Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na yau Laraba 5 ga watan Fabrairun 2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Haruna Kakangi da Aisha Aliyu Jaafar

  1. Mata sama da 100 aka yi wa fyaɗe aka kuma ƙona su a Kongo - MDD

    Fursunoni mata sama da 100 ne aka yi wa fyaɗe sannan kuma aka ƙone su da ransu a lokacin da aka fasa kurkukun birnin Goma na Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Kongo, in ji Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Ɗaruruwan fursunoni ne suka fasa gidan yarin Munzenze a ranar Litinin da ta wuce, bayan da mayaƙan ƙungiyar 'yantawaye ta M23 suka fara kama birnin.

    Tsakanin mata fursunoni 165 da 167 ne takwarorinsu maza a gidan sarƙar suka ci zarafinsu a lokacin, kamar yadda wata takarda ta tsakanin jami'an Majalisar, wadda BBC ta gani, ta nuna.

    Rahoton ya nuna cewa yawancin matan an kashe su ne bayan da 'yankason suka cinna wa gidan wuta.

    Sai dai BBC ba ta iya tabbatar da sahihancin rahoton ba.

    Goma, wanda babban birni ne da ke da mutane sama da miliyan ɗaya ya faɗa hannun 'yantawayen ne da Rwanda ke mara wa baya, lokacin da mayƙan suka ƙaddamar da hare-hare daga gabashin ƙasar ta Kongo.

    Birnin ya rikici, inda ake ganin gawarwaki watse a kan tituna kuma harsasai da sauran makamai na ta wucewa ta kan gidan jama'a, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

  2. MDD ta yi wa Donald Trump martani kan karɓe Gaza

    Babban jami'in kare hakkin bil'Adama na Majasar Ɗinkin Duniya ya jaddada cewa korar mutane daga yankin da aka mamaye abu ne da ya saba wa dokokin duniya.

    Volker Turk ya bayyana haka ne bayan da Donald Trump ya ce ya kamata a kwashe Falasɗinawa baki-daya daga zirin Gaza.

    jami'in ya ce ya kamata a mayar da hankali kan mataki na gaba a yarjejeniyar tsagaita wuta domin ganin an sako dukannin mutanen da aka yi garkuwa da su tare da kawo ƙarshen yaƙin.

    Rahotanni sun ce jigan-jigan masu tsattsauran ra'ayi a Isra'ila sun yi kira a mayar da shirin kwashe mazauna Gaza cikin manufofin ƙasar.

    Sai dai shawarar ta Mista Trump kan ƙwace ikon Gaza tare da sake tsugunar da mazaunanta ta janyo kakkausar suka daga Falasɗinawa da kuma gwamnatocin ƙasashen Gabas ta Tsakiya da sauran ƙasashen duniya.

  3. 'Yantawayen M23 sun zafafa hare-hare a Kongo

    Jami'ai a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo sun ce mayaƙan 'yantawaye na ƙungiyar M23, da ke samun goyon bayan Rwanda sun ƙaddamar da sabon farmaki a gabashin ƙasar kwanaki biyu bayan ayyana tsagaita buɗe wuta.

    Sun ce mayaƙan sun ƙwace garin Nya-bib-we inda ake haƙar ma'adanai wanda ke tsakiyar garin Goma wanda kawo yanzu ke ƙarƙshin ikonsu da kuma Bukavu babban birnin yankin.

    Mataimakiyyar shugaban shirin taimaka wa ƙasar ta JD Kongon, Vivian van de Perre ta ce mutanen da aka kashe a garin na Goma, inda ta ce zuwa yanzu an kwashe gawarwaki 2,000 daga kan titunan birnin a kwanakin baya-bayan nan.

    Kuma ta ce akwai gawarwaki 900 a wurin ajiye gawarwaki na asiboticin yankin.

    A hirar da aka yi da Shugaba Paul Kagame na Rwanda a ranar Litinin da ta gabata ya ce ba shi da masaniya a kan ko akwai sojojin kasarsa a Kongo.

  4. Ɗansanda ya harbe kansa a jihar Nasarawa

    Wani ɗansandan Najeriya, kurtu da ke aiki a caji ofis na Mada da ke ƙaramar hukumar Nasarawa Eggon a jihar Nasarawa ya harbe kansa.

