Haaland na son komawa Madrid, Zirkzee zai iya barin Man U

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Erling Haaland yana sha'awar Real Madrid, Arsenal na sa ido kan Victor Gyokeres, ana sa ran Alexander Isak zai ci gaba da zama a Newcastle.

Dan wasan gaban Manchester City Erling Haaland, mai shekara 24, yana sha'awar komawa Real Madrid idan ya bar kulob dinsa na yanzu, inda kwantiragin dan kasar Norway din zai kare a shekarar 2027. (Mundo Deportivo)

Ana alakanta dan wasan gefe na Liverpool Federico Chiesa da barin kungiyar a matsayin aro yayin da dan wasan mai shekaru 26 ke neman dawo da martabarsa, kuma yana iya komawa AC Milan, da Roma, da Inter Milan. (Calciomercato)

Har yanzu Arsenal da Liverpool na son siyan dan wasan tsakiyar Real Madrid Arda Guler, mai shekara 19, yayin da dan wasan na Turkiyya ke ci gaba da fafutukar ganin ya taka leda a kakar wasa ta bana. (CaughtOffside)

Arsenal na iya shiga cikin fafutukar sayen dan wasan gaba na Sporting da Sweden Victor Gyokeres, mai shekara 26, yayin da kocin kungiyar Mikel Arteta ke kokarin inganta gabansa. (GiveMeSport)

Dan wasan gaban Sweden Alexander Isak, mai shekara 25, yana sha'awar sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya ta dogon lokaci da za ta kai 2028 a Newcastle, duk da sha'awar da Arsenal da Chelsea ke yi ta dauakrsa. (i Sport)

Dan wasan Manchester United Joshua Zirkzee, mai shekara 23, zai iya komawa Seria A aro bayan cin kwallo daya kacal a wasanni 11 da ya buga, kuma ana ganin Juventus ce ta fi dacewa da dan kasar ta Holland. (Tuttosport/TeamTalk)

Besiktas na son daukar dan wasan Everton Dominic Calvert-Lewin, mai shekara 27, aro, yayin da suma Newcastle, da Arsenal da Manchester United ke zawarcin dan wasan na Ingila. (Fotomac)

Kociyoyi biyu yan Ingila, Graham Potter da Gareth Southgate na cikin 'yan takarar da za su maye gurbin kocin Crystal Palace Oliver Glasner idan har kungiyar bata samu wani ci gaba ba a karkashin kocin dan kasar Austria. (TeamTalk)

Arsenal na tunanin zawarcin dan wasan gaban Juventus Dusan Vlahovic, mai shekara 24, wanda a baya ya yi kokarin sayen dan kasar Serbia a shekarar 2022. (Caught Offside)

Daraktocin Barcelona sun gana da wakilin dan wasan tsakiyar Spain Pedri, mai shekara 21, inda suka tattauna batun kwantiraginsa, wanda har yanzu ba a warware shi ba. (Mundo Deportivo)

Middlesbrough ta yanke hukuncin cewa dan wasan tsakiyar Ingila Hayden Hackney mai shekaru 22 zai koma Newcastle United ko Tottenham Hotspur a watan Janairu. (GiveMeSport)