Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 21/10/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya a sauran sassan duniya. 21/10/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, Muhammad Annur, Isiyaku Muhammed, Usman Minjibir da Ahmad Bawage

  1. Togo da Benin na samun wutar sa'a 24 daga Najeriya – TCN

    Manajan darakta kuma babban jami'in gudanarwa na Hukumar Rarraba wutar lantarkin Najeriya TCN, Sule Abdulaziz ya ce ƙasashen Togo da Benin suna samun wutar lantarki ta sa'a 24 daga Najeriya.

    "Muna ba Togo da Benin da Nijar lantarki. Suna samun wutar awa 24, kuma suna biya," in ji Abdulaziz a tattaunawarsa da tashar talabijin ta Channels a ranar Lahadi.

    Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ƴan Najeriya da dama ba sa samun wutar kamar haka, sai ya ce, "Yan Najeriya na samun wuta sosai amma ba a ko'ina ba. Waɗanda suke Band A suna samun lantarki na tsakanin awa 20 zuwa 22 a rana," in ji shi.

    Abdulaziz ya ƙara da cewa, "ina tabbatar muku za mu iya fara samun isasshiyar wutar lantarki nan da shekara biyar. Sabon ministan yana ƙoƙari domin tabbatar da hakan."

    Ya ƙara da cewa akwai bambanci tsakanin TCN da Nepa, "lokacin da muke Nepa, mu ne muke samar da wutar, mu rarraba, sannan mu yi kasuwancinta, amma yanzu rarraba wutar kawai muke yi," in ji shi. Sannan ya ƙara da cewa idan aka samu tangarɗa daga babban layin ƙasar, ana ɗora musu laifi ne saboda ana musu kallon Nepa.

    "Idan an samu tangarɗa ba dole ta zama daga TCN ba, domin za a iya samu a sauran ɓangarorin."

    Shugaban na TCN ya kuma bayyana lalacewar kayan aiki, a matsayin wata matsala da ke addabarsu, inda ya ce, "yawancin kayayyakin aikin da muke amfani da su sun haura shekara 50."

    A game da tsadar lantarki kuwa, Abdulaziz ya ce, wutar lantarki na da sauƙi a Najeriya, idan aka kwatanta da wasu ƙasashen Afirka irin su Burkina Faso da Senegal da Jamhuriyar Nijar.

  2. Masar ta kawar da cutar zazzaɓin cizon sauro bayan shekara 100

    Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta ce Masar ta yi nasarar kawar da cutar zazzaɓin cizon sauro - maleriya - lamarin da ya jawo wa ƙasar yabo sosai.

    "Cutar maleriya ta daɗe a ƙasar, amma yanzu an samu nasarar yaƙarta baki ɗaya," kamar yadda shugaban WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana a wata sanarwa.

    Kusan shekara 100 da suka gabata ne ƙasar ta ƙaddamar da yaƙi da cutar ta maleriya, wadda take kashe aƙalla mutum 600,000 duk shekara a duniya, mafi yawa a ƙasashen nahiyar Afirka.

    A sanarwar, WHO, ta yaba wa ƙasar Masar da mutanenta bisa ƙoƙarin da suka yi wajen "yaƙi da cutar wadda ta kasance a nahiyar tun shekaru aru-aru.

    Bayan yaƙi da cutar, kafin WHO ta ayyana nasarar ƙasar, sai da ta gamsu da shirinta na kare sake komawar cutar.

  3. Amurka na binciken yadda takardun sirri na shirin Isra'ila na kai wa Iran hari suka fito fili

    Amurka na gudanar da bincike kan wasu muhimman takardu na sirri da suka fito fili, waɗanda ke bayyana nazarin da Amurka ke yi na shirin Isra'ila na kai wa Iran hari, kamar yadda Shugaban majalisar wakilan Amurkar Mike Johnson ya tabbatar.

    Rahotanni sun ce a makon da ya wuce ne aka wallafa takardun a intanet, inda aka ce suna bayyana wasu hotunan tauraron ɗan'Adam da ke nuna yadda Isra'ila ke jigilar makamai a shirin da take yi na kai harin ramuwar-gayya na harin makami mai linzami da Iran ta kai mata ranar 1 ga watan Oktoba.

    Takardun waɗanda aka bayyana a matsayin babban sirri - ƙasashe biyar ƙawayen Amurka - Birtaniya da Kanada da New Zealand da kuma Australia na iya musayarsu a tsakaninsu, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta CBS, da ke Amurka wadda ke alaƙa da BBC ra ruwaito.

    Tsawon makonni Isra'ila ke duba lokaci da kuma yadda za ta kai wa Iran wannan hari - abin da ministan tsaron Isra'ilar ya yi gargaɗin cewa zai kasance mai muni kuma na ban mamaki da yankan shakku.

    A ranar Juma'a ne aka wallafa takardun da aka danganta da hukumar nazarin bayanan sirri na kasa na Amurka da kuma hukumar tsaron kasar ta Amurka, a wani shafin sada zumunta da muhawara na Telegram da ke da alaƙa da Iran.

