Asuba ta gari
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya a sauran sassan duniya. 21/10/2024
Umar Mikail, Muhammad Annur, Isiyaku Muhammed, Usman Minjibir da Ahmad Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a arewacin Gaza, mazauna yankin na ci gaba da bayyana abunda ke faruwa a Jabaliya.
Ma'aikatan lafiya na asibitin Indonesiya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa dakarun Isra'ila sun yi wa wata makaranta da ake amfani da ita a wajen tsugunar da ƴan gudun hijira ƙawanya, inda suka tsare mutane tare da cinna wa wajen wuta.
Gobarar da suka haddasa ta lalata cibiyar samar da wuta ta asibitin.
Sai dai Isra'ila ta ce tana yin haka ne domin dakatar da Hamas daga sake dunƙulewa a arewacin Gaza.
A wani labarin, sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken zai sake komawa Gabas ta tsakiya domin sake duba yiyuwar tsagaita wuta a Gazar.
Dakarun tsaron Isra'ila sun yi iƙirarin kashe shugaban sashen kuɗi na ƙungiyar Hezbollah a wani hari a Damascus, babban birnin Syria.
Tun da farko, ma'aikatar tsaro ta ƙasar Syria ta fitar da wata sanarwar cewa an kashe fararen hula biyu tare da jikata wasu mutum uku a harin da Isra'ilar ta kai.
"Za mu ci gaba da farmaki kan Hezbollah a Syria da kuma ko'ina," in ji sanarwar dakarun Isra'ila a yammacin nan.
Ƴan tawayen M23 sun ƙwace iko da wani gari a gabashin jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo bayan artabu da sojojin Kamaru da ƙawayensu.
Mazauna yankin arewacin lardin Kivu sun ce rikicin da aka yi a Kalembe ya jikkata gomman fararen hula.
Jami'an yankin sun ce wasu da dama sun tsere zuwa garuruwan makwabta.
Sai dai sojojin Kongon ba su ce komai ba kan haka.
A tsawon makonni kafin Isra'ila ta kaddamar da farmakin soji kan Hezbollah, jakadan Amurka a Lebanon, Amos Hochstein ya yi ƙoƙarin dakatar da hakan, amma bai yi nasara ba.
A yanzu, ya koma zuwa Lebanon, domin ganin ko za a samu zaman lafiya bayan kusan makonni hudu da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare.
Ya ce dole ne abin da ke faruwa a yanzu ya sauya, bayan ganawa da kakakin majalisar dokokin Lebanon.
A daren jiya ne Isra'ila ta jefa bam kan wnai bankin Hezbollah a Beiru, inda ta ce tana son daƙile hanyoyin da ƙungiyar ke samun kuɗi.
Hezbollah na a kowane ɓangare na rayuwa a Lebanon, inda take bayar da taimakon kuɗi a wajen da gwamnatin Lebanon ba za ta iya ba.
Isra'ila na son Hezbollah ta tsame hannunta kacokan kan harkokin rayuwa a Lebanon.
zuwa yanzu dai, babu ɓnangaren da ya shirya dakatar da faɗa.
Shugaban Kamaru Paul Biya ya koma ƙasarsa, bayan shafe tsawon lokaci ana yaɗa jita-jita kan lafiyarsa abin da ya kai ga ana zargin cewa ya mutu.
Shugaba Biya mai shekara 91 da yanzu haka ya kusan shafe shekaru 42 kan karagar mulki, ya ɗaga hankalin 'yan ƙasar bayan daina jin ɗuriyarsa tun bayan taron ƙasahen China da Afirka da aka gudanar a watan da ya gabata a Beijing.
Mahukunta Kamaru sun dage kan cewa Mista Biya na cikin ƙoshin lafiya sannan yana hutu ne a gidansa da ke Geneva ta kasar Switzerland.
Cuncurundon mutane cikin farin ciki da annashuwa da suka haɗar da jami’an gwamnati da kuma magoya bayan shugaba Paul Biya ne suka tarbe shi a babban birnin ƙasar Younde.
Mutane sun taru a kan titunan babban birnin kasar inda aka riƙa shewa da kaɗe-kaɗe don nuna jin daɗi a kan dawowar shugaban kasar gida.
A wannan karon, ministan harkokin cikin gidan ƙasar ya hana kafafan yaɗa labarai cewa komai a kan lafiyar shugaban ƙasar.
