ta Saudiyya ta sanar ranar Alhamis cewar Ronaldo zai ci gaba da taka mata leda zuwa kaka biyu nan gaba.

    A watan jiya aka yi ta jita-jitar cewar ƙyaftin din tawagar Portugal zai buga Club World Cup, duk da cewar Al- Nassr ba ta samu tikitin shiga wasannin ba.

    Ronaldo ya ce ya zaɓi ya huta kan fara kakar tamaula ta Saudiyya da kuma kasarsa Portugal.

    Tsohon ɗan wasan Manchester United da Real Madrid da Juventus, ya ci ƙwallo a karawa da suka tashi 2-2 da Sifaniya, sannan suka lashe Nations League a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

    Ronaldo, wanda ya koma Al-Nassr a 2022, bayan barin Manchester United ya ci ƙwallo 93 a wasa 105 a dukkan fafatawa.

    Haka kuma Ronaldo na fatan cin ƙwallo dubu ɗaya nan gaba, ya zura 794 a raga a ƙungiyoyin da ya yi da kuma 138 da ya ci wa tawagar Portugal, jimilla yana da 932.

  8. Wataƙila sai Manchester United ta biya ƴanwasanta su bar ƙungiyar a wannan bazara saboda tsadar kwantiraginsu mai tsawo, yayin da ɗanwasa Marcus Rashford mai shekara 27 da takwaransa Alejandro Garnacho mai shekara 20 ke cikin ƴan wasan da kulob ɗin ke son cefanarwa. (Telegraph - subscription required)

    Sunderland ta amince ta biya Strasbourg fam miliyan 30 kan ɗanwasan Habib Diarra mai shekara 21 wanda ɗan asalin Senegal ne. (Guardian)

    Nottingham Forest ta yi tayin fam miliyan 5 kan ɗanwasan Real Mallorca Pablo Maffeo mai shekara 27. (El Chiringuito - in Spanish)

    Newcastle da Burnley sun kasa daidaitawa kan farashin James Traffordyayin da aka yi fatali da tayin da Magpies ta yi tun asali na fam miliyan 25 kan ɗanwasan Ingilan mai shekara 22. (Sky Sports)

  9. Kano Pillars za ta fara atisaye ranar Litinin, domin tunkarar kakar 2025/26

    Ƙungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars za ta fara atisaye a sanyin safiyar Litinin, domin tunkarar babbar gasar tamaula ta Najeriya ta 2025/26 da za a fara a cikin watan Agusta.

    Ƴan wasan Pillars sun yi hutu wata daya bayan da aka kammala kakar da ta wuce, inda sai masu gida ta kare a mataki na tara daga kungiya 20 da maki 53 daga fafatawa 38.

    Cikin wadanda ake sa ran za su koma atisaye har da Muttaka Musa, Abdullahi Abubakar, Fahad Usman, Dawud Ibrahim, Abdullahi Ali, Yusuf Bala Maigoro, Naziru Auwalu Ibrahim, Rabiu Ali, Aminu Adam Sani, Habibu Yakubu, Ahmed Musa, Mustapha Umar, Ibrahim Sani Halliru.

    Sauran sun hada da Jerry Alex, Umar Sani Yakasai, Auwal Ali Malam, Imran Ahmad, Sudais Ali Baba, Zaharadeen Bello, Shehu Abdullahi, Yusuf Abdullahi, Okeke Destiny Abuchi, Bright Emmanuel, Ibrahim Inuwa da kuma Mubarak Lawan.

    Haka kuma an daga likkafar wasu matasan yan wasa domin su bugawa babbar Kano Pillars tamaula da suka hada da Jibrin Yusuf, Aminu Muhammed, Mustapha Muhammed da kuma Muhammad Usman.

    Sannan sabbin yan wasan da ta dauka don tunkarar kakar 2025/26, za su fara karbar atisaye ranar Litinin, ciki har da Suleiman Idris Ibrahim daga Turai.

    Ana kuma sa ran nan da kwani Pillars za ta sanar da sabon kociya da zai ja ragamar kungiyar.

