Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/06/2025

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi da Isiyaku Muhammed

  1. Isra'ila ta ce Iran ta harba mata makamai masu linzami

    Isra'ila

    Asalin hoton, EPA

    Isra'ila ta ce Iran ta harba mata wasu makamai masu linzami, kamar yadda rundunar sojin ƙasar ta bayyana a wata sanarwa.

    Ta ce tsaron sararin samaniyarta "na ta ƙoƙari domin daƙile harin," sannan ta ba ƴanƙasar shawarar su nemi mafaka har zuwa wani ɗan lokaci.

    Har yanzu dai babu cikakken bayani kan hare-haren - saboda zuwa wannan lokacin Iran ba ta tabbatar ba.

    Waɗannan hare-haren na zuwa ne jim kaɗan bayan Isra'ila ta tabbatar da tsagaita wuta. Amma ama tun farko ministan harkokin wajen Iran ya ce ba su daina ɓarin wuta ba har sai Isra'ila ta daina kai mata hare-hare.

  2. Oman za ta sanya haraji kan kuɗaɗen da ƴanƙasar ke samu

    Oman ta ce za ta sanya harajin kan kuɗaɗen da mutane ke samu, inda ta zama ƙasa ta farko a yankin Gulf da za ta aiwatar da irin wannan tsarin.

    Oman, wadda ta dogara ne kan kuɗaɗen shiga da ta ke samu daga man fetur, tana neman bunƙasa hanyoyin samun kuɗaɗen shiganta harajin ba zai fara aiki ba har sai nan da shekara ta 2028.

    Za a sanya harajin kashi biyar ne cikin ɗari kan kuɗaɗen da suka haura dalar Amurka dubu ɗari da tara.

    Kashi ɗaya bisa ɗari na al'ummar ƙasar ne ake hasahen wannan harajin zai shafa.

  3. Isra'ila ta amince da tsagaita wuta da Iran

    Netanyahu

    Asalin hoton, Reuters

    Isra'ila ta tabbatar tare da amincewa da shiga yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran a yaƙin da suke gwabzawa a tsakaninsu.

    Isra'ila ta ce ta amince da tsagaitar ce bayan "ta cimma burinta," na ƙaddamar da yaƙin a Iran tun a farko.

    A wata sanarwa da ta fitar, Isra'ila ta ce ta daƙile "dukkan barazanar" da take fuskanta daga Iran na mallakar nukiliya da makamai masu linzami.

    Sanarwar ta kuma ƙara da cewa ta "samu nasarar kawo tsaiko a tsarin shugabancin sojin Iran, da ma tarwatsa gomman kadarorin gwamnatin Iran masu muhimmanci."

    Ta ƙara da cewa hare-harenta sun "tarwatsa dakarun Basij - waɗanda ta ce ƴanbindiga ne da gwamnatin Iran ke amfani da su domin fatattakar masu zanga-zanga - sannan ta ce ta kashe masana nukiliyar ƙasar."

    "Isra'ila ta yi godiya da Trump da Amurka bisa gudunmuwar tsaro da taimakonta wajen tarwatsa barazanar nukiliyar Iran."

  4. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu ɗaura daga inda muka tsaya a jiya a wanna shafin namu na labaran kai-tsaye.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunt irin su Facebook da X da Instagram da ma zauren na Whatsapp domin karanta wasu labaran da tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.