    Rahotanni sun nuna cewa an ga ɗansandan, Dogara Akolo-Moses yana gudanar da aikinsa yadda ya saba a ranar da ya kashe kansa, kamar yadda jaridar daily Trust ta ruwaito.

    Wani da ya ga lamarin ya ce ɗansandan ya keɓe kansa ne a wani ɗaki ya harbe kansa da bindigar da kw wajensa.

    Ya ƙara bayanin da cewa ƙarar bindigar ne ya ja hankalin sauran abokan aikinsa da ke caji ofis ɗin a lokacin inda suka garzaya ɗakin suka iske mamacin kwance cikin jini da bindigarsa a gefe.

    Kakakin rundunar 'yansandan jihar ta Nasarawa, Ramhan Nansel, ya ce ana gudanar da bincike kan lamarin, wanda ba a san dalilin da ya sa ya aikata hakan ba.

  5. Kotu ta dakatar da Trump haramta wa haifaffun Amurka shedar zama 'yanƙasa

    Wani alƙalin tarayya a Amurka ya dakatar da aiwatar da umarnin Shugaba Trump na daina bai wa jariran da aka haifa a ƙasar takardar zama 'yan ƙasa ta kai tsaye.

    Wasu mata biyar masu juna biyu ne da ba su da takardar zaman ƙasar suka shigar da ƙarar a jiahr Maryland.

    A ƙarar da suka shigar sun ce umarnin na Trump ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Amurka da kuma dokokin tarayya da dama.

    Lauyoyin ma'aikatar shari'a ta Amurka sun ce damar bai wa waɗanda aka haifa 'yancin zama 'yan ƙasa ta ƙirƙiri jin daɗi da ya wuce hankali da ke ƙarfafa baƙin haure.

    Idan aka aiwatar da uamrnin na Trump, hakan zai hana zama 'yan ƙasa ga 'ya'yan baƙin haure ko kuma waɗanda suka shiga ƙasar ta ƙa'ida amma zaman wucin-gadi.

  6. Argentina ta bi sahun Amurka na ficewa daga hukumar lafiya ta duniya

    Shugaban Argentina, Javier Milei ya sanar da cewa ƙasarsa za ta fice daga hukumar lafiya ta duniya, WHO.

    Mista Milei mai sha'awar salon mulkin Shugaba Donald Trump ne, wanda ya fitar da Amurka daga hukumar ta duniya a watan da ya gabata.

    Kakakin shugaban ƙasar, Manuel Adorni, ya ce Mista Milei bai yarda da manufofin hukumar ba da dama - musamman yadda ta gudanar da aikinta a kan annobar Korona.

    Ya ce Argentina, ba za ta bar wata hukuma ta duniya ta sa mata baki ba a kan abin da ya shafi 'yancin na ƙasa mai cin gashin kanta ba.

    Wakilin BBC a Geneva, hedikwatar hukumar ta, WHO ya ce wannan mataki wani ƙarin koma-baya ne ga hukumar lafiyar - wadda ke aiki a faɗin duniya domin yaƙi da cutar HIV mai karya garkuwar jiki da tarin-fuka da zazzaɓin cizon sauro tare kuma da bayar da taimakon lafiya a wuraren da ake rikici.

  7. Majalisar Dattawan Najeriya ta kori kwamishinonin zaɓen jihohi uku

    Majalisar Dattawan Najeriya ta soke aikin kwamishinonin zaɓe uku bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa buƙatar hakan kamar yadda sashena 157(1) na kundin tsarin mulkin ƙasar na 1999 ya tanada.

    Kwamishinonin uku su ne Dr. Nura Ali na jihar Sokoto da Barrister Hudu Yunusa Ari na jihar Adamawa da kuma Farfesa Ikemefuna Chijioke Uzochukwu na jihar Abia.

    Tun a shekara ta 2023 aka dakatar da su saboda zargin aikata wasu laifuka ciki har da saɓa ƙa'idar zaɓe, da saɓa ƙa'idar dokar zaɓe, da maguɗin zaɓe da kuma ƙaurace wa aiki.

