Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/06/2025

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi da Isiyaku Muhammed

  1. Rufewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin na BBC Hausa, da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, a nan za mu rufe shafin na yau Talata - 24 ga watan Yunin 2025.

    Da fatan za ku sake kasancewa da mu a gobe Laraba, idan Allah Ya kai mu lafiya.

    Amma za ku iya ziyartar shafinmu na bbchausa.com domin ci gaba da karanta labarai da kuma kallon bidiyo da sauransu.

    Rai baƙon duniya - Allah Ya yi mana jinkiri mai amfani Ya kyautata ƙarshenmu

  2. Yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta ta fara aiki tsakanin Isra'ila da Iran

    Hoton Netanyahu da Trump da Ayatollah Ali Khamenei

    Asalin hoton, Getty Images

    Bisa ga dukkan alamu yarjejeniyar tsagaita wuta da ba ta da tabbas da aka ƙulla tsakanin Isra'ila da Iran, bayan fushin da Shugaba Trump ya nuna a kan batun ta fara aiki.

    Shugaban Amurkan ya zargi ɓangarorin biyu da saɓa yarjejeniyar tsagaita wutar da aka ƙulla tun da farko.

    Bayan tattaunawar da aka yi tsakanin Mista Trump da Benjamin Netanyahu, ofishin firaministan Isra'ilan ya fitar da sanarwar da ke cewa sun dakatar da hare-harensu.

    Wakiliyar BBC ta ce: Gwamnatin Isra'ila ta ce ta dakatar da duk hare-haren da take kai wa Iran.

    Shi ma shugaban Iran ya ce ƙasarsa za ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar, idan har Isra'ila ba ta canza matsaya ba.

    Kawo yanzu dai ƙasashen biyu sun fara sanar da sassauci a kan matakan da suka tsaurara a baya.

  3. Gwamnan Kano ya yi tir da kisan wasu matasa biyu 'yan jihar a Benue

    Abba Kabir Yusuf

    Asalin hoton, Abba Kabir/Facebook

    Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi kakkausar suka tare da yin Allah-wadarai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasa biyu 'yan jihar a garin Makurɗi, babban birnin jihar Benue.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce, a jiya Litinin ne da misalin ƙarfe 11:00 da dare wasu da ba a gano ko su waye ba har yanzu suka far ma matasan biyu - Barhama Suleiman da Jamilu Ahmad, inda suka yi musu kisan-gilla, haka kawai.

    A sanarwar gwamnan ya bayyana harin a matsayin na dabbanci da rashin imani da hankali, wanda ba za a lamunta da shi ba.

    A yayin da ya kai ziyarar ta'aziyya ga 'yan uwa da iyalan mamatan Abba Kabir ya jajanta wa fitaccen malamin nan na addinin Musulunci Sheikh Ibrahim Khalil wanda shi ne tamkar mahaifi a garesu.

    Sannan ya roƙi jama'ar jihar ta Kano da su kwantar da hankalinsu, inda ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya wajaba don ganin an yi bincike a kan lamarin tare da hukunta waɗanda suka yi kisan.

    Wannan ya faru ne kuwa yayin da ake ci gaba da alhinin kisan-gillar da aka yi wa wasu 'yan jihar Kaduna, 12 a garin Mangu na jihar Filato.

  4. Gwamnan Kano ya nuna alhininsa kan rasuwar ma'aikaciyar BBC

    Abba Kabir Yusuf

    Asalin hoton, Abba Kabir Yusuf/Facebook

    Bayanan hoto, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

    Gwamman jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya aike da saƙon ta'aziyarrasa kan rasuwar ma'aikaciyar BBC Bilkisu Babangida.

    Cikin wata sanarwa da kakain gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce marigayiyar ta bayar da gagarumar gudunmowaa fagen yaɗa labarai.

    ''Bilkisu Babangida ta bar gagarumin giɓi a fannin yaɗa labarai a duniya, wadda za a jima ana tuna irin gudnmowar da ta hayar a fannin'', in ji snarwar.

