Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/11/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/11/2024

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Annur Muhammad Annur da Isiyaku Muhammed

  1. Isra'ila da Lebanon sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta - Biden

    Joe Biden

    Asalin hoton, US POOL

    Isra'ila da Lebanon sun amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta domin kawo ƙarshen fada da ƙungiyar Hezzbollah, a cewar shugaban Amurka Joe Biden.

    Da yake magana daga fadar White House, shugaba Biden ya ce yana da "albishir" kuma "ya ji dadin sanar" da cewa bayan ya yi magana da firaministocin Isra'ila da Lebanon, sun amince da yarjejeniyar.

    Lokacin da yarjejeniyar ta fara aiki, Biden ya ce: "Za a kawo ƙarshen faɗan. Za a kawo ƙarshen yaƙin.

    Ya sake nanata cewa nan ba da jimawa fararen hula daga ɓangarorin biyu za su samu damar komawa yankunansu cikin koshin lafiya.

    Amurka, tare da Faransa da kawayenta, sun yi alƙawarin yin aiki tare da Isra'ila da Lebanon don tabbatar da "cikakkiyar" aiwatar da yarjejeniyar, in ji shi.

    Ya kuma tabbatar da cewa babu wani sojan Amurka da zai shiga cikin lamarin.

    Dangane da Gaza, ya ce mutanen da ke wurin ma sun cancanci a kawo karshen fadar da ake yi a yankin.

  2. Ministan Isra'ila ya ce yana adawa da yarjejeniyar tsagaita wuta

    Itamar Ben-Gvir

    Asalin hoton, Reuters

    Ministan tsaron Isra'ila Itamar Ben-Gvir ya ce yana adawa da shirin tsagaita bude wuta da aka cimma tsakanin ƙasarsa da ƙungiyar Hezbollah, yana mai cewa yarjejeniyar ba ta tabbatar da komawar ƴan Isra'ila zuwa arewacin ƙasar ba.

    Ben-Gvir wanda ɗan ra'ayin riƙau ne na gwamnatin Netanyahu ya ce sojojin Lebanon ba su da ƙarfin da za su iya murƙushe Hezbollah. Ya nace cewa "dole ne Isra'ila ta tabbatar da tsaronta" kafin barin Lebanon.

    "Bai kamata mu amince da kowa ba sai kanmu," in ji shi.

    Da yake magana tun farko, firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce a shirye yake ya aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta, kuma zai mayar da martani mai tsanani kan duk wani yunƙurin saɓa yarjejeniyar da Hezbollah za ta yi.

  3. Hare-haren Isra'ila sun kashe mutum uku a tsakiyar birnin Beirut

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Isra'ila ta kai wani mummunan hari a kudancin birnin Beirut, a daidai lokacin da ake sa ran majalisar ministocin tsaron Isra'ila ta tattauna batun tsagaita wuta da ƙungiyar Hezbollah.

    Hare-haren da aka kai a Dahieh, yankin da Hezbollah ke da hedkwatarta ​​a babban birnin ƙasar, ya zo ne bayan da sojojin Isra'ila suka ba da sanarwar ficewa daga gine-gine 20. Hotunan da aka watsa a gidajen talabijin sun nuna yadda hayaki ya turnuƙe yankin.

    Kimanin minti 30 kafin wannan lokacin, an kai wani hari ta sama a Nuweiri, a tsakiyar birnin Beirut, ba tare da gargaɗi ba, wanda ke nuni da yuwuwar yunƙurin kashe wani jigon Hezbollah.

    Ya zuwa yanzu dai babu wani bayani daga sojojin Isra'ila.

    Aƙalla gini ɗaya ya ruguje, kuma hotuna sun nuna jama'a na binciken baraguzan ginin.

    Aƙalla mutane uku ne suka mutu sannan wasu fiye da 20 suka jikkata, a cewar ma'aikatar lafiya ta ƙasar Lebanon.

  4. Gwamnati jihar Sokoto za ta bai wa makarantu tallafi domin inganta ilimi

    ...

    Asalin hoton, Sokoto Govt. House

    Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya sanar da cewa gwamnatin Jihar za ta bai wa shigabannin makarantu tallafin naira 200,000 kowane wata domin inganta ɓangaren ilimi a jihar.

    A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook gwamnan ya bayyana cewa tallafin zai taimakawa shugananin makarntun wurin don aiwatar da sabbin shirye-shiryen ilimi, waɗanda za su haifar da ingantattun sakamako ga ɗalibai, da kuma ƙara kuzari da ɗabi'a a tsakanin ma'aikata.

