Mata sama da 100 aka yi wa fyaɗe aka kuma ƙona su a Kongo - MDD

Fursunoni mata sama da 100 ne aka yi wa fyaɗe sannan kuma aka ƙone su da ransu a lokacin da aka fasa kurkukun birnin Goma na Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Kongo, in ji Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ɗaruruwan fursunoni ne suka fasa gidan yarin Munzenze a ranar Litinin da ta wuce, bayan da mayaƙan ƙungiyar 'yantawaye ta M23 suka fara kama birnin.
Tsakanin mata fursunoni 165 da 167 ne takwarorinsu maza a gidan sarƙar suka ci zarafinsu a lokacin, kamar yadda wata takarda ta tsakanin jami'an Majalisar, wadda BBC ta gani, ta nuna.
Rahoton ya nuna cewa yawancin matan an kashe su ne bayan da 'yankason suka cinna wa gidan wuta.
Sai dai BBC ba ta iya tabbatar da sahihancin rahoton ba.
Goma, wanda babban birni ne da ke da mutane sama da miliyan ɗaya ya faɗa hannun 'yantawayen ne da Rwanda ke mara wa baya, lokacin da mayƙan suka ƙaddamar da hare-hare daga gabashin ƙasar ta Kongo.
Birnin ya rikici, inda ake ganin gawarwaki watse a kan tituna kuma harsasai da sauran makamai na ta wucewa ta kan gidan jama'a, kamar yadda rahotanni suka bayyana.



