    Gwamnan ya kuma yi addu'a a madadin gwamnati da al'ummar Kano kan samun rahamar ubangiji ga marigariyar da kuma fatan samun gidan aljanna, tare da addu'ar bai wa iyalai da abokan aikinta haƙurin jure rashinta.

    Da safiyar yau Talata ne dai Allah ya yi wa Bilkisu Babangida rasuwa, bayan fama da jinya.

  5. Gwamnan jihar Kaduna ya kai wa iyalin waɗanda aka kashe a Filato ta'aziyya

    Gwamnan Uba Sani da tawagarsa

    Asalin hoton, Kaduna State Government

    Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan mutane 12 da aka kashe a Mangu, jihar Filato, a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure.

    Tawagar gwamnan wadda ta ƙunshi manyan jami'an gwamnati da tsohon gwamnan jihar Mukhhtar Ramalan ta kai ziyarar ne a Unguwan Dantsoho da ke Kudan.

    Gwamnan ya yi addu'ar Allah Ya jiƙansu Ya kuma ba wa waɗanda aka jikkata sauƙi, sannan ya bai wa iyalansu tallafi.

    Ya ce ya yi magana da shugaban ƙasa da mai bai wa shugaban shawara na musamman kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, da kuma gwamnan jihar Filato, kan su tabbatar an gano waɗanda suka aikata wannan ta'asa domin gurfanar da su gaban shari'a.

    Hukumomi sun ce zuwa yanzu an kama mutum 22 da ake zargi da hannu a harin.

  6. Yara da dama sun mutu a harin asibiti a Sudan - WHO

    ...

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana harin da aka kai wani asibiti a Sudan a matsayin "mummunan hari", inda ya ce mutum fiye da 40 sun mutu – ciki har da yara da ma’aikatan lafiya.

    A wata sanarwa da ya wallafa a shafin X ranar Talata, Tedros ya ce: “Ba za mu gaji da jaddada wannan ba – dole ne a daina kai hari kan cibiyoyin lafiya a ko’ina cikin duniya!”

    An kai harin ne a Asibitin Al-Mujlad da ke jihar Kordofan ta Yamma.

    Dakarun RSF sun zargi sojojin gwamnati da kai harin, sai dai rundunar sojin Sudan bata fitar da wata sanarwa ba har yanzu.

    Tun daga watan Afrilun 2023 da yaƙin ya ɓarke a Sudan, Majalisar Dinkin Duniya ta ce halin da ake ciki ya zama mafi muni a duniya dangane da bala’in jin kai.

  7. Shugabannin jam'iyyar PDP na ganawa da INEC

    Shugaban INEC da na PDP

    Asalin hoton, INEC

    Jagororin babbar jam'iyyar hamayyar Najeriya, PDP na wata ganawar sirri da jami'an hukumar zaɓen ƙasar a shalkwarar INEC da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da INEC din ta wallafa a shafinta na X, ta ce shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya tarbi wakilan jam'iyyar.

    INEC ta ce maƙasudin taron shi ne domin tattauna matsalolin jam'iyyar, musamman batun amincewa INEC kan gudanar da taron shugabannin jam'iyyar na ƙasa.

    Shugaban INEC da na PDP

    Asalin hoton, INEC

    A baya-bayan ne hukumar INEC ta ƙi amincewa da buƙatar jam'iyyar na gudanar da taron shugabanninta, saboda kasa cika ƙa'idojin hukumar.

    Haka kuma hukumar ta bayar hujjar rikici kan kujerar sakataren jam'iyyar a matsayin wani dalilin ƙin amincewa da buƙatar tata.

    Jagoroin PDP da suka halarci zaman sun haɗa da shugaban riƙonta na ƙasa, Amb. Umar Damagum, da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da gwamnonin jihohin Bauchi da Zamfara da Plateau kuma jihar Oyo.