    Rahoton bayanan sirri da ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara, Nuhu Ribadu da kuma hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS, ya nuna cewa an zargi Dr Nura Ali da laifin bayar da kai a kan zaɓen shugaban ƙasa na 2023 da kuma zaɓen majalisun dokoki na tarayya ta hanyar nuna rashin dacewa da cin hanci da rashawa, inda ya amsa cewa ya karɓi dala 150,000 daga 'yansiyasa.

    Shi kuwa Barrister Hudu Yunusa, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne ya dakatar da shi daga aiki bayan da ya saɓa doka ya bayyana sakamakon zaɓen gwamnan jihar Adamawa - aikin da ba nasa ba ne.

    Farfesa Uzochukwu kuwa an same shi ne da laifin rashin alkinta kayan zaɓe da barin zaɓen gwamna da kuma na majalisar jiha, da kuma ƙin sake tsayar da ranar wasu zaɓuka.

    Majalisar bisa tanadin sashe na 157(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya bayar da damar jami'ai bisa kasa gudanar da aiki ko saɓa ƙa'ida, ta cire su daga aikin kwamishinonin zaɓen da rinjayen ƙuri'a kashi biyu bisa uku.

    Da wannan yanzu Shugaba Tinubu zai aiwatar da korar tasu daga matsayin kwamishinonin zaɓe na jihohin uku.

  8. Jirgin yaƙin Amurka ya mayar da Indiyawa kimanin 100 gida

    Jirgin saman sojoji da ke ɗauke da baƙin haure ƴan Indiya fiye da 100 da za a mayar gida daga Amurka ya isa garin Punjab.

    Ana ganin dukkanin mutanen da ke cikin jirgin ko dai sun shiga Amurka ba bisa ƙa'ida ba ko kuma sun cigaba da zama bayan wa'adin da aka diɓar musu na zama ya ƙare.

    Shugaba Trump ya mayar da aikin korar dubban baƙin haure a matsayin wani muhimmin abu kuma zuwa yanzu yanata amfani da jiragen yaƙi domin mayar da su gida.

    Yin amfani da jiragen soji maimako jiragen da akayi shata domin mayar da baƙin haure gida abu ne da ba a saba gani ba kuma abu mai tsada, sai dai ƙwararru na ganin kamar alama ce ta nuna ƙarfin Amurka.

  9. An ci gaba da faɗa a jamhuriyar Congo

    Faɗa ya ci gaba a kudancin yankin Kivu da ke Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo duk da tsagaita buɗe wuta da ƙungiyar ƴan tawayen M23 suka ce sun yi.

    Rahotanni na nuna cewa rikicin ya tsananta ne tsakanin ƴan tawayen M23 da dakarun Kongo a safiyar yau a Nyabibwe, wani kauye da ke yankin Kalehe.

    A ranar Litinin ne ƴan tawayen su ka sanar da tsagaita wuta saboda dalilan jin ƙai, inda suka ce basu da niyyar sake kwace wani yanki kuma bayan kwace garin Goma.

    Jam'ian Kongo sun ce harin yau kan wuraren gwamnati da ƴan tawayen sukayi na nuna keta alƙawarin tsagaita wuta da ƙungiyar ta ɗauka ƙasa da kwanaki biyu da suka wuce.

    Bayan ƙwace garin Goma, ƙungiyar M23 ta so ƙwace Bukavu, babban birnin yankin kudancin Kivu.

    Sai dai rahotannin na cewa sun fuskanci turjiya daga dakarun Congo da Burundi waɗanda suka ƙwato wasu ƙauyuka daga hannun ƴan tawayen a kudancin Kivu.

    Abin da ake sa ido kai a yanzu shi ne ko M23 za su ƙara yunƙurin shiga Bukavu a kwanaki masu zuwa.

  10. Ana sanya ido kan wani dutsen sararin samaniya da ya tunkaro duniya

    Hukumomin sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a sararin samaniya sun ce suna sanya ido kan wani ƙatoton dutse da aka yi hasashen zai iya cin karo da duniya.

    Sai dai Hukumar nazarin sararin samaniya ta yankin Turai (ESA) ta bayyana cewa akwai ƙwaƙƙwarar alamar da ke nuna cewa dutsen zai iya ci gaba da shawaginsa a sararin samaniya ba tare da yin karo da duniyarmu ba.

