Everton na zawarcin Chukwueze, Manchester United na ƙoƙarin shawo kan Davies

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Everton na shirin na nazarin miƙa ta kan ɗan wasan AC Milan da Najeriya Samuel Chukwueze, mai shekara 25, a kasuwar musayar ƴan wasa ta watan Janairu. (Football Insider)

Manchester United na kokarin shawo kan ɗan wasan baya na Bayern Munich Alphonso Davies, mai shekara 23, domin ya yi watsi Real Madrid ya koma Old trafford idan kwantiragin ɗan wasan na Canada ya ƙare a ƙarshen kakar wasa ta bana. (Fichajes)

Arsenal za ta iya sayan Dusan Vlahovic ɗan ƙasar Serbia mai shekara 24 a kan farashi mai rahusa yayin da aka samu tazgaro a tattaunawar da ɗan wasan ke yi da Juventus kan sabunta kwantiraginsa. (Caught Offside)

Aston Villa ta shiga takarar neman ɗan wasan gaban Kamaru Bryan Mbeumo, mai shekara 25, daga Brentford. (TBR Kwallon kafa)

Manchester United za ta iya bai wa Juventus aron ɗan wasan gaban Netherlands Joshua Zirkzee, mai shekara 23, idan har ta sayi ɗan wasan gaban RB Leipzig ɗan ƙasar Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 21, a bazara mai zuwa. (Tuttomercato)

Manchester City da Liverpool da Tottenham sun sanya ido kan ɗan wasan Real Valladolid ɗan ƙasar Sifaniya Raul Moro, mai shekara 21. (Fichajes)

Arsenal da Juventus da AC Milan da Napoli na cikin kungiyoyin da ke sha'awar ɗan wasan Como da Argentina Nico Paz mai shekaru 20. (Nicolo Schira)

Arsenal da Tottenham da Crystal Palace da kuma Nottingham Forest - na zawarcin ɗan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jamie Bynoe-Gittens, mai shekara 20 - duk da cewa ƙungiyar ta ƙasar Jamus ba ta shirya karɓar tayin ƙasa da fam miliyan 50 kan ɗan wasan ba.

Kociyan Ingila mai jiran gado Thomas Tuchel ya raba gari da abokin aikinsa Zsolt Low kafin karɓar aikin horas da tawagar ta Ingila. (Sun)