    Shugaban INEC da na PDP

    Asalin hoton, INEC

  8. An ƙaddamar da aikin samar da ruwan famfo na Sokoto

    Gwamnan jihar Sokoto Adamu Aliyu da gwamnan jihar Yobe Mai mala Buni da Sarkin Musulmi na Najeriya Sa'ad Abubakar a wurin ƙaddamar da aikin samar da ruwan famfo na Sokoto

    Asalin hoton, Gwamnatin jihar Sokoto

    Bayanan hoto, Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu da gwamnan jihar Yobe Mai mala Buni da Sarkin Musulmi na Najeriya Sa'ad Abubakar a wurin ƙaddamar da aikin samar da ruwan famfo na Sokoto

    Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu ya ƙaddamar da wani ɓangare na aikin samar da ruwan famfo na babban birnin jihar wanda ake sa ran idan aka kammala zai riƙa samar da ruwa galan miliyan 40 a kowace rana ga mazauna birnin.

    A cikin jawabin da ya yi lokacin ƙaddamarwar, gwamna Aliyu ya ce ɗaukacin aikin zai laƙume kuɗi naira biliyan 14,138,289,057.

    Sai dai ana sa ran kashin na farko da aka ƙaddamar a ranar Litinin zai samar da tsaftataccen ruwan famfo galan miliyan uku a kowace rana.

    Ƙarancin tsaftataccen ruwan sha na daga cikin manyan matsalolin da ke addabar kusan dukkanin yankunan Najeriya.

    Da dama daga cikin al’ummar ƙasar masu hannu da shuni kan gina rijiyoyin burtsatse – waɗanda ake gargaɗin suna da illa ga muhalli – yayin da marasa ƙarfi kan shiga cikin hatsarin amfani da ruwa maras tsafta.

    Cibiyoyin shida da za a samar ƙarƙashin shirin samar da ruwan sha na Sokoton su ne na Tamaje, da tsohon filin jirgi na Sokoto, da Gagi da Mana da Runjin Sambo da kuma Rugar Liman.

  9. Trump ya soki Isra'ila da Iran kan karya yarjejeniyar tsagaita wuta

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Trump ya soki Isra'ila da Iran, bayan zargin ƙasashen biyu da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ƙulla ƴan sa'oi da suka wuce.

    Sukar tasa na zuwa ne bayan rahoton kai wa juna hari daga dukkan ƙasashen biyu, duk da ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta.

    Mr Trump ya ce ƙasashen sun daɗe suna faɗa da juna, kuma a wannan mataki ana iya cewa ba su ma san abin da suke yi ba.

    Ya ce: "Ba abin da muke so ke nan ba, ina tabbatar maku cewa ina fushi da abin da suka aikata."

    Shugaba Trump ne mutum na farko da ya fara sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ilan da Iran, bayan shafe kwana 12 suna kai wa juna hare-hare.

  10. Muna da alaƙa mai kyau da Qatar da sauran maƙwabtanmu - Iran

    Iran

    Asalin hoton, EPA

    Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran ya ce hare-haren ƙasarsa a Qatar, sansanin sojin Amurka suka hara, inda ya ce lamarin ba shi da alaƙa da ƙasar ta Qatar.

    Iran ta mayar da martani ne ga Amurka bayan Donald Trump ya ƙaddamar da hare-hare a cibiyoyin nukiliyar Iran, inda ya ce ya lalata cibiyoyin.

    Sai dai kakakin ma'aikatar, Esmail Baqai ya ce duk da sansanin na Qatar ne, Iran ta ɗauki matakin ne "domin kare kanta."

    "Iran na cigaba da girmama maƙwabtakanta kuma tana girmama Qatar da sauran ƙasashen da muke maƙwabtaka da su," kamar yadda Baghaei ya wallafa a shafin X.

  11. Babu barazanar tsaro a Abuja - Gwamnatin Najeriya

    Tinubu

    Asalin hoton, Twittter/@officialABAT

    Gwamnatin Najeriya ta ce babu wata barazanar a babban birnin ƙasar, Abuja, inda ta yi kira ga mazauna birnin su cigaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin lumana.