    Sai dai hukumomin Amurka da Isra'ila da ke da alaka da lamarin ba su fito fili sun ce komai ba game da lamarin.

    Amurka na gudanar da bincike kan ko da niyya wani jami'in leken asirinta ya fitar da takardun ko satarsu aka yi ta hanyar kutsen intanet.

  4. Mahaukaciyar guguwa mai suna Oscar ta afka wa ƙasar Cuba

    Mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwan sama, wadda aka yi wa laƙabi da suna, Oscar, ta afka wa gabashin ƙasar Cuba.

    Rahotanni sun ce guguwar na gudun kusan kilomita 130 a cikin sa'a ɗaya.

    Ƙasar wadda ke tsibiri na fama da rashin wutar lantarki bayan matsalar da aka samu a babbar tashar lantarki ta ƙasar a ranar Juma'a, to amma Shugaba Miguel Diaz-Canel ya ce hukumomi na aiki tuƙuru don kare lafiyar al'umma.

    Bayanai na nuna cewa yanzu wannan guguwar tana kara jefa ƙasar wadda daman tuni ke fama da hauhawar farashin kayayyaki da ƙarancin abinci da magunguna da kuma tsaftacaccen ruwan sha, cikin mawuyacin hali.

  5. Malamin da aka zarga da shirya juyin mulki a Turkiyya ya rasu - Rahotanni

    Babban malamin nan na Turkiyya, Fethullah Gulen, wanda aka zarga da shirya juyin mulkin da aka zubar da jini, wanda bai yi nasara ba a ƙasar a 2016 ya rasu yana da shekara 83.

    Kafafen yaɗa labaran Turkiyya da wasu saƙonni na kafafen intanet da ke da kusanci da malamin ne suka bayyana rasuwar.

    Rahotanni sun ce malamin addinin Musuluncin wanda ke zaman gudun hijirar da sa kanshi a Amurka, ya rasu ne bayan an kwantar da shi a wani asibiti a Pennsylvania

    Malamin wanda wani lokaci ake bayyana shi a matsayin mutum na biyu mafi ƙarfin iko a Turkiyya, shi ne jagoran ƙungiyar addinin Musulunci ta Gulen, mai matuƙar tasiri da ke da mabiya a Turkiyya da sauran ƙasashen duniya.

    Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ɗora alhakin shirya juyin mulkin da aka murƙushe a 2016 a kan mabiya ƙungiyar ta Gulen, zargin da malamin ya musanta.

  6. Isra'ila ta rushe katangar sansanin dakuran MDD a Lebanon

    Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya a kudancin Lebanon ta ce wata motar rushe gine-gine ta Isra'ila ta lalata shingen tsaro da kuma katangar daya daga cikin sansanoninta.

    Wannan shi ne lamari na baya-bayan nan cikin jerin abubuwan da suka auku bayan kiran da Isra'ila ta yi da a janye dakarun rundunar ta UNIFIL daga Lebanon.

    Kakakin rundunar ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNIFIL) a Beirut, Andrea Tenenti, ya gaya wa BBC cewa wannan wani harin ne cikin waɗanda suka sha fama da su a cikin makonnin da suka gabata daga rundunar sojin Isra'ila.

    Kakakin ya ƙara da cewa wannan lamari ne da ya saba wa dokokin ƙasa da ƙasa.

  7. Kotu a Landan ta fara shari'ar fashewar dam mafi muni ta Brazil

    A yau ne babbar kotun birnin Landan ta fara sauraren shari'a kan rugujewar madatsar ruwa da ta auku a Brazi a shekara ta 2015, rugujewar wadda ita ce bala'in muhalli mafi muni a ƙasar.

    Lamarin dai ya yi sanadiyar mutuwar mutane 19 tare da lalata daruruwan gidaje.

    Wannan ita ce shari'a da ta shafi jama'a mafi yawa a tarihin Biritaniya, inda fiye da ƴan Brazil dubu ɗari shida suka shigar.

    Madatsar ruwan dai wani aikin hadin gwiwa ne tsakanin kamfanonin hakar ma'adanai na BHP da kuma Vale.

    Sun dai ki daukar alhakin lamarin inda suka ce sun riga sun biya biliyoyin dala kan ayuyukan gyara da kuma diyya

  8. Isra'ila ta kai hare-hare a bankin Al-Qard al-Hassan a Lebanon

    Isra'ila ta ce ta kai hare-hare kan gomman gine-gine da a cikinsu akwai bankunan Al-Qarda al-Hassan (AQAH) - bankin da Isra'ila ta ce yana taimakon Hezbollah.

    Akwai sassan bankin guda 34 a cikin Lebanon. Sannan kafofin watsa labarai na ƙasar Lebanon sun ruwaito cewa an kai aƙalla hare-hare guda 16 a sassan bankin a kudancin Beirut.

    Tun da farko, rundunar tsaron Isra'ila ta gargaɗi mutanen da suke zaune a sama da yankuna 20 a Lebanon - ciki har da yankuna 14 a babban birnin ƙasar - inda ta ce za ta yi luguden wuta a yankunan.

  9. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran duniya.

    Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.