Sarki Charles lll na Birtaniya ya bayyana wa shugabannin ƙasashe rainon Ingila, wato Commonwealth, cewa babu wanda zai iya canja tarihin abubuwan da suka faru a baya.
Sarkin ya bayyana haka ne a taron Commonwealth na 2024 da ke gudana tsibirin Samoa da ke yankin tekun Pacific.
Ya ƙara da cewa shugabanni za su samu daraja ta hanyar nazartar abubuwan da suka gabata, "tare da lalubo wasu hanyoyi na fuskantar abubuwan da ke gaba," in ji.
Wata majiya ta shaida wa BBC wasu shugabannin ƙasashen ƙungiyar sun fara tattauna yiwuwar buƙatar gwamnatin Birtaniya ta biya diyyar cinikayyar bayi saboda rawar da ta taka a harƙallar.
Sarkin, wanda bai fito fili ya yi magana game da cinikayyar bayin ba, wannan ne karon farko da yake halartar taron na ƙasashen Commonwealth a matsayin shugaban ƙungiyar mai mambobi 56.
Shi ma firaiministan Birtaniya, Sir Keir Starmer ya ce dole shugabannin ƙasashen ƙungiyar "su fahimci cewa akwai abubuwan da suka haɗa mu masu yawa."