Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labaran abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni

Wannan shafi ne da zai kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 28 ga watan Yuni zuwa Juma'a 5 ga watan Yulin 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da Umar Mikail

  1. Sifaniya za ta kara da Portugal ranar Alhamis a Euro 2025

    Yar wasan tawagar Sifaniya, Aitana Bonmati ta fara atisaye, bayan fama da jinya, bayan da kasar ke shirin wasan farko a gasar cin kofin nahiyar Turai Euro 2025 da za a yi a Switzerland.

    Mai taka leda a Barcelona ta ziyarci otal din Sifaniya daga baya ta mota jiki ranar Talata.

    Bonmati, mai rike da kyautar Ballon d'Or, ba ta buga wa Sifaniya wasan sada zumuntar da ta doke Japan 3-1 ranar Juma'a ba.

    Sifaniya za ta kara da Portugal ranar Alhamis a wasan cikin rukuni na biyu.

    Bonmati ta ci kwallo 30 a wasa 78 a tawagar Sifaniya mai rike da kofin duniya a 2023.

    Ingila ce mai Euro 2022 da ta lashe a gasar da ta gudanar a Wembley

  2. Chelsea ta ɗauki Pedro, zai kuma iya buga mata Club World Cup

    Chelsea ta kammala sayen Joao Pedro daga Brighton, watakila ya buga mata Club World Cup da za ta kara da Palmeiras a zagayen kwata fainal.

    Ɗan wasan tawagar Brazil, ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka takwas kan £60m.

    Mai shekara 23 ya je Amurka, inda aka auna koshin lafiyarsa, yanzu yana da damar yi wa Chelsea karawar da za ta yi da Palmeiras ranar Asabar a Philadelphia.

    Matashin da ya fara taka leda daga Fluminense ya ci ƙwallo 30 a wasa 70 da ya buga wa Brighton, tun bayan da ya koma ƙungiyar dake buga Premier League daga Watford a 2023 kan £30m.

    Haka kuma Borussia Dortmund ta amince da tayin da Chelsea ta yi na kan £55m ga ɗan wasan tawagar Ingila, Jamie Gittens.

    Sai dai mai shekara 20 ba zai iya buga wa Chelsea Club World Cup ba, saboda ya wakilci Dortmund a wasannin.

    Haka kuma Chelsea ta ɗauki Liam Delap da Mamadou Sarr da Dario Essugo, tun kan fara gasar, waɗanda ta yi musu rijistar buga mata Club World Cup.

  3. Iyalan Berlusconi za su tsame hannunsu a harkar tamaula

    Iyalan Berlusconi sun amince za su sayar da AC Monza ga wani kamfanin zuba hannun jarin Amurka, Beckett Layne Ventures.

    Idan aka kammala cinikin hakan zai kawo karshen hannun iyalan Berlusconi a fannin tamaula, bayan da Silvio Berlusconi ya mutu a 2023, wanda ya yi minista karo hudu a Italiya kuma hamshakin dan kasuwa.

    Silvio Berlusconi, wanda ya mallaki AC Milan, ya sayi Monza a 2018, wadda a lokacin tana buga gasa mai daraja ta uku a Italiya.

    Sai dai a kulawar tsohon jami'in AC Milan, Adriano Galliani ya kai Monza, wadda take Arewacin Milan zuwa Serie A a 2022, amma ta fadi gasar a kakar da ta wuce.

    Monza ita ce kungiya ta kwanan nan daga Italiya da za a sayar da ita ga masu zuba hannun jari daga Amurka, bayan Inter Milan da AC Milan da Roma da Parma da Fiorentina da kuma Hellas Verona.