  10. An bai wa Chelsea damar ta ɗauko ɗanwasan Aston Villa Emiliano Martinez kan fam miliyan 45 duk da cewa ana tunanin golan na Argentina ɗan shekara 32 zai fi karkata ga komawa Manchester United. (Mirror)

    Manchester United ta shirya fara tattaunawa kan yarjejeniyar sayen Martinez idan suka cefanar da golan Kamaru Andre Onana mai shekara 29. (Football Insider)

    Za a duba lafiyar ɗanwasan Liverpool mai shekara 22 Jarell Quansah a Bayer Leverkusen ranar Litinin kafin sayen shi kan fam miliyan 35. (Fabrizio Romano)

    Liverpool ta kusa daidaitawa kan sayen ɗanwasan Crystal Palace mai shekara 24 Marc Guehi. (Mirror)

  11. Shawara ce mafi muni da aka ƙirƙiri Club World Cup - Klopp

    Tsohon kociyan Liverpool, Jurgen Klopp ya ce gasar Club World Cup shawara ce mafi muni da aka ƙirƙiri wasannin.

    An fara Club World Cup da aka sauya mata fasali da ƙungiya 32 da aka fara a cikin watan a Amurka da za a karkare ranar 13 ga watan gobe a birnin New York.

    Lokacin zai rage saura wata ɗaya a fara Premier League, inda Liverpool mai rike da kofin za ta fara wasan farko ranar 15 ga watan Agusta.

    Klopp ya yi korafi kan yawan wasannin da ƴan ƙwallo ke bugawa da cewar ya yi musu yawa, duk da ɗan karen kuɗi da ƙungiyoyi za su karba.

    Ɗan kasar Jamus ya ce yadda za ka fahimci wasannin gasar tamaula ya yi yawa shi ne a bara an buga Copa America ga gasar cin kofin nahiyar Turai ga Club World Cup da ake yi, sannan za a buga gasar cin kofin duniya a baɗi a Amurka da Canada da kuma Mexico.

  12. Bellingham ya cika shekara 22 da haihuwa ranar Lahadi

    Ɗan wasan Real Madrid, Jude Bellingham ya cika shekara 22 da haihuwa ranar Lahadi.

    An haifi ɗan wasan tawagar Ingila ranar 29 ga watan Yunin 2003.

    Ya koma Real Madrid a kakar 2023, wanda yanzu haka ya buga wasa 97 da cin ƙwallo 39.

    Ya kuma lashe Champions League da La Liga da kuma Spanish Super Cup a Real Madrid.

    Ya koma Sifaniya daga Borussia Dortmund, wanda ya fara wasa a Real Madrid ranar 12 ga watan Agustan 2023 a karawa da Athletic Club.

  13. An sallami ƴar wasan tawagar Sifaniya, Bonmati daga Asibiti

    An sallami ƴar wasan tawagar Sifaniya, Aitana Bonmati daga asibiti, bayan rashin lafiya.

    Za a fara gasar cin kofin nahiyar Turai Euro 2025 ranar Laraba, yayin da ake sa ran mai shekara 27 za ta koma sansanin tawagar, domin tunkarar kalubalen dake gaban kasar.

    Tawagar Sifaniya, mai rike da kofin duniya za ta fara wasa a rukuni na biyu da Portugal a Bern.

    Bonmata, mai taka leda a Barcelona ba ta buga wasan sada zumunta ba ranar Juma'a da Sifaniya ta doke Japan 3-1.

  14. Crystal Palace ta shirya gogayya da Newcastle da Liverpool da Tottenham a zawarcin ɗanwasan Southampton mai shekara 19 Tyler Dibling a wannan bazarar. (Football Insider)

    Nico Williams ya shaida wa Barcelona cewa yana son ya koma ƙungiyar daga Athletic Bilbao sai dai ɗanwasan na Sifaniya mai shekara 22 ya nemi a yi masa rajistar buga wasa wanda hakan na iya nufin sai Barca ta fara cefanar da ƴan wasanta don ta iya biyan buƙatun La Liga. (Marca - in Spanish)

    Tuni Al-Nassr ta ƙulla yarjejeniyar tura ɗanwasanta Jhon Duran mai shekara 21 zaman aro a Fenerbahce. (Foot Mercato - in French)

  15. Dominic Calvert-Lewin zai bar Everton

    Dominic Calvert-Lewin zai bar Everton, bayan da ya yanke shawara mai tsauri.

    Mai shekara 28, dan wasan tawagar Ingila, yarjejeniyarsa za ta kare a ƙungiyar ranar Litinin.

