Hikayata 2024: Labarai 30 da suka yi fice a gasar bana

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Bayan tantancewa, alƙalan gasar Hikayata sun zaɓi labarai guda 30 da suka ce su ne suka yi fice a gasar Hikayata ta bana.

Da farko dai BBC Hausa ta samu labarai kimanin 450 da marubuta suka aiko mata inda kuma bayan tankaɗe da rairaiya aka miƙa labarai 400 ga alƙalai na sahun farko waɗanda duka malaman jami'a ne masana harshen Hausa inda suka tantance suka zaɓi guda 30 kamar haka.

  • Labarin WANDA YA ƘI JI...na Jamila Lawal Zango
  • Labarin TSALLE DAYA na Zainab Muhammad Chibado
  • Labarin MUCIYA DA ZANE na Fa’iza Muhammad Sajo
  • Labarin RAYUWAR ZAWARCI na Fatima Adamu Fate
  • Labarin YANKINMU na Suwaiba Ishaq Zailani
  • Labarin ZAMANI RIGA na Sha’awanatu Isa
  • Labarin BUƊAƊƊIYAR WASIƘA na Zulaihat Haruna Rano
  • Labarin IGIYAR ZATO na Rahama Abdulkadir Usman
  • Labarin MADUBIN WAHALA na Sadiya Muhammad
  • Labarin WAYE SANADI na Fatima Ibrahim
  • Labarin BAKON WATA na Fatima Ibrahim Garba
  • Labarin WANDA BAI JI BARI BA….na Amina Adamu
  • Labarin TSOKACI na Kansa'u Bello
  • Labarin GARKUWA CE SANADI na Safnah Aliyu Jawabi
  • Labarin NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE Salma Ahmad Isah
  • Labarin NAƊIN LAUJE na Fauziyya Sani Jibril
  • Labarin TSAKA MAI WUYA na Sajida El Sa’idu Kulley
  • Labarin AMON 'YANCI na Hajara Ahmad Hussain
  • Labarin YI WA KAI na Maryam Abdul’aziz
  • Labarin TSAYUWAR WATA na Zainab Sulaiman
  • Labarin GUGUWAR ZAMANI na Zainab Abdullahi
  • Labarin MAGARIBAR JAKI na Safiyya Mukhtar Garba
  • Labarin GUDUNMAWAR BIKI na Dayyaba Abdulhamid
  • Labarin HALITTA BIYU na Faiza Abubakar
  • Labarin MAFITARMU na Hajara Haruna Aliyu
  • Labarin BIYU BABU na Zainab Abdurrahman Aminu
  • Labarin MUGUN NAMA na Fatima Isa
  • Labarin KURA A RUMBU na Amrah Auwal
  • Labarin UNGUWAR ZOMA na Zainab Abdulmumin Ibrahim
  • Labarin HANGEN HADARIN NESA na Zainab Ɗahiru Wowo

Nan gaba kaɗan kuma alƙalai za su zaɓi labarai 15, inda a ciki za a samu na ɗaya da na biyu da na uku da kuma guda 12 da suka cancanci yabo.

A watan Nuwamban 2024 ne dai za a yi bikin karrama gwarazan gasar na bana a birnin Abujar Najeriya, inda waɗanda suka zo na ɗaya da na biyu da na uku za su karɓi kyautukan kuɗi da lambar yabo da kuma shaidar samun nasara.