    Dutsen wanda aka lissafa cewa zai iso kusa da duniya a ranar 22 ga watan Disamban 2032, akwai yiwuwar cewa zai iya faɗowa kan doron duniyar tamu.

    Dakta Robert Massey na ƙungiyar masana ilimin sararin samaniya ta Birtaniya ya ce "ba na tayar da hankalina game da dutsen".

    "Babu buƙatar tayar da hankali," in ji shi. "Abin da ke faruwa shi ne a mafi yawan lokuta daga baya za ka ga dutsen ya sauya hanya."

    Dutsen, wanda aka yi wa laƙabi da YR4, an fara tsinkayar shi ne a ranar 27 ga watan Disamban 2024.

    Masana ilimin sararin samaniya sun ƙiyasta girman dutsen da cewa ya kai tsawon mita 40 zuwa 90.

    Haka nan ana ƙiyasta cewa ƙarfin faɗowarsa kan duniya zai yi daidai da na bam ɗin nukiliya, kuma zai tafka gagarumar ɓarna idan ya faɗa a wuraren da mutane ke zama.

    To sai dai ana kyautata zaton cewa ko da zai faɗo kan doron duniyarmu, to zai faɗa ne a wani daji ko kuma a cikin teku.

    Yanzu haka dai nisan da dutsen ke da shi daga duniya ya sanya babu tabbas kan daidai wurin da dutsen zai iya faɗawa idan ya ci karo da duniyarmu.

  11. Gwamnatin sojin Nijar ta kori ƙungiyar agaji ta Red Cross daga ƙasar

    Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da soke duk wata yarjejeniya tsakanin ƙasar da ƙungiyar bayar da agaji ta Red Cross

    Hukumomin sun kuma rufe ofisoshin ƙungiyar a faɗin ƙasar da kuma korar duk ma'aikatan ƙungiyar da ba ƴan ƙasar ba.

    Duk da dai ba a san dalilin yin hakan ba zuwa yanzu, an jima ana samun rashin jituwa tsakanin ɓangarorin biyu tun watan Nuwamban bara, lokacin da 'hukumomin Nijar suka nuna damuwa kan yadda ake tafiyar da tallafin jin-ƙai da Tarayyar Turai take bai wa ƙungiyoyin masu zaman kansu, ciki har da Red Cross.'

    Hukumomin sojin kasar sun furta cewa kungiyoyin ba su gudanar da ayyukansu a cikin hanyoyin da suka dace kamar yadda dokoki da yarjeniyoyi suka tanada ta hanyoyin hulda ta kasa da kasa.

    Red Cross (Croix Rouge) ta kasance a kasar ta Jamhuriyar Nijar tun shekara ta 1990, inda kuma ta kara kaimi wajen gudanar da ayyukanta a cikin kasar daga shekara ta 2007.

    A lokacin da kungiyar ƴan tawaye ta MNJ ta fara gudanar da ayyukan tayar da kayar baya a cikin kasar ta Jamhuriyar Nijar, kungiyar ta cigaba da taimaka wa alummar da suka tsere daga gidajensu ta hanyar samar masu da ruwan sha da sauran buƙatu.

    A watan Nuwamba hukumomin sojin kasar sun dakatar da kungiyoyi biyu masu zaman kansu ba tare da sanar a hukumance ba hujojin da suka kawo ga hakan.

    Kungiyoyin sun hada da ACTED Agency for Assistance for Cooperation and Development ko kuma Agence da la coperation pour l’assistance au Developpement da kuma APBE.

  12. Tinubu ya ƙara yawan kuɗin kasafin Najeriya na 2025

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nemi a yi ƙari a kasafin kuɗin da ya gabatar na shekarar 2025 daga naira triliyan 49.7 zuwa naira triliyan 54.2.

    Hakan na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da shugaban ya aika wa shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio, wanda ya karanta a zaman majalisar a yau Laraba.

    A cikin wasiƙar, shugaban ya ce buƙatar ƙarin ta taso ne sakamakon samun ƙarin kuɗaɗen shiga na naira triliyan 1.4 daga hukumar tattara haraji ta ƙasar FIRS, da naira triliyan 1.2 daga hukumar hana-fasa-ƙwauri ta kwastam, sai kuma naira triliyan 1.8 daga wasu hukumomin gwamnati.