  4. Bayern Munich na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan gaban Manchester United da Ingila Marcus Rashford, mai shekara 27, bayan ta yi amanna da hazaƙar da ya nuna a zaman aron da ya yi a Aston Villa a kakar da ta gabata. (Sun)

    Arsenal na dab da ƙulla yarjejeniya da ɗan wasan gaba na Sporting Viktor Gyokeres. Ɗan ƙasar Sweden mai shekara 27 ya shaidawa kulob ɗinsa cewa yana son ya koma Gunners. (L'Equipe)

    Crystal Palace ta cimma yarjejeniya kan farashin fam miliyan 47 don siyan Ousmane Diomande, mai shekara 21, daga Sporting, inda ake ganin ɗan wasan baya na Ivory Coast zai iya maye gurbin ɗan wasan Ingila Marc Guehi mai shekara 24 . (A Bola)

    Manchester United ta tuntuɓi Inter Milan game da cinikin ɗan wasan Italiya Davide Frattesi, mai shekara 25. (Caught Offside)

  5. Ɗan wasan Liverpool, Quansah ya kammala komawa Leverkusen

    Dan wasan Liverpool, Jarrell Quansah ya kammala komawa Bayern Leverkusen kan yarjejeniyar kaka biyar kan £35m.

    Wasa 13 ya buga a Premier League da ta wuce, jimilla ya yi karawa 58 tun daga lokacin da ya fara taka mata leda daga makarantar koyon tamaula ta Liverpool.

    An yi wa Liverpool tayin ɗan wasan ga Newcastle da cewar za a yi musaya da Anthony Gordon domin ya koma Anfield.

  6. Arsenal ta tattauna da wakilan ɗan wasan tsakiya na Crystal Palace da Ingila Eberechi Eze, mai shekara 27, wanda ke da farashin fam miliyan 67.5. (Guardian)

    Ɗan wasan Aston Villa da Ingila Ollie Watkins, mai shekara 29, yana cikin jerin ƴan wasan da Manchester United ke nazari a kai idan ɗan ƙasar Denmark Rasmus Hojlund, mai shekara 22, ya bar Old Trafford a bazara. (Athletic)

    Bayern Munich ta sanya ɗan wasan gaban Liverpool da Colombia Luis Diaz, mai shekara 28, a jerin sunayen ƴan wasan da ta ke bibiya yayin da ta ke ci gaba da neman ɗan wasan gaba mai kai hari ta gefen hagu. (Sky Germany)

    Fulham na shirin fara zawarcin ɗan wasan gaba na Genk da Najeriya Tolu Arokodare, mai shekara 24, wanda Manchester United da AC Milan ke sanya wa ido. (Sun)

  7. Sakamakon wasannin damben gargajiya da aka buga ranar Litinin a gidan wasa da ke Ado Bayero Square a Kano Nigeria.

    An tashi canjaras tsakanin Dogon Shamsu da Shagon Bata jemu ba da na Dogon Musa da Gaba bakwai baya bakwai da na Bahagon Biyu da Dan dabar Autan dan Bunza da na Alasan Shagon Bahagon yan Sanda da Shagon bata jemu ba.

    Garkuwan Bahagon Musan Kaduna ya buge Dogon Shagon Audu Kai ga yan dambe rauni targade karaya Allah ya kare

  8. West Ham za ta saurari tayin kusan fam miliyan 60 kan Kudus, wanda ke jan hankalin Chelsea da Newcastle da Manchester United. (Guardian)

    An bai wa ɗan wasan gaban Brazil Richarlison, mai shekara 28, damar barin Tottenham kuma ana tunanin zai nufi Turkiyya domin komawa Galatasaray. (Sun)

    Chelsea na fatan samun kusan fam miliyan 35 idan ta yi nasarar cefanar da ɗan wasan gaban Faransa Christopher Nkunku, mai shekara 27 a wannan bazarar. (Metro)

  9. Wasannin kwata fainal a Club World Cup

    Wasannin kwata fainal a Club World Cup

    • 4 Yuli: Fluminense v Al-Hilal
    • 5 Yuli: Palmeiras v Chelsea
    • 5 Yuli: PSG v Bayern Munich
    • 5 Yuli: Real Madrid ko Juventus da Borussia Dortmund ko kuma Monterrey
  10. Labarai da dumi-dumi, Arsenal ta kammala ɗaukar Kepa Arrizabalaga

    Arsenal ta kammala ɗaukar ɗan kasar Sifaniya, mai tsaron raga, Kepa Arrizabalaga daga Chelsea.

    Tun farko mai shekara 30-yana da sauran yarjejeniya a Stamford Bridge da za ta karkare a karshen watan Yunin 2026.

    Ya buga wasannin aro a kaka biyu baya a Real Madrid da Bournemouth, yanda ya yi kaka bakwai a Chelsea.