Dawowar ta Paul Biya ta kawo ƙarshen jita-jitar da ake yaɗawa cewa ya mutu, to amma ba a ce komai a game da jimawar da aka yi ba a ji ɗuriyarsa ba.
Jami'an hukumar shige da fice ta Najeriya sun ce sun kama Idris Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky.
Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta kama Bobriksy ne a lokacin da yake ƙoƙarin tserewa daga Najeriya a iyakar Seme.
"Muna son mu sanar da al'umma cewa mun kama Idris saboda abubuwa da suka faru a baya-bayan nan. Yana ci gaba da amsa tambayoyi kuma za mu miƙa shi ga hukumomin da suka kamata domin ɗaukar mataki," in ji hukumar.
Hukumar ta ƙara da cewa za ta ci gaba da aiki tukuru wajen tsare kan iyakokin Najeriya yadda ya kamata.
Bayan tantancewa, alƙalan gasar Hikayata sun zaɓi labarai guda 30 da suka ce su ne suka yi fice a gasar Hikayata ta bana.
Da farko dai BBC Hausa ta samu labarai kimanin 450 da marubuta suka aiko mata inda kuma bayan tankaɗe da rairaiya aka miƙa labarai 400 ga alƙalai na sahun farko waɗanda duka malaman jami'a ne masana harshen Hausa inda suka tantance suka zaɓi guda 30 kamar haka.
Nan gaba kaɗan kuma alƙalai za su zaɓi labarai 15, inda a ciki za a samu na ɗaya da na biyu da na uku da kuma guda 12 da suka cancanci yabo.
A watan Nuwamban 2024 ne dai za a yi bikin karrama gwarazan gasar na bana a birnin Abujar Najeriya, inda waɗanda suka zo na ɗaya da na biyu da na uku za su karɓi kyautukan kuɗi da lambar yabo da kuma shaidar samun nasara.
Babban attoni janar na ƙasa kuma ministan shari`a Lateef Fagbemi ya ce gwamnatin Najeriya ta fara aiwatar da ƙarin kashi 300 na albashin ma'aikatan shari'a.
Fagbemi ya bayyana haka ne ranar a bikin kammala karatu na jami'ar Afe Babalola a jihar Ekiti yau Litinin.
"Abin damuwa ɗaya kafin na zo kan muƙamina shi ne rashin kyawun albashin ma'aikatan shari'a," in ji ministan na shari'a.
Ya ce abin farin ciki shi ne yanzu gwamnatin Najeriya karkashin shugaba Tinubu ta fara aiwatar da ƙarin albashi da ta yi wa jami'an shari'a.
Ministan ya kwatanta matakin a matsayin wani ɓangare na farko na karfafa tsarin shari'ar Najeriya.
A watan Agustan ne shugaba Tinubu ya rattaɓa hannu kan ƙarin albashi kashi 300 ga ma'aikatan shari'a.
Babban attoni janar ɗin ya kuma ce gwamnatin Najeriya za ta sabunta ko yin garanbawul ga dokokin Najeriya domin su tafi daidai da buƙatun yau da kullum a faɗin ƙasar.
Sama da mutum miliyan ɗaya ne ambaliyar ruwa ta shafa a Sudan ta kudu, kamar yadda kwamitin ayyukan jin-ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya, Ocha ya bayyana.
Kusan rubu'in mutanen da ambaliyar ta shafa, ta raba su da muhallansu, inda yanzu suke zaune a sansanonin wucin gadi.
Ocha ya ce mamakon ruwan sama da ake tafkawa ya janyo wahala wajen kai kayan agaji ga waɗanda ke buƙata.
Wannan dai shi ne ambaliya mafi muni da Sudan ta Kudu ta fuskanta cikin gomman shekaru - ƙasar da ke da al'umma sama da miliyan 11
Ambaliyar ta shafi mutum 112,000 a lardin Pibor da ke gabashin ƙasar, inda mutane suka rasa gidajensu, a cewar ma'aikatar agaji ta gwamnati a can.
Ga waɗanda suka tsere zuwa yankuna marasa haɗari na fama da matsalar abinci saboda sun bar komai a gidajensu, a cewar darektan ƙungiyar agaji a lardin Pibor, Joseph Nyao.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta buƙaci mutanen da ke zaune a yankunan da ambaliya za ta shafa da su tashi nan take domin kare kansu.
