Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/11/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/11/2024

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Annur Muhammad Annur da Isiyaku Muhammed

  1. Majalisar zartaswar Isra'ila za ta tattauna buƙatar tsagaita wuta ta kwana 60 a Lebanon

    Netanyahu

    Asalin hoton, Reuters

    Majalisar zartaswar ƙasar Isra'ila za ta tattauna tsagaita wuta ta kwana 60 a ƙasar Lebanon, duk da cewa a jiya Litinin ma dukkan ɓangarorin biyu sun kai wa juna hare-hare.

    Tun a ranar 8 ga watan Oktoba ne ake ɓarin wuta a tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hezbollah, tun bayan da ƙungiyar ta Hezbollah ta harba wasu rokoki a Isra'ila.

    Sai dai yaƙin ya ƙara ƙazancewa ne bayan Isra'ila ta kutsa kudancin Lebanon ta ƙasa kimanin wata biyu da suka gabata.

  2. Ana cigaba da neman waɗanda suka ɓace bayan kifewar jirgin ruwa a Masar

    Jirgin ruwa

    Asalin hoton, Red Sea Governorate

    Hukumomi a ƙasar Masar sun ce mutum 16 sun ɓace, ciki har da ƴanƙasashen waje, sannan an ceto 28 bayan wani jirgin ruwan ƴan yawon buɗe ido ya nutse a tekun Bahar Maliya.

    Huɗu daga cikin waɗanda ake neman ƴan Masar ne yayin da sauran sha biyun yanƙasashen waje ne, ciki har da masu yawon buɗe ido ƴan ƙasar Finland da Birtaniya.

    Wakiliyar BBC ta ce hukumomin Masar sun ce mutum 44 ne cikin jirgin, sha uku daga ciki ma'aikatan jirgin ne yayin da sauran talatin da ɗaya masu yawon buɗe ido ne.

    Hukumomin ƙasar ba su bayyana dalilin da ya haddasa nutserwar jirgin ba, sai dai bayanai daga waɗanda suka tsira sun nuna cewa igiyar ruwa ce ta afkawa jirgin da ya yi sanadin kifewarsa.

    Masu hasashen yanayi sun yi gargaɗi game da tafiya kan teku a ranar Lahadi da Litinin.

  3. Trump zai sa harajin kashi 25 kan kayayyakin Mexico da Canada

    Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Zaɓaɓɓan shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump ya ce zai sa harajin kashi ashirin da biyar kan dukkan kayan da aka shigar Amurka daga Mexico da Canada a ranar farko ta shugabancinsa.

    A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya ce zai ƙaƙaba harajin har zuwa lokacin da Mexico da Canada za su dakatar da shigar da ƙwayoyi da kuma kwararar baƙi ƙasar ta kan iyakokinsu.

    Mista Trump ya kuma yi alƙawarin ƙara kashi goma kan harajin kayan Chana har ita ma sai ta dakatar da fataucin ƙwayoyin zuwa Amurka.

    Wakilin BBC ya ce a lokacin yaƙin neman zaɓensa, Trump ya yi barazanar sanya harajin kashi ɗari na kayan da ake shigarwa Amurka daga Mexico da Chana madamar ba su yi abun da ya dace ba.

    A nata martanin, Chana ta ce tana ɗaukar matakin daƙile fataucin miyagun ƙwayoyi tun bayan yarjejeniyar da aka cimmawa tsakanin Shugaba Biden da takwaransa na Chanar, Xi Jinping.

  4. Shugabannin Najeriya suna hawa mulki ba tare da sun shirya ba - Bishop Kukah

    Kukah

    Asalin hoton, Others

    Ɗaya daga cikin shugabannin cocin Katolika a Najeriya ya ce abin da ya sa ƙasar ke fuskantar matsaloli wajen bunƙasar tattalin arziki shi ne galibin waɗanda ke samun shugabancin ƙasar suna hawa mulki ne ba tare da shiri ba.

    Bishop Mathew Hassan Kukah, wanda shi ne shugaban cocin Katolika a yankin Sokoto ya bayyana hakan, inda ya ƙara da cewa rashin ingantaccen shiri da kuma kyakyawan tsari daga wajen waɗannan shugabannin na bayyana ne jim kaɗan bayan sun ɗare kan madafan iko.

  5. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da war haka, barkanmu da sake saduwa a wannan shafinmu na kai-tsaye daga nan sashen Hausa na BBC.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.