  11. Ƴan Premier League da ƙwantiraginsu ya kare 1 ga watan Yuli

    Ga jerin ƴan wasan Premier League da yarjejeniyarsu ya kare daga ranar 1 ga watan Yuni.

    Arsenal: Thomas Partey

    Aston Villa: Kortney Hause

    Brentford: Josh Dasilva, Ben Mee

    Brighton: Ba ko ɗaya

    Bournemouth: Ba ko ɗaya

    Burnley: Ashley Barnes, Josh Brownhill, Michael Obafemi, Nathan Redmond, Jonjo Shelvey

    Chelsea: Lucas Bergstrom

    Crystal Palace: Joel Ward

    Everton: Asmir Begovic, Dominic Calvert-Lewin, Abdoulaye Doucoure, Idrissa Gueye, Michael Keane, Joao Virginia, Ashley Young

    Fulham: Tom Cairney, Kenny Tete, Carlos Vinicius

    Leeds United: Sam Byram, Junior Firpo, Josuha Guilavogui

    Liverpool: Ba ko ɗaya

    Manchester City: Scott Carson

    Manchester United: Christian Eriksen, Victor Lindelof

    Newcastle United: Jamaal Lascelles, Jamal Lewis, John Ruddy, Callum Wilson

    Nottingham Forest: Wayne Hennessey, Harry Toffolo

    Sunderland: Ba ko ɗaya

    Tottenham Hotspur: Fraser Forster, Sergio Reguilon, Alfie Whiteman

    West Ham: Michail Antonio*, Vladimir Coufal, Aaron Cresswell, Lukasz Fabianski, Danny Ings

    Wolves: Craig Dawson, Nelson Semedo

  12. Mutum na huɗu ya mutu a haɗarin sitadiya a Algeria

    Mutum na hudu ya mutu sakamakon fadowa daga bene a sitadiya, bayan da MC Alger ta lashe babban kofin tamaula na Algeria, kamar yadda kungiyar ta sanar ranar Litinin.

    Na hudun ya mutu a asibiti, bayan da aka yi masa aiki kan raunukan da ya samu a hadarin da ya faru ranar 21 ga watan Yuni.

    Wani dan kallo ne ya fara mutuwa daga baya biyu suka ce ga garun kunan, sakamakon munanan raunukan da suka ji.

    Wasu kafafen labaran kasar sun ce shingen da dubban magoya baya da suka jingina ne ya karye da ta kai da dama suka fado kasan tsandauri da ta kai an rasa rai da wadanda suka jikkata.

  13. John Textor ya ajiye jagorancin Lyon

    Ɗaya daga mamallakin Crystal Palace, John Textor ya ajiye aikin daya daga shugabannin Lyon.

    Ɗan Amurka ya amince zai sayar da hannun jarinsa da ya kai kaso 43 cikin 100 a Palace da Woody Johnson mai New York Jets, yana da hannun jarin kaso 77 cikin 100 a Lyon ta Faransa.

    Lyon za ta koma buga gasa mai daraja ta biyu ta Faransa, saboda yanayi mara kyau a huldar kasuwancin ƙungiyar.

  14. Tawagar Ingila za ta kare kofin Nahiyar Turai a Switzerland

    Switzerland ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a filaye takwas daga biyu ga watan Yuli zuwa 27 ga watan gobe.

    Filayen sun hada da Basel da Bern da Geneva da Zurich da St. Gallen da Sion da Lucerne da kuma Thun, inda za a yi wasan bude labulen gasar a birnin Basel a filin wasa na St-Jakob.

    Ingila mai rike da kofin ta lashe shi a 2022, bayan doke Jamus a karawar karshe a fafatawar da ta gudanar a Wembley.

    Rabon da Switzerland ta karbi bakuncin babbar gasar tamaula tun 2008, lokacin da ta yi hadakar shirya wasannin maza a gasar cin kofin nahiyar Turai da makwabciyarta Austria.

  15. Alcaraz ya kai zagaye na biyu a Wimbledon Open

    Mai rike da kofin Wimbledon Open Carlos Alcaraz ya kai zagaye na biyu, mai garand Slam biyar mai Wimbledon biyu a jere dan kasar Sifaniya ya caskara Fabio Fognini da cin 7-5 6-7 7-5 2-6 6-1.

