Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/10/2024

Wannan shafi en da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/10/2024

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail da Abdullahi Bello Diginza

  1. Dakatar da yaƙi kan Falasɗinawa nauyi a kan duniya - Volker Turk

    Shugaban Ofishin kare haƙƙin ɗan adama na Majalisar Dinkin Duniya ya ce nauyi ne ya rataya kan ƙasashen duniya wajen dakatar da abun da ke faruwa a Gaza.

    Ya ce ana kai munanan hare-hare da kuma azabtar da mutane da yunwa.

    Volker Turk ya ce yaƙin da aka kwashe shekara ana yi ba a taɓa shiga mummunan yanayi irin wanda ake ciki yanzu a Gaza ba.

    An kwashe makonni kayan agaji ba su shiga arewacin Gaza ba.

  2. Rasha ta kai hari a birnin Kyiv

    Magajin garin Kyiv ya ce Rasha ta kai harin jirgi marar matuƙi kan wani dogon gini a babban birnin Ukraine din.

    Vitaliy Klitschko ya ce saman benen ginin na ci da wuta kuma ma'aikatan bada agajin gaggawa na kan hanyarsu ta kai agaji.

    Ya zuwa yanzu ba a samu rahotan mutuwar mutane ba.

  3. Mutumin da ke cin zarafin yara a intanet zai yi zaman gidan kaso na rai da rai

    Wani alƙali a arewacin Ireland ya yanke wa daya daga cikin fitattun da suka fi kowa cin zarafin yara a internet a duniya hukuncin daurin rai da rai.

    Rahotanni sun ce Alexander McCartney ya ci zarafin yara sama da yara dubu uku a ƙasashe talatin na duniya.

    Hukumomi sun ce Alexander na yaudarar yaran ta nuna masu cewa shi ƙaramar yarinya ce domin su tura masa hotunan tsirai cin su.

  4. An yanke wa tsohon kwamandan mayaƙan LRA hukucin shekara 44 a gidan yari

    Kotu a Uganda ta yanke wa tsohon kwamandan mayaƙan ƙungiyar 'yan tawayen LRA hukucin zaman gidan yari na shekara 44, bayan an same shi da aikata laifukan da suka haɗa da kisan kai da azabtarwa da fyaɗe.

    Thomas Koyelo shi ne ɗan ƙungiyar na farko da aka yanke wa hukunci a kotun Uganda.

    Wakiliyar BBC ta ce za a iya yankewa tsohon ɗan tawayen hukuncin kisa ko kuma ɗaurin rai da rai, sai dai al'ƙalan sun ce sun kaucewa hakan ne saboda yana yaro a lokacin da aka shigar da shi ƙungiyar ƴan tawayen.

    Ɗaya daga cikin gagarumin farmakin da ƙungiyar ta kai shi ne wanda ta kaddamar kan fararen hula da ya raba da dama da muhallansu shekaru 20 da suka gabata a arewacin Uganda, inda suka kashe gomman mata da ƙananan yara.

  5. Gwamnatin Kano ta sa dokar hana zirga-zirga ta awa 18 a jihar saboda zaɓe

    Gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar hana zirga-zirga ta awa 18 tun daga ƙarfe 12:00 na daren Juma'a zuwa ƙarfe 6:00 na yammacin ranar Asabar.

    A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar ya fitar, Malam Halilu Ɗantiye, gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da jami'an tsaro na jihar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa dokar hana zirga-zirgar ta shafi ɗaiɗaikuwar jama'a da ababan hawa a ƙananan hukumomin jihar 44.

    Sai dai kuma dokar ta ware mutanen da suke aikin zaɓe da sauran masu ayyukan buƙata na yau da kullum.

  6. Jami'an TCN na aikin gyaran babban layin wutar lantarkin Najeriya

    Jami'an hukumar da ke kula da rarraba wutar lantarki ta Najeriya, TCN na aikin a tashar wutar lantarki da ke yankin Kukwaba da ke Abuja, ɗaya daga cikin wuraren da ke shayar da babban layin wutar kasar wuta.

    Hakn ba zai rasa nasaba da lalacewar da babban layin wutar lantarki na ƙasar ke yi, inda a wannan watan ya lalace kusan sau 10.

    Majalisar dokokin Najeriya dai ta ce ta fara bincike kan dalilan da ke janyo lalacewar babban layin.

  7. Volodymyr Zelensky ya ce Rasha za ta aike da sojojin Koriya ta Arewa ƙasarsa

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce ya samu bayanan sirri cewa Rasha na shirin kai sojojin Koriya ta Arewa filin daga a ranar Lahadi.