    Bayan karanto wasiƙar shugaban ƙasar, shugaban majalisar dattawan ya buƙaci kwamitin da ke kula da kasafin kuɗin kan su gaggauta duba batun.

    Ya kuma tabbatar cewa za a kammala dubawa da amincewa da kasafin kudin kafin ƙarshen Fabrairu.

  13. Ɓarayi sun sace ƙwai sama da 100,000 a wani kanti da ke Amurka

    Ɓarayi a jihar Pennsylvania da ke Amurka sun sace ƙwai fiye da 100,000 daga wani kanti, wanda jimillar kuɗinsu ya kai dala 40,000.

    A cewar ƴan sanda, ɓarayin sun samu nasarar yin fashin ƙwayayen ne ta hanyar ɓalle bayan motar kantin sayar da kayan gargajiya na Pete & Gerry's Organics da ke yankin Greencastle a ranar 1 ga watan Fabrairu.

    Hakan na zuwa ne a lokacin da farashin ƙwai ya yi tashin gwauron zabi sakamakon annobar murar tsuntsaye sa ta sanya ƙwan ya yi tsada.

    Farashin ƙwai ya haura da kashi 65 a bara a cewar alkaluman gwamnatin ƙasar, inda suka yi hasashen zai kuma ƙaru da kashi 20 cikin ɗari a 2025.

    Annobar murar tsutsayen ta ɓulla ne a shekarar 2022 kuma tana ta yaɗuwa a sassa daban-daban na ƙasar a ƴan watannin baya, a cewar sashen noma da kiwo.

    Hukumar ta kuma ce farashin ya ƙaru da kashi 8 cikin ɗari a cikin watan Disamba kawai.

    Alkaluma daga sashen sun kuma nuna cewa farashin katan ɗaya na ƙwai ya kai dala 2.51 ne a Disamban 2023 wanda kuma ya haura zuwa dala 4.15 bayan shekara guda.

    Ƙarin farashin ya sa ba a samun shi a wasu shagunan.

    Rahotanni sun nuna ana samun cutar murar tsutsayen a cikin tsuntsaye da shanu a faɗin ƙasar, sai dai ba a fiye samu a mutane ba.

  14. An naɗa Farfesa Ahmed a matsayin shugaban Jami'ar Ahmadu Bello

    Hukumar gudanarwar Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta naɗa Farfesa Adamu Ahmed a matsayin sabon shugaban Jami'ar.

    Shugaban hukumar, Mahmud Yayale Ahmad ne ya sanar da hakan a lokacin da ya ke jagorantar taron hukumar karo na 209 a yau Laraba.

    Kafin naɗin nasa, sabon shugaban Jami'ar Farfesa Adamu, malami ne a sashen karatun tsara birane a jami'ar, kuma zai maye gurbin tsohon shugaban jami'ar Farfesa Kabir Bala.

  15. Ƴansanda na zurfafa bincike kan wanda da ya kashe mutum 10 a Sweden

    Ƴan sanda a Sweden sun ce ba su da wata hujja da ke nuna cewa maharin da ya kashe mutane goma a wata makaranta a birnin Örebro ya yi hakan ne saboda wata aƙida.

    Sun ce suna cigaba da lalubo dalilan da ya sa aka kai harin binɗiga mafi muni a tarihin Sweden kuma sunyi watsi da abin da suka kira 'bayanan ƙarya' da ake ta yaɗawa a kafafen sada zumunta.

    Tun da farko dai sunce ya kai harin ne shi kaɗai.

  16. Tinubu zai sake komawa Faransa a yau Laraba

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa a yau Laraba, a wata ziyara ta ƙashin kai.

    Mai bai wa Tinubu shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga a shafinsa na X, ya ce Tinubu zai tafi Paris ɗin ne gabanin tafiyar da zai yi zuwa Addis Ababa, babban birnin Habasha domin taron ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU).

    A lokacin taron da za a yi a birnin na Addis Ababa a farkon mako mai zuwa, Shugaba Tinubu zai gana da shugabannin ƙasashen Afirka domin taron ƙungiyar da za a gudanar daga ranar 12 zuwa 16 ga watan Fabrairun 2025.

    A yayin ziyararsa a Faransa, Tinubu zai gana da takwaran aikinsa na Faransa Emmanuel Macron.

