Dakatar da yaƙi kan Falasɗinawa nauyi a kan duniya - Volker Turk

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Ofishin kare haƙƙin ɗan adama na Majalisar Dinkin Duniya ya ce nauyi ne ya rataya kan ƙasashen duniya wajen dakatar da abun da ke faruwa a Gaza.
Ya ce ana kai munanan hare-hare da kuma azabtar da mutane da yunwa.
Volker Turk ya ce yaƙin da aka kwashe shekara ana yi ba a taɓa shiga mummunan yanayi irin wanda ake ciki yanzu a Gaza ba.
An kwashe makonni kayan agaji ba su shiga arewacin Gaza ba.



















