Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na yau Laraba 5 ga watan Fabrairun 2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Haruna Kakangi da Aisha Aliyu Jaafar

  1. A shirye nake na tattauna da shugaban Rasha - Zelensky

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce duk wata tattaunawa da za a yi kan makomar ƙasarsa, wajibi ne a sanya ƙasashen yamma da Amurka da Rasha da kuma Ukraine din a ciki.

    A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, Volodymyr Zelensky ya ce a shirye yake ya tattauna kai tsaye da shugaba Vladimir Putin, idan har hakan ne zai kawo ƙarshen yaƙin da suka kwashe kusan shekara uku suna gwabzawa.

    Sai dai shugaba Zelensky ya sake nanata buƙatarsa ta ƙarin makamai domin ci gaba da samun nasara kan Rashar.

  2. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu a wannan shafin da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, muna muku maraba a wannan safiya ta Laraba 5 ga watan Fabarairun 2025.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu da sada zumunta: facebook, X, Instagram, WhatsApp da YouTube domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa da kuma kallon hotuna da bidiyo.