    Shi kuwa dan kasar Girka, Stafanos Tsitsipas ya sanar cewar bai da amsar da zai bayar kan rashin kuzarinsa, wanda ya hakura da gasar ta Wimbledon ana tsaka da wasa, saboda ciwo bayan a lokacin da yake rashin nasara 6-3 6-2 a hannun Valentin Royer.

    Shi kuwa Danil Medvedev an yi waje road da shi a zagayen farko, bayan da dan kasar Fransa Benjamin Bonzi, wanda bai taba cin wasan tennis ba a kan ciyawa a shekara uku baya, yayi nasarar cin 7-6 3-6 7-6 da kuma 6-2.

    Medveded dan kasar Rasha ya kai zagayen daf da karshe har karo biyu a wasannin da ake yi a All Engalnd Club.

  16. Crystal Palace na shirin gabatar da tayin fam miliyan 27 don ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Ingila Hayden Hackney, mai shekara 23, da ɗan wasan baya na Holland Rav van den Berg, mai shekara 20 daga Middlesbrough (Sun).

    Manchester United na fafutukar ganin ta sallami Tyrell Malacia, mai shekara 25, bayan PSV Eindhoven ta ƙi amincewa da damar sayen ɗan wasan kan kwantiragin dindindin bayan zaman aro da ya yi a kulob ɗin. (Mirror)

    Aston Villa na shirin sallamar matasa ƴan wasa Louie Barry da Kaine Kesler-Hayden, dukkansu masu shekara 22, zuwa ƙungiyoyin Hull da Coventry na gasar Championship. (Athletic)

  17. Abraham zai koma Besiktas daga Roma kan £17million

    Tsohon ɗan wasan Chelsea, Tammy Abraham na daf da komawa Besiktas daga Roma.

    Mai shekara 27, ya buga wa tawagar Ingila karawa 11, ya yi wasannin aro a AC Milan da cin ƙwallo 10.

    Ana sa ran zai je ya saka hannu kan yarjejeniyar £17million, domin komawa buga babbar gasar tamaula ta Turkiya.

    Abraham ya yi wasannin aro a Aston Villa daga nan ya koma Roma kan £34million a 2021, ya lashe Europa Conference League karkashin Jose Mourinho.

  18. Rashford ya koma United bayan wasannin aro a Aston Villa

    Marcus Rashford ya koma Manchester United bayan kammala wasannin aro a Aston Villa.

    Mai shekara 27-ya koma Villa a watan Janairu, bayan kalubalan da ya fuskanta a zagayen farko a kakar da ta wuce a Old Trafford.

    Lokacin da ya taka leda a Villa Park, Rashford ya yi karawa 17 a dukkan fafatawa da cin ƙwallo huɗu da bayar da shida aka zura a raga.

    United ta koma yin atisaye ranar Litinin, wadda za ta buga wasan sada zumunta da Leeds United a Sweden ranar Asabar 19 ga watan Yuli.

  19. Johnny Evans ya yi ritaya United ta ba shi aiki

    Manchester United ta bai wa Jonny Evans ragamar farauto mata matasan yan wasa masu baiwa, bayan da ya sanar da yin ritaya.

    Mai shekara 37 ya lashe Champions League da Premier League da FA Cup da League Cups a karo biyu da ya taka leda a kungiyar ta Old Trafford.

    Evans, ya buga wa tawagar Ireland ta Arewa wasa 107, ya fara wasa daga makarantar koyon tamaula a United, ya kuma yi wa babbar kungiya fafatawa 241.

  20. Giroud zai koma Lille da taka leda

    Ɗan wasan tawagar Faransa, Olivier Giroud na daf da komawa buga gasar Ligue 1 a ƙungiyar Lille, bayan barin Los Algeles mai buga babbar gasar tamaula ta Amurka, wato Major League Soccer.

    Mai shekara 38, wanda shi ne kan gaba a yawan ci wa Faransa ƙwallaye mai 57 a raga, ya taka leda a Arsenal da Chelsea da kuma AC Milan daga nan ya koma LAFC a bara.

    Ya taimaka ta lashe Open Cup a karon farko da cin ƙwallo a watan Satumba.

    A makon jiya LAFC ta sanar da tafiyar Geroud.