    Gwamna Aliyu ya ce ''Bayar da tallafin kuɗi ga shugabannin makarantu zai haɓaka kwarin gwiwarsu, tare da ƙarfafa su don ɗaukar nauyi mafi girma wajen haɓaka ingantaccen yanayin makaranta.''

    Ya ƙara da cewa tallafin zai taimaka wurin haɓaka ƙwarewar ma'aikatan makaranta, wanda zai haifar da ingantattun malamai waɗanda za su iya ba da ilimi mai inganci.

    ''Ta hanyar mayar da hankali kan jagorancin makaranta, wannan yunƙurin yana ƙarfafa gwiwar al'umma wurin shiga a dama da su a harkar ilimi wanda zai haɓaka haɗin gwiwar da zai amfanar da ɗalibai da kuma makarantu.'' in ji shi

  5. Majalisar tsaron Isra'ila za ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta - Netanyahu

    Benjamin Netanyahu

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce majalisar tsaronsa za ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta domin kawo karshen faɗa da ƙungiyar Hezbollah a Lebanon.

    A ƙarƙashin yarjejeniyar, ya ce, duk wani yunƙurin da ƙungiyar Hezbollah za ta yi na sake tattara makamai zai zama saɓawa yarjejeniyar, kuma Isra'ila za ta mayar da martani mai tsanani idan hakan ya faru.

    Ya ƙara da cewa idan ƙungiyar Hezbollah ta saɓa yarjejeniyar, Isra'ila za ta kai hari.

    Shugaban na Isra'ila ya ce wasu sun gargade shi cewa tsagaita wuta na nufin Isra'ila ba za ta iya komawa Lebanon ba idan har tana buƙatar hakan. Netanyahu ya ƙare da cewa "ana iya aiwatar da yarjejeniya kuma za mu tabbatar da hakan".

  6. Ana dab da ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon - Blinken

    Antony Blinken

    Asalin hoton, Reuters

    Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra'ila da Hezbollah na kan matakin ƙarshe,

    Yayin da ya ke magana bayan taron G7, Mista Blinken ya ce: "Wannan wani yunƙuri ne na diflomasiyya mai zurfi da Amurka da kawayenta kamar Faransa suka yi aiki tare da Isra'ila, da Lebanon, kuma ya ɗauki watanni masu yawa. Kuma idan muka kai ga matsayar da na ke fatan za a cimma nan ba da jimawa ba, zai yi babban tasiri" in ji shi.

    Ya ce tasirin da zai yi zai haɗa da ceton rayuka da rayuwa a ƙasar Lebanon, da samar da yanayin komawar ƴan Isra’ilawa gidajensu a arewa su kuma ƴan Lebanon su koma gidajensu a kudanci ƙasar.

    Blinken ya kara da cewa, wannan yunƙurin kawar da tashe-tashen hankula a yankin, na iya taimakawa wajen kawo ƙarshen rikicin a Gaza, domin Hamas za ta san cewa ba za ta iya dogaro da cewa wasu rikice-rikicen za su ɓarke a wasu ɓangarorin ba.

  7. Rasha ta kori jami'in diflomasiyyar Birtaniya bisa zargin leƙen asiri

    ...

    Rahotanni sun bayyana cewa Rasha ta kori wani jami'in diflomasiyyar Burtaniya daga ƙasar bayan ta zarge shi da leƙen asiri.

    Kamfanin dillancin labaran TASS ya ambato mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova tana cewa ma'aikatar ta kuma gayyaci jakadan Birtaniya.

    Hotuna sun nuna lokacin da motar jakadan Birtaniyya ta isa ma'aikatar harkokin wajen ƙasar a birnin Moscow.

    Kakakin ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ya ce: "Wannan ba shi ne karon farko da Rasha ke zarge-zargen da da su da tushe kan ma'aikatanmu ba. Za mu mayar da martani a kan lokaci."

    Kamfanonin dillancin labaran ƙasar sun ruwaito hukumar tsaron ƙasar ta FSB na zargin jami'in diflomasiyyar - wanda aka nuna hotonsa ta kafar talabijin - da bayar da bayanan karya a takardunsa da kuma gudanar da ayyukan leken asiri da zagon ƙasa.

    An ƙara da cewa jami'in diflomasiyyar ya maye gurbin ɗaya daga cikin jami'an diflomasiyyar Burtaniya shida da aka kora a watan Agusta, duk bisa zargin leƙen asirin.

    Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka ke ƙara taɓarɓarewa tsakanin Burtaniya da Rasha tun bayan mamayar da ta yi wa Ukraine a shekarar 2022.

  8. Jami'an tsaro sun fatattaki magoya bayan Imran Khan

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Jami'an tsaro sun fatattaki magoya bayan tsohon Firaministan Pakistan Imran Khan da ke ɗaure a gidan yari, bayan da suka isa tsakiyar babban birnin ƙasar da ke da safiyar ranar Talata.

    Tun a ƙarshen mako ne ayarin masu zanga-zangar suka yi tattaki zuwa dandalin D Chowk na Islamabad suna neman a biya masu wasu buƙatu da suka haɗa da sako Khan.

    Aƙalla mutane shida ne suka mutu – ƴan sanda huɗu, da kuma masu zanga-zanga biyu – yayin da masu tattakin suka ratsa cikin birnin, inda suka yi arangama da jami’an tsaro a wasu wurare.

    Da yawa daga cikin masu zanga-zangar sun sami isa dandalin D Chowk, kuma an gan su suna ta kutsawa kan kwantenonin jigilar kayayyaki da aka ajiye don tare hanya.

    Amma sa'o'i bayan da masu zanga-zangar suka isa dandalin, jami'an tsaro sun yi nasarar tarwatsa su. Yayin da gari ya yi duhu aka kuma kashe fitilu, jami'an ƴansanda da sojojin sa kai ne kaɗai suka rage a wurin.

    Khan, wanda ya shafe sama da shekara guda a gidan yari bisa zargin da ya ce na da alaƙa da siyasa, ya buƙaci magoya bayansa da kada su yi ƙasa a gwiwa - yana karfafa mutane su ci gaba da yin tururuwa zuwa D Chowk.

  9. Rasha ta tabbatar da kama wani ɗan Birtaniya a kan zargin yi wa Ukraine yaƙi

    ...

    Wata kotu a ƙasar Rasha ta tabbatar da kama wani ɗan Burtaniya da ake zargi da yi wa Ukraine yaƙi a yankin Kursk na ƙasar Rasha.

    Wani bidiyon da ya yi yawo a shafukan intanet cikin ƴan kwanakin nan ya nuna wani mutum sanye da kayan soja wanda ya bayyana sunansa a matsayin James Scott Rhys Anderson mai shekaru 22, kuma ya ce ya taɓa aiki a rundunar sojin Burtaniya.

    Wata kotu a Rasha ta ce ta bayar da umarnin a tsare Mista Anderson a gidan yari, bisa zarginsa da hannu a tashin hankali a yankin Kursk.

    A ranar 6 ga watan Agusta ne Ukraine ta ƙaddamar da wani harin ba-zata a yankin na Rasha kuma har yanzu tana riƙe da wani ɓangare na yankin.

    Mista Anderson ya bayyana a gaban kotu ranar Litinin a matsayin ɗan ƙasar Burtaniya daga yankin Banbury, Oxfordshire.

    Masu bincike na Rasha sun zarge shi da aikata ta'addanci da kuma zama sojan haya. Hakan yana nufin cewa maimakon a ɗauke shi a matsayin fursunan yaƙi, zai fuskanci tuhumar aikata manyan laifuka.

    Laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa na ɗauke da hukuncin ɗaurin shekaru 20 da 15 a gidan yari.

  10. Gwmanatin Kano ta rufe ofisoshin kamfanin Ɗantata da jirgin Max saboda zargin rashin biyan haraji

    ...

    Asalin hoton, KIRS/Facebook

    Hukumar tara haraji ta jihar Kano ta rufe babban ofishin jirgin saman Max Air saboda zargin rashin biyan harajin ma'aikatan kamfanin wato PAYE na naira miliyan 190 da sauran na'ukan haraji tsakanin shekarar 2012 zuwa 2017.

    Matakin wani ɓangare ne na yaƙi da marasa biyan haraji a jihar. A cewar ofishin Darakta mai kula da basussuka na KIRS, hukumar ta dauki matakin rufe harabar kamfanin ne bayan da aka yi ƙoƙarin sasanta lamarin ta hanyar tattaunawa.

    "Mun aika wasiƙu da dama zuwa ga Max Air don daidaita bashin harajin su, amma ba mu sami amsa daga garesu ba. A matsayin matakin na ƙarshe, mun samu umarnin kotu na rufe hedikwatarsu kamar yadda doka ta tanada,” in ji ofishin.