    Mista Zelesky ya ce hakan ka iya sanya yaƙin ya ƙara yin muni, inda ya yi kira ga shugabannin ƙasashen duniya da su mayar da kakkausan martani.

    BBC ta gano Ukraine ta yi ƙiyasin cewa aƙalla sojojin Koriya ta arewa 12,000 ne ake bai wa horo a Rasha, tare da tanadar musu kayan aiki.

    Rasha ba ta gaskgata ba ba kuma ta musanta rahotannin da ke cewa tana horar da dubban sojojin Koriya ta arewa ba domin taimaka mata a yaƙin da take da Ukraine.

  8. Hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna yadda hare-haren Isra'ila suka tagayyara Lebanon

    Tsananta luguden wuta da Isra'ila ta yi a Lebanon a mako biyu da suka gataba sun lalata gine-gine sama da waɗanda suka lallata a shekara ɗaya da aka yi ana gwabza yaƙin tsakaninta da Hezbollah, kamar yadda wasu hotuna da aka ɗauka da tauroron ɗan'adam da BBC ta gani suka bayyana.

    Hotunan da BBC ta nazarta sama da 3,600 na gine-ginen ne aka lalata tsakanin 2 zuwa 14 ga Oktoban 2024 - wanda ya nuna kashi 54 na adadin gine-ginen da aka lalata tun bayan da yaƙin ya ɓarke a tsakanin Isra'ila da Hezbollah, kwana ɗaya bayan harin Hamas na 7 ga Oktoban shekarar 2023.

    Hotunan, waɗanda Corey Scher na Jami'ar City da ke Landan da Jamon Van Den Hoek na Jami'ar Jihar Oregun ne suka ɗauka.

    Wim Zwijnenburg, wani masanin harkokin muhalli daga ƙungiyar wanzar da zaman lafiya ta Pax for Peace organisation ya nazarci hotunan, inda ya yi gargaɗin matsalolin da za su biyon tsanantar hare-haren.

  9. Muna gargaɗin gwamnan Kano da ka da ya gudanar da zaɓe - APC

    Shugaban jam'iyyar APC mai adawa a jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya gargaɗi gwamna Abba Kabir Yusuf da ka da ya kuskura ya gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi "kamar yadda wata kotu bayar da umarni."

    A wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar ranar Juma'a a Abuja, Abdullahi Abbas ya ce ya kamata gwamna Kabir Yusuf ya san cewa idan har ya ci gaba da gudanar da zaɓen na to "tamkar ya gayyato rashin zaman lafiya ne a jihar ta Kano."

    "Kawai gwamna ya bi umarnin kotu. A matsayinmu na masu son bin doka da oda da kuma son cigaban jiharmu ta Kano, dole ne gwamna ya guji duk abin da ka iya jefa jihar tamu cikin ruɗani." In ji Abdullahi Abbas.

  10. Al'ummar Thailand na nuna damuwa kan ƙin hukunta waɗanda suka kashe Musulmi

    Mutane sun fusata a Thailand saboda alamu na nuna cewa ba za a hukunta kowa ba kan mutuwar mutane 78 da suka rasu bayan da sojoji suka tsare su.

    A ƙa'ida ya kamata a gama shari'ar ne a cikin shekaru ashirin da aikatan laifin, sai dai yau Juma'a ne wa'adin ya cika.

    Gwamnatin Thailand ta ce ba za ta iya tsawaita lokacin da aka diɓar wa shari'ar ba.

    Lamarin ya faru ne a shekarar 2004 lokacin da sojoji suka cunkusa ɗaruruwan musulmi masu zanga-zanga a bayan manyan motocin yaƙinsu.

    Ofishin kare haƙƙin ɗan adam na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a yi wa iyalan mamatan adalci.

  11. Ba mu shawarci Tinubu ya cire tallafin mai ba

    Asusun Lamuni na Duniya, IMF ya ce shugaba Tinubu gaban kansa ya yi wajen cire tallafin mai amma asusun bai ba shi shawarar yin hakan ba.

    Wannan dai na ɗauke a wata hira da darektar Asusun a nahiyar Afirka, Abebe Selassie ta yi da manema labarai a birnin Washington wadda kuma aka ɗora sahfin X na IMF ɗin.

    "Shawarar cire tallafin mai daga cikin gida ne. Shugaba Tinubu ne ya yi. Ba mu da shirye-shirye a Najeriya. Damar da muke da ita ba ta wuce tattaunawa ba, kamar yadda muke yi da sauran ƙasashe kamar Japan da Burtaniya." Kamar yadda ta ce.

    A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne dai shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin mai jim kaɗan bayan rantsar da shi tun ma kafin ya shiga ofis.