"Yawan ruwa na ƙaruwa kuma lamarin na ci gaba da ɗaiɗaita mutane," in ji Nyao.
An bude taron kungiyar ƙasashen rainon Ingila wato Commonwealth na wannan shekarar a yau a tsibirin Samoa da ke a tekun Pacific.
Sarki Charles na Ingila ne ke jagorantar shugabannin ƙasashen ƙungiyar su 56 a taron na kwanaki 6.
Taron dai zai mayar da hankali ne kan yadda ƙasashen ƙungiya za su yi amfani baiwar da suke wajen ƙara samun cigaba da kuma ƙara dunƙulewa ta amfani da fasahar zamani.
Ɗaruruwan masu zanga-zanga sun yi arangama da ƴansanda a babban birnin Mozambique, Maputo a wurin da aka bindige wasu makusantan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyar Hamayya.
Rahotanni sun ce ƴansanda sun far wa shugaban jam'iyar Podemos, Ve-nan-ci-yo Mond-lane a lokacin da yake tattaunawa da ƴan jarida.
Mista Mondlane ya yi ta ƙalubalantar sakamakon zaɓe na farko-farko na zaɓen da aka gudanar a farkon wannan watan.
An kashe lauyan mista Mondlane da kuma wani jami'in jam'iyar a ranar Juma'a lokacin da wasu ƴan bindiga suka kai wa motarsu hari.
Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Moussa Faki Mahamat ya yi allawadai da kashe-kashen tare da yin kira ga mahukunta a Mozambique da su gurfanar da wadanda suka aikata ta'asar.
BBC ta ga wata sanarwa daga ofishin ministan shari'ar Isra'ila wadda ta ta fayyace yadda za a hukumta wasu ƴan Isra'ila guda bakwai waɗanda suka fito daga Haifa da arewacin Isra'ilar da ake zargi da "yi wa ƙasar Iran aiki a lokacin yaƙin da ake yi da kafinsa."
Sanarwar dai ta bayyana yadda aka biya mutanen "ɗaruruwan dubban dalolin Amurka ta hanyar kuɗin kirifto".
Sanarwar ta ci gaba da cewa mutanen "sun ƙaddamar da ɗaruruwan ayyuka" inda suka ɗauki hotuna da kuma haɗa bayanan sirri da ya haɗa da kayan aikin rundunar IDF da wuraren da baturan tsarin tsaron Isra'ilar mai sulke suke.
Ana sa ran nan da wasu ƴan kwanaki ne za a fayyace laifukan da ake tuhumar mutanen.
Ofishin ya bayyana wannan al'amari da "ɗaya daga cikin manyan laifuka" a ƴan shekarun nan.
Wani jami'in Hamas ya gaya wa BBC cewa wataƙila ƙungiyar ta riƙa ɓoye sunayen sababbin shugabanninta saboda dalilai na tsaro.
A shekara ta 2003 ma ƙungiyar ta yi hakan bayan kisan gillar da Isra'ila ta yi wa tsohon shugabanta Sheikh Ahmed Yassin da kuma wanda ya gaje shi, Dr Abdel Aziz al-Rantisi.
Ƙungiyar ta tsara zaɓen sabon shugabanta a watan Maris na shekara mai zuwa, to amma kafin sannan wani kwamitin mutum biyar ne zai riƙa gudanar da ita.
Kwamitin zai ƙunshi Khalil al-Hayya, da Khaled Meshaal, da Zaher Jabarin, da Muhammad Darwish, shugaban majalisar magabata - Shura - da kuma mutum na biyar wanda ba a bayyana shi ba.
Jami'in ya nuna cewa Khalil al-Hayya shi ya karɓi yawancin ɗawainiyar siyasa da harkokin waje, ƙari a kan gudanar da harkokin Gaza.
Saboda wannan ɗawainiya da yake ggudanarwa kusan a yanzu shi ne ke aiki kamar shugaban ƙungiyar.
Yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a arewacin Gaza, mazauna yankin na ci gaba da bayyana abin da ke faruwa a Jabaliya.
Ma'aikatan lafiya na asibitin Indonisiya sun shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa dakarun Isra'ila sun yi wa wata makaranta da ake amfani da ita a wajen tsugunnar da ƴan gudun hijira ƙawanya, inda suka tsare mutane tare da cinna wa wajen wuta.