    Kamfanin Max Air, mallakin Dahiru Barau Mangal, fitaccen ɗan kasuwa kuma surukin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, shugaban jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) na kasa, ba shi ne kaɗai kamfanin da matakan suka shafa ba.

    Hukumar KIRS ta kuma rufe ofisoshin kamfanin Dantata and Sawoe da ke kan titin Zaria bisa laifin rashin biyan sama da Naira miliyan 241 na harajin PAYE da sauran haraje-haraje daga 2021 zuwa 2022. Haka kuma ta rufe kamfanin Northern Rice and Oil Milling Nigeria Ltd da ke gudumawa.

  11. Mun kama Yahaya Bello - EFCC

    Yahaya Bello

    Asalin hoton, Yahaya Bello/Facebook

    Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzƙin Najeriya ta'annati, EFCC, ta ce ta kama tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a yau Talata.

    Kafin hukumar ta tabbatar da kama shi rahotanni da dama na ambato cewa, tsohon gwamnan wanda ke fuskantar tuhumar almundahana, ya kai kansa ne ofishin hukumar da ke Abuja tare da rakiyar wasu lauyoyinsa.

    A wani hoton bidiyo na tashar talabijin ta Channels, kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da cewa hukumar tana tsare da tsohon gwamnan na Kogi.

    Taƙaddama ta kasance tsakanin EFCC da tsohon gwamnan, bayan da hukumar ta ayyana nemansa a watan Afirilu, bayan ya ƙi amsa gayyatar da ta sha aika masa tare da nuna tirjiya kan duk wani yunƙuri na kama shi, wanda hakan ya sa ya shiga kulli-kurciya da hukumar.

  12. Jiragen saman sojin Jordan sun jefa kayan agaji a Gaza - MDD

    Mutane da ɗaukar kayan agaji

    Asalin hoton, Reuters

    A karon farko cikin wata tara jiragen saman sojojin ƙasar Jordan sun jefa kayan agaji zuwa zirin Gaza.

    Jami'an gwamnatin Jordan sun ce kusan tan bakwai na abinci da wasu muhiman kayayyaki aka jefa a yankunan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa suna matukar buƙatar kayan agaji.

    Gaza na fama da matsalar jinƙai bayan yaƙin watanni goma sha uku tsakanin Israila da mayaƙan Hamas.

    Hukumar agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ke wurin ta ce mutane rabin miliyan na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa sakamakon mamakon ruwan sama.

  13. Za a iya kawo ƙarshen cutar AIDS ko SIDA zuwa 2030 - MDD

    Masu ɗauke da cutar AIDS ko SIDA

    Asalin hoton, OTHERS

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ƙasasahen duniya za su iya kawo ƙarshen cuta mai karya garkuwar jiki, AIDS ko SIDA nan da shekarar 2030 amma ta hanyar kare haƙƙin bil'Adama da kuma yin adalci wajen bada magunguna.

    A rahotonta na shekara-shekara, Majalisar ta ce mutane fiye da miliyan ɗaya da ke ɗauke da ƙwayar cutar HIV a duniya baki ɗaya ba sa samun maganin rage kaifin cutar.

    A wasu sassan Afrika mata matasa masu shekaru fiye da 18 sun fi kamuwa da cutar ninki uku idan aka kwatanta da matasa maza.

    Majalisar ta ce gwamnatoci za su iya daƙile yaɗuwar cutar ta hanyar ɗaukar mataki a kan tsangwamar da ake nuna wa masu fama da cutar, kuma hukumomi su daina watsi da dokokin hukunta masu nuna tsangwama ga masu cutar.

  14. 'Yankasuwar Nijar sun roƙi gwamnati ta sassauta dokar shigar da kaya Benin

    Shugaban mulkin sojin Nijar

    Asalin hoton, OTHERS

    Ƙungiyoyin 'yan kasuwa da na sufuri na Nijar sun buƙaci gwamnati ta sassauta matakan hana shiga da fita da wasu kayayyaki daga ƙasar, kamar yadda gwamnatin Jamhuriyar Benin ta yi.

    Kiran ya biyo bayan wata sanarwa ne da hukumomin Benin suka fitar a ƙarshen mako inda suka bayar da izinin zirga-zirgar jama'a da kayayyaki da dama zuwa Nijar.