    Masu lura da al'amura dai ba su ɗora laifin cire tallafin mai da Tinubu ya yi a kan IMF ba kasancewar ya yi hakan ne tun kafin ya shiga ofis.

    Sai dai an fi alaƙanta cire tallafin wutar lantarki da Tinubu ya yi da asusun na IMF.

  12. Zaɓen Amurka 2024: Mutum miliyan 32 sun kaɗa ƙuri'arsu a zaɓen farko

    Masu zaɓe fiye da miliyan 32 sun kaɗa ƙuri'arsu a sahun farko na zaɓen na bana kamar yadda ɗakin sa ido kan zaɓe na jami'ar Florida.

    Kimanin mutum miliyan 15 na waɗanda suka yi zaɓen na wuri za ta kaɗa ƙuri'ar a rumfunan zaɓe, inda kuma kimanin miliyan 17 suka yi zaɓen ta hanyar gidan waya.

    Wannan zaɓen na wuri dai na zuwa saura kimanin mako guda a kaɗa ƙuri'ar gamagari abin da ke nufin za a ci gaba da samun ƙaruwa da raguwar alƙaluma ga dukkannin ƴantakarar.

    Ƴan jam'iyyar Democrat sun fi kaɗa ƙuri'ar ta hanyar saƙon gidan waya. To amma a shekarar 2024, ƴan jam'iyyar Republic suna ta ƙaoƙarin ƙwarara wa ƴan jam'iyyarsu gwiwa da su ma su yi zaɓen ta gidan wayar.

    A 2020 ƴan Republican sun soki kaɗa ƙuri'ar ta gidan waya inda suka ce wata hanya ce ta maguɗi. Sai dai bincike da aka gudanar ya nuna cewa da wuya a samu maguɗi ta hanyar idan dai ban da wasu ƴan lokuta da akan iya samun hakan.

  13. Harin Isra'ila ya kashe 'yanjarida uku a Lebanon

    Wani hari ta sama da Isra'ila ta kai kan wani gida - wanda 'yanjarida ke zama a ckinsa a kudu maso gabashin Lebanon - ya kashe 'yanjarida uku, kamar yadda shaidu suka bayyana wa BBC.

    An kai harin ne kan gidan saukar baƙi - wanda gomman 'yan jarida na kafofin yaɗa labarai aƙalla bakwai ke amfani da shi - a Hasbaya da ke kudancin lebanon.

    Harabar gidan cike take da motocin da aka rubutawa alamar na 'yanjarida ne (Press) ƙarara a jikinsu.

    'Yanjaridar uku da aka kashe ma'aikatan gidajen talbijin na Al-Manar TV da Al-Mayadeen TV ne a ƙasar, wadanda tuni suka fitar da saƙon ta'aziyya ga ma'aikatan nasu.

  14. Akwatin aika saƙonni ta Email na Majalisar Dattawan Kenya ya samu tangarɗa

    Akwatin aikewa da sakonni ta Email na Majalisar dattawan Kenya ya samu tangarɗa sakamakon yawan sakonin martanin da al'umma ke aikawa kan ƙudurin da ke cike da ce-ce-ku-ce na tsawaita wa'adin mulkin shugaban ƙasar.

    Majalisar Dattawan na gudanar da taron sauraren ra'ayin jama'a kan yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin ƙasar da zai ƙara wa ƴan siyasar ƙasar wa'adi daga shekara biyar zuwa bakwai.

    Ƙudurin da wani aminin shugaba Ruto ya gabatar ya haifar da hayaniya a majalisar, sai dai duk da haka ya wuce karatun farko.

  15. Zelensky ya ce Rasha na shirin kai sojojin Koriya ta Arewa filin daga

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce ya samu bayanan sirri cewa Rasha na shirin kai sojojin Koriya ta Arewa filin daga a ranar Lahadi.

    Mista Zelesky ya ce hakan ka iya sanyawa yaƙin ya ƙara yin muni, inda ya yi kira ga shugabannin ƙasashen duniya da su mayar da kakkausan martani.

    Ukraine ta yi ƙiyasin cewa aƙalla sojojin Koriya ta arewa 12,000 ne ake ba horo a Rasha, tare da tanadar masu kayan aiki.

    Rasha ba ta amsa ko musanta rahotannin da ke cewa tana horas da dubban sojojin Koriya ta arewa domin taimaka mata a yaƙin da take da Ukraine.

  16. Wane ne kan gaba a ƙuri'ar jin ra'ayin jihohi marasa tabbas?

    Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa Donald Trump na kan gaba a jihohi huɗu cikin bakwai marasa tabbas, yayin da Kamala Harris ke kan gaba a jihohi biyu, suke kuma kankankan a jihar Nevada.