Gobarar da suka haddasa ta lalata cibiyar samar da wuta ta asibitin.
Sai dai Isra'ila ta ce tana yin haka ne domin dakatar da Hamas daga sake dunƙulewa a arewacin Gaza.
A wani labarin, sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken zai sake komawa Gabas ta tsakiya domin sake duba yiyuwar tsagaita wuta a Gazar.
Wakili na musamman da Shugaba Biden na Amurka ya aika zuwa Lebanon ya ce suna aiki tare da dukkan ɓangarori domin ganin an kawo ƙarshen rikicin Isra'ila da Hezbollah.
Amos Hochstein ya ce suna ƙoƙarin ganin sun ba kowane ɓangare damar buɗe sabon shafi na zaman lafiya mai ɗorewa.
Wakilin na magana ne a lokacin da yake tattaunawa da babban jagoran Shi'a a Beirut, Nabih Berri wanda shi ne wakilin Hezbollah.
Sai dai kuma Isra'ila na ci gaba da kai munanan hare-hare a Lebanon duk da ziyarar ta Amos.
Mai magana da yawun gwamnatin Isra'ila David Mensa ya ce cikin daren jiya, sun kai hare-hare kan sansanonin Hezbollah da kuma wuraren da ƙungiyar ke ajiye kudadensu.
Sannan ya ce sun fitar da bayanan yadda Iran ke aika wa ƙungiyar dala miliyan hamsin kowane wata.
Ƴan Maldova sun goyi bayan sauya kundin tsarin mulkin ƙasar wanda zai ba ta damar shiga ƙungiyar Tarayyar Turai, EU. Sai dai sun samu nasarar ne ba tare da wani gagarumin rinjaye ba, ƙasa da yanda aka yi hasashe.
Shugabar ƙasar, Maya Sandu mai goyon bayan Tarayyar Turai, ta ce sun samu nasarar da za ta tabbabar da makomar ƙasar nan gaba.
Ta ce burinsu na siyan ƙuri’u 300,000 tare da biyan mutane 150,000 don kada ƙuri’a ya nuna cewa dole ne su gano inda aka yi kura-kurai domin su ɗauki darasi.
Hukumomin ƙasar ta Moldova sun zargi ƙasar Rasha da sayen ƙuri'u domin kawo cikas ga shirin shiga ƙungiyar ta Tarayyar Turai.
Hedikwatar tsaron Najeriya ta gargaɗi ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi da ke kira ga sojoji su yi juyin mulki a ƙasar, tare da jaddada cewa yin hakan cin amanar ƙasa ne a ƙarƙashin kundin tsarin mulki.
Hukumomin sojin sun kuma ƙara jaddada biyayyarsu ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da ƙudurinsu na kare tsarin dumukuraɗiyya a ƙasar.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da darektan yada labarai na hedikwatar tsaron, Birigediya Janar Tukur Gusau ya fitar, inda ya ce sojojin za su ci gaba da mayar da hankali a kan babban aikin da ya wajaba a kansu, wanda ya haɗa da kare yankin ƙasar tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
Darektan ya ƙara da cewa ya kamata masu neman sojoji su yi juyin mulki, kamar yadda aka gani a wani hoton bidiyo da ake ta yaɗawa, su sani cewa wannan abu cin amanar ƙasa ne a bisa tanadin kundin tsarin mulki.
Janar Gusau, ya kuma ce zaman lafiyar da aka samu a ƙasar a yanzu, ya samu ne sakamakon goyon bayan da shugaban ƙasar ke ba wa sojoji da kuma jajircewar shugabancin sojojin.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa sojojin tare da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaro za su ɗauki dukkanin matakan da suka dace wajen hana duk wani yunƙuri na sauyin da ta hanyar kundin tsarin mulki ba.
Hedikwatar tsaron ta Najeriya ta fitar da wannan sanarwa ne, bayan da aka riƙa yaɗa wani hoton bidiyo a kwakin nan inda wasu ke kira ga sojoji su yi juyin mulki a Najeriyar.
Shugaban Zambia Hakainde Hichilema ya kori manyan alƙalai uku waɗanda ya dakatar a baya, bisa zargin saɓa dokokin shari'a, abin da ya ƙara janyo masa zargin tsoma baki a ɓangaren shari'a.