    Ana ganin matakin na Benin a matsayin nuna sha'awarta ta samun kwanciyar hankali a tsakanin ƙasashen biyu da ke da sabani ta fuskar diflomasiyya tun daga juyin milkin da sojoji suka yi a Nijar.

    Hukumomion Benin sun sassauta matakin ne duk kuwa da cewa iyakar ta Nijar na ci gaba da zama a rufe.

  15. Shugaban sojin Sudan ya ba Majalisar Ɗinkin Duniya damar kai kayan tallafi ƙasar

    Janar Abdel Fattah al-Burhan

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban rundunar sojin Sudan da ke zaman mai mulkin ƙasar, Abdel Fattah al-Burhan, ya umarci Majalisar Ɗinkin Duniya da ta kafa cibiyoyin samar da kayan agaji tare da amfani da filayen jirgin sama uku wajen samar da kayan taimakon.

    Babban jami'in Majalisar kan ayyukan jinƙai, Tom Fletcher, ya yi maraba da sanarwar bayan tattaunawar da suka yi a Port Sudan.

    Yaƙin da ake yi tsakanin rundunar sojin ƙasar da kuma dakarun RSF, wanda ke ci gaba tsawon sama da shekara ɗaya, ya jefa mutane cikin gagarumar matsala ta rayuwa.

    Ma'aikatan agaji na faman yanda za su tsallaka wasu yankunan da ke hannun ɓangarorin da ke gaba da juna domin kai abinci.

    Mutum miliyan 25 a ƙasar ta Sudan ke buƙatar agajin abinci su rayu kuma an ce da dama na dab da fadawa yanayi na yunwa.

  16. Najeriya na asarar sama da dala biliyan ɗaya kan cutar maleriya duk shekara - Minista

    Mutane a asibiti

    Asalin hoton, OTHERS

    Ministan lafiya na Najeriya Farfesa Muhammad Pate, ya ce arziƙin da ƙasar take asara a shekara sakamakon cutar zazzaɓin cizon sauro (maleriya) ya zarta dala biliyan 1.1.

    Pate ya bayyanna hakan ne kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, yayin ƙaddamar da taron bayar da shawarwari da tuntuɓa kan yaƙi da cutar ta maleriya a Najeria, wanda aka yi a Abuja.

    A wata sanarwa da mataimakin darektan yaɗa labarai na ma'aikatar, Alaba Balogun, ya fitar a yau Talata, ya ce Farfesa Pate ya ce maleriya ba matsala ce ta rashin lafiya ba kaɗai ta zama matsala ga tattalin arziƙi da cigaba wadda ya kamata a ɗauki ƙwararan matakan yaƙi da ita.

    Ya ce, maleriya na ci gaba da gagarumar illa a kan Najeriya, inda take da kashi 27 cikin ɗari na yawan mutanen da ke kamuwa da cutar a duniya, da kuma kashi 31 cikin ɗarin na yawan mutanen da ke mutuwa a duniya a dalilinta .

    Ministan ya ƙara da cewa Najeriya ce ta fi fama da matsalar wannan cuta, inda a 2022, sama da yara 'yan ƙasar 180,000 'yan ƙasa da shekara biyar suka mutu a sanadiyyar cutar - ''wanda wannan abu ne da za mu iya kauce wa.'' In ji ministan.

  17. Hikayata 2024: Gwaraza uku da suka ciri tuta a gasar bana

    Hikayata

    Asalin hoton, BBC Sport

    Hausawa kan ce wai rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya. Bayan kwashe watanni tara ana gwagwagwa dangane da gasar rubutun gajeru kuma ƙagaggun labarai ta mata zalla ta BBC Hausa wato Hikayata, a yau za mu bayyana muku sunayen mata guda uku da labaransu suka ciri tuta.

    Da farko dai BBC Hausa ta samu labarai kimanin 450 da marubuta suka aiko mata inda kuma bayan tankaɗe da rairaiya aka miƙa labarai 400 ga alƙalai na sahun farko waɗanda duka malaman jami'a ne masana harshen Hausa inda suka tantance suka zaɓi guda 30.

    Daga cikin 30 din ne kuma alƙalan na ƙarshe suka zaɓi guda 15, inda 12 suka cancanci yabo sannan kuma uku suka zama zakaru inda a ciki za a bayyana labari na ɗaya da na biyu da kuma na uku. Labarai ukun kuwa su ne:

  18. Matatar Fatakwal ta koma aikin tace man fetur

  19. Abubuwan da yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon ta ƙunsa