    Ga jadawalin sakamakon ƙuri'ar, kamar yadda ta nuna a kowace jiha.

    • Nevada: Harris: 47.3%, Trump: 47.3%
    • Wisconsin: Harris 47.8%, Trump 47.6%
    • Pennsylvania: Harris: 47.6%, Trump 47.9%
    • Michigan: Harris 47.7%, Trump 47.0%
    • North Carolina: Harris 47.1%, Trump 48.3%
    • Georgia: Harris 47.0%, Trump 48.5%
    • Arizona: Harris 46.8%, Trump 48.6%
  17. Harris da Trump na kankankan a sabuwar ƙuri'ar jin ra'ayi

    'Yan takarar shugabancin Amurka biyu, Kamala Haris ta jam'iyyar Dimokrats da Donald Trump na Repulican na kankankan a sabuwar ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da Jaridar New York Times ta gudanar tare da haɗin gwiwar kwalejin Sienna.

    Ƙuri'ar ta nuna kowane ɗan takara na da kashi 48 na goyon bayan jama'a.

    Ita dai ƙuria'r jin ra'ayin jama'a ra'ayi na kowane ɗan ƙasa, to amma abin da ke tabbatar da cin zaɓen ƙasar shi ne kwamitin masu zaɓe da ake kira 'electoral college', wanda kowace jiha ke da mabambancin adadi na mambobin kwamitin.

    Yayin da ya rage saura kwana 11 a gudanar da zaɓen, a yanzu 'yan takatar biyu sun zafafa yaƙin neman zaɓe musamman a jihohi marasa tabbas, da za su iya sauya sakamakon zaɓe a kowane lokaci

  18. Ba za mu iya canja tarihinmu ba- Sarki Charles lll a taron Commonwealth

    Sarki Charles lll na Birtaniya ya bayyana wa shugabannin ƙasashe rainon Ingila, wato Commonwealth, cewa babu wanda zai iya canja tarihin abubuwan da suka faru a baya.

    Sarkin ya bayyana haka ne a taron Commonwealth na 2024 da ke gudana tsibirin Samoa da ke yankin tekun Pacific.

    Ya ƙara da cewa shugabanni za su samu daraja ta hanyar nazartar abubuwan da suka gabata, "tare da lalubo wasu hanyoyi na fuskantar abubuwan da ke gaba," in ji.

    Wata majiya ta shaida wa BBC wasu shugabannin ƙasashen ƙungiyar sun fara tattauna yiwuwar buƙatar gwamnatin Birtaniya ta biya diyyar cinikayyar bayi saboda rawar da ta taka a harƙallar.

    Sarkin, wanda bai fito fili ya yi magana game da cinikayyar bayin ba, wannan ne karon farko da yake halartar taron na ƙasashen Commonwealth a matsayin shugaban ƙungiyar mai mambobi 56.

    Shi ma firaiministan Birtaniya, Sir Keir Starmer ya ce dole shugabannin ƙasashen ƙungiyar "su fahimci cewa akwai abubuwan da suka haɗa mu masu yawa."

  19. Najeriya ta yi Allah wadai da harin ta'addanci a Turkiyya

    Gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da harin ta'addanci da aka kai kan masana'antar sufurin jiragen saman ƙasar Turkiyya da ke birnin Ankara.

    A ranar Laraba ne wasu mahara biyu suka buɗe wuta a kusa mashigar masan'antar, lamarin da ya yi sanadin kashe mutum biyar tare da jikkata wasu fiye da 20.

    Cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Najeriyar ta fitar, ta ce gwamnatin ƙasar ta kaɗu da harin wanda ta ce barazana ce ga zaman lafiya da kwanciyar hankali.

    Haka kuma sanarwar ta miƙa sakon jaje ga gwamnati da al'ummar Turkiyya, musamman iyalan waɗanda suka mutu a lokacin harin.

  20. Cutar mashaƙo ta kashe mutum 1,191 cikin shekara biyu a Najeriya - NCDC

    Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya, NCDC ta ce kimanin 1,191 ne suka rasu sakamakon kamuwa da cutar mashaƙo daga watan Mayun 2022 zuwa yanzu a sassan ƙasar.

    Hukumar ta kuma cewa mutum 28,000 ne suka kamu da cutar.

    Dokta Muzammil Sani Gadanya, babban jami'in kula da ayyukan daƙile cutar mashakon ne a hukumar ta NCDC, ya ce ana bin matakan da suka dace domin gano waɗanda suka kamu da ita, don kuma yi masu magani.