  17. An tsawaita wa'adin biyan kuɗin aikin hajjin 2025 a Najeriya

    Hukumar aikin hajji ta Najeriya NAHCON ta ƙara wa'adin biyan kuɗin aikin hajjin bana zuwa ranar 10 ga watan Fabrairun 2025.

    A cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktar sashen watsa labarai ta hukumar, Fatima Usara ta fitar, ta ce hukumar ta ɗauki matakin ne sakamakon roƙon da aka yi a madadin maniyyata aikin hajjin da suka kasa biyan ƙudin aikin kafin ƙarewar wa'adin da aka saka da farko na 31 ga watan Janairu.

    Shugaban hukumar ta ƙasa ya buƙaci shugabannin hukumomin aikin hajji na jihohi su tabbatar sun aika kuɗaɗen a kan lokaci, inda ya ce hakan na da muhimmanci ganin cewa Saudiyya ta sanya ranar 14 ga watan Fabrairun 2024 a matsayin ranar ƙarshe na sanya hannu kan kwantiragin da aka yi.

  18. Tankar dakon man fetur ta ƙone a Adamawa

    Rahotanni daga Yola, babban birnin jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa gobara ta tashi a lokacin da wata tankar dakon man fetur ke sauke mai a wani gidan mai da ke birnin, sai dai lamarin bai kai ga asarar rai ba.

    Gobarar ta faru ne a kan titin Numan kusa da filin jirgin sama na jihar Adamawa.

    Zuwa yanzu ba a gano musabbabin gobarar ba sai dai lamarin ya janyo fargaba da ya kai ga dandazon mutane sun toshe hanyar shiga birnin.

    An kuma tura jam'ian tsaro wurin domin kare mutane da kuma hana su zuwa ɗibar man.

    Wannan ibtila'i na gobara ko faɗuwar tankar mai na cigaba da zama babbar matsala a Najeriya inda ko a ranar 18 ga watan Janairun wannan shekarar, aƙalla mutane 86 suka mutu yayin da wasu 55 suka jikkata a lokacin da suke ɗibar mai bayan fauwar wata tankar mai.

    Ko a bara ma an samu haɗurran tankar dakon man fetur da ya yi sanadiyyar mutuwar ɗaruruwan mutane da kuma asarar dukiya.

  19. Amurka ta tasa ƙeyar Indiyawa kusan 100 zuwa gida

    Aƙalla mutanen Indiya kimanin 100 da ake zargin sun shiga Amurka ta ɓarauniyar hanya ne ake sa ran za su isa jihar Punjab a yau.

    Wani jirgin saman sojojin Amurka da ke ɗauke da mutanen ya bar birnin Texas a daren ranar jiya Talata.

    Jami'ai a birnin Amritsar sun bayyana cewa a shirye su ke na karɓar mutanen.

    Donald Trump ya sanya aikin korar dubban baƙin haure da ke zama a Amurka ba bisa ƙa'ida ba cikin muhimman tsare tsarensa.

    Ya ce Firaministan Indiya Narendra Modi ya tabbatar masa cewa ƙasarsa za ta yi 'abin da ya dace' wajen ƙarbar waɗanda za a dawo da su.

  20. Saudiyya ta yi watsi da shirin fitar da Falsɗinawa daga Gaza

    Ƙasar Saudiyya ta yi watsi da duk wani yunƙuri na kwashe Falsɗinawa daga yankinsu kamar yadda shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana.

    Saudiyya ta ce ba za ta ƙulla duk wata alaƙa ta diflomasiyya da Isra'ila ba tare da an bai wa Falsɗinawa ƙasarsu mai ƴanci ba.

    Wani mai magana da yawun ƙungiyar Hamas ya bayyana shawarar ta Donald Trump a matsayin abin takaici, wadda za ta haifar da ƙarin zaman tankiya a yankin.

    Haka nan an samu wasu daga cikin sanatocin Amurka na jam'iyyar Democrats waɗanda suka soki batun, inda ɗaya daga cikinsu ya bayyana lamarin a matsayin "yunƙurin kawar da wata ƙabila daga doron ƙasa."

    Tuni Masar da Jordan suka yi watsi da batun tayin karɓar Falsɗinawan.