Alƙalan uku sun jagoranci shari'ar zaɓen shugaban ƙasa ne a 2016, inda a lokacin suka yi watsi da ƙarar da Hichilema ya shigar kan ƙalubalantar nasarar da tsohon shugaban ƙasar Edgar Lungu ya samu.
Haka kuma suna daga cikin waɗanda suka zartar da hukuncin da ya janyo taƙaddama wanda ya bai wa Mista Lungu damar sake tsayawa takara a zaɓen 2021, duk da cewa ya yi wa'adi biyu da tsarin mulkin ƙasar ya amince.
Korara tasu ta tabbata ne bayan da suka yi rashin nasara a ƙarar da suka ɗaukaka kan shawarar da wani kwamitin shari'a ya zartar inda ya bayar da shawarar korarsu daga aiki.
A jiya Lahadi ne fadar shugaban ƙasar ta fitar da sanarwar korarsu, kamar yadda kwamitin binciken ya bayar da shawara.
Alƙalan uku - Justice Annie Sitali, da Justice Mungeni Mulenga, da Justice Palan Mulonda – ba su ce komai ba game da korar.
Kwamitin hukumar kula da harkokin shari'a na ƙasar ya gudanar da bincike a kansu ne bayan da wani ɗan kasar ta Zambia Moses Kalonde ya shigar da ƙorafi a kansu.
Ana bayyana ra'ayoyi daban-daban a kan korar alƙalan.
Haka kuma ana samun ƙaruwar zaman ɗar-ɗar a ƙasar ta Zambia yayin da take fuskantar zaɓen 2026, a lokacin da ake sa ran Hichilema da Lungu za su sake fafatawa a karo na huɗu.
Ƙarƙashin kundin tsarin mulkin Zambia, shugaban ƙasa ne ke naɗa dukkanin alƙalai ciki har da alƙalin alƙalai bisa shawarar hukumar kula da harkokin shari'a da kuma amincewar majalisar dokoki ta ƙasar.
Mutumin da ya fi kowa kuɗi a duniya Elon Musk ya ce zai riƙa bayar da kyautar dala miliyan ɗaya a duk rana daga yanzu har zuwa ranar zaɓe - 5 ga watan Nuwamba, ga mai zaɓe ɗaya, a muhimman jihohin da za su tabbatar da wanda zai ci zaɓen Amurka.
Za a zaɓi wanda ya yi nasarar cin kuɗin ne daga waɗanda suka sanya hannu na goyon baya ga wata takarda kan kundin tsarin mulkin Amurka, wadda Elon Musk ke jagoranta mai laƙabin AmericaPAC, wadda ke goyon bayan Donlad Trump na jam'iyyar Republican, a fafutukarsa ta sake komawa kujerar mulkin ƙasar.
A ranar Asabar da daddare ne aka bai wa mutum na farko da ya ci kuɗin a Pennsylvania, sannan a ranar Lahadi ma aka bai wa wani.
Gwamnan jihar Pennsylvania Josh Shapiro, ɗan Democrat wanda ke goyon bayan mataimakiyar shugaban ƙasa, kuma ƴar takarar jam'iyyar ta Democrat, Kamala Harris, ya kira tsarin na Mr Musk abin damuwa sosai.
A tattaunawarsa da kafar yaɗa labarai ta NBC Shapiro ya ce kamata ya yi jami'an tsaro su duba wannan lamari ya bayar da kuɗin ga masu zaɓe.
Gasar ta tsaya ne ga masu zaɓe a jihohin Pennsylvania, da Georgia, da Nevada, da Arizona, da Michigan, da Wisconsin da kuma North Carolina, waɗanda dukkaninsu jihohi ne da za su raba gardama a zaɓen shugaban Amurkar.
Ƙwararre a kan dokokin zaɓe, kuma malami a jami'ar California, Los Angeles (UCLA), Rick Hasen, ya rubuta a shafinsa na intanet cewa yana ganin abin da Mr Musk ke yi haramun ne ƙarara.
Dokokin tarayya na Amurka sun ayyana cewa duk wanda ya biya kuɗi ko ya yi tayin bayar da kuɗi domin wani ya yi rijista ya yi zaɓe ko kuma don mutum ya yi zaɓe, mutumin na fuskantar haɗarin hukuncin tarar dala dubu 10 ko hukuncin ɗaurin shekara biyar.