    Calvert-Lewin ya koma Everton daga Sheffield United kan £1.5m a 2016, ya ci ƙwallo 71 a wasa 273 a ƙungiyar.

  16. Pogba ya koma Monaco kan yarjejeniyar kaka biyu

    Tsohon ɗan wasan Manchester United da kuma Juventus, Paul Pogba ya koma Monaco kan yarjejeniyar kaka biyu.

    Mai shekara 32 ya koma a matakin wanda bai da kwantiragi tun daga watan Nuwamba, bayan da Juventus ta soke yarjejeniyar da take tsakaninsu.

    Tun farko an dakatar da Pogba shekara huɗu, sakamakon zargin shan abubuwan kara kuzarin wasa a Maris ɗin 2024.

    Amma yanzu zai koma taka leda bayan da aka rage hukuncin zuwa wata, sakamakon ɗaukaka kara a watan Oktoba.

    Ya fara taka leda a Manchester United daga nan ya koma Juventus a 2012.

  17. Mbappe na samun sauki, bayan da Real za ta kara da Juv

    Kylian Mbappe na murmurewa, bayan da Real Madrid ke shirin buga zagaye na biyu a Club World da za ta fafata da Juventus.

    Ranar Talata Real Madrid za ta fuskanci ƙungiyar da ke buga Serie A a filin wasa na Hard Rock a Miami Gardens, wadda take fatan Mbappe zai buga mata karawar.

    Ɗan kasar Faransa bai buga wasa ko ɗaya ba, sakamkon rashin lafiya, wanda bai yi karawar da Real ta tashi 1-1 da Al-Hilal da 3-1 da ta doke Pachuca da 3-0 da ta yi nasara a kan RB Salzburg, wadda ta ja ragamar rukuni na takwas.

  18. Danilo ya ce kowa zai iya cin kowa tsakanin Flamengo da Bayern Munich

    Mai tsaron bayan Flamengo, Danilo ya ce kowa zai iya kai wa zagaye na biyu a Club World Cup a wasan da za su buga da Bayern Munich.

    Flamengo za ta fuskanci ƙungiyar Jamus ranar Lahadi zagayen ƴan 16 a filin wasa na Hard Rock a Miami.

    Ƙungiyar Brazil ta ja ragamar rukuni na huɗu, ciki har da doke Chelsea 3-1.

    ita kuwa Bayern Munich ta kare a mataki na biyu a rukuni na uku, bayan rashin nasara 1-0 a hannun Benfica duk da doke Aucland City 10-0 da cin Boca Junior 2-1 a sauran wasannin cikin rukuni.

  19. An naɗa Kuyt a matakin kociyan FC Dordrecht

    Tsohon ɗan wasan Liverpool, Dirk Kuyt ya zama kociyan Dordrecht mai buga gasa mai daraja ta biyu a Netherlands.

    Tsohon ɗan wasan tawagar Netherlands, wanda ya taka leda a Feyenoord da Fernerbahce an kore shi a Beerschot a makon jiya, bayan da ta kare ta karshe a teburi, sannan ta faɗi daga gasar.

    Kuyt ya kai ƙungiyar babbar gasar tamaula ta Netherland a baya.

  20. Gwiwar Manchester United da Newcastle da Tottenham ta yi sanyi a zawarcin ɗanwasan Ghana Antoine Semenyo mai shekara 25 yayin da Bournemouth ke neman fam miliyan 70 kafin cefanar da shi. (The I - subscription required)

    Arsenal na fatan daidaitawa kan yarjejeniyar sayen ɗanwasan Sifaniya mai shekara 21 Cristhian Mosquera bayan tattaunawa da Valencia. (Guardian)

    Ɗanwasan tsakiya na Kamaru Bryan Mbeumo mai shekara 25 ya sanar da Brentford da Tottenham kan matakinsa na ƙulla yarjejeniya da Manchester United a bazara. (The Athletic - subscription required)

    Ɗanwasan Everton mai shekara 23 Jarrad Branthwaite ya shirya sabunta kwantiraginsa da shekara biyar yayin da kulob ɗin ke fatan ɗanwasan tsakiya na Senegal Idrissa Gueye mai shekara 35 zai sa hannu kan kwantiragin shekara ɗaya. (Times - subscription required)