    Gwamnatin Najeriya ta bayyana haka ne a matsayin martani ga gargaɗin tsaro da Amurka ta aika zuwa ga ƴanƙasarta da ke birnin Abuja.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Ministan Watsa Labarai na Najeriya, Mohammed Idris ya fitar, inda a ciki ya ce, "gwamnatin Najeriya ta samu labarin gargaɗin da Amurka ta aika wa ma'aikatan ofishin jakadancinta da ma ƴanƙasarta da ke Abuja game da tsaro.

    "Duk da gwamnatin Najeriya na girmama haƙƙin da ofisoshin jakadanci - ciki har da na Amurka - ke da shi na ba ƴanƙasarta shawara ko gargaɗi game da matsalolin tsaro, yana da muhimmanci mu tabbatar da cewa babu wata barazanar tsaro da Najeriya ke fuskanta, sannan mazauna birnin da masu ziyara babu wata barazana da suke fuskanta."

    Sanarwar ta ƙara da cewa akwai cikakken tsaro a Abuja, "domin jami'an tsaro suna aiki ba dare ba rana domin tabbatar da daƙile dukkan wata barazanar tsaro."

  12. Yadda aka gudanar da jana'izar Bilkisu Babangida

    Bilkisu Banagida

    An gudanar da jana'izar tsohuwar abokiyarmu a BBC Hausa, Hajiya Bilkisu Babangida wadda ta rasu bayan fama da jinya na tsawon lokaci.

    Daga cikin waɗanda suka halarci jana'izar akwai shugaban sashen Hausa na BBC Hausa, Aliyu Abdullahi Tanko da abokan aikinta, da ƴaƴanta da ƴan'uwa da abokan arziki.

    An gudanar da sallar Jana'izar ce a Masallacin Abuja, sannan aka binne ta a maƙabartar Gudu da ke yankin Apo a Abuja.

    Allah ya yi mata rahama.

    Bilkisu Banagida
    Bilkisu Banagida
    Bilkisu Banagida
    Bilkisu Banagida
  13. BBC na jimamin rasuwar Bilkisu Babangida

    Bilkisu

    A yau da safe ne shugaban sashin Hausa na BBC, Aliyu Abdullahi Tanko ya sanar da rasuwar ma'aikaciyarsu, Hajiya Bilkisu Babangida.

    Ta rasu yau Talata da safe bayan doguwar jinya.

    Bilkisu na da shekaru 56 a duniya kuma ta bar 'ya'ya biyu da jikoki shida.

    Ta soma aiki ne da sashen Hausa na BBC a shekara ta 2006 a matsayin wakiliyar BBC a jihohin Borno da Yobe.

    Shahararriyar 'yar jaridar a 2009 ta yi hira da Muhammad Yusuf - mutumin da ya kafa kungiyar Boko Haram kafin mutuwarsa.

    Ta yi aiki da BBC a Abuja da kuma London.

    Allah Ya jikanta da rahama.

  14. Mali da Rasha sun ƙulla yarjejeniyar samar da makamashin nukiliya

    Mali

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Mali da Rasha sun sanya hannu a wasu yarjejeniya, waɗanda aka tsaro domin inganta alaƙar kasuwanci da tattalin arziki.

    Daga cikin abin da yarjejeniyar ta ƙunsa akwai haɗin kai domin samar da makamashin nukiliya, kamar yadda Rashar ta bayyana.

    An bayyana alaƙar ce bayan ziyarar da shugaban mulkin sojin Mali, Assimi Goïta ya kai Moscow, inda ya tattauna da Shugaban Rasha Vladimir Putin na kimanin awa biyu, kamar yadda kafar watsa labaran Rasha ta bayyana.

    Goïta dai yana ƙara ƙulla alaƙa da Rasha ne bayan juyin mulkin da ya jagoranta a shekarar 2021, sannan ya juya wa Faransa - wadda ta raini ƙasarsu baya.

    Da yake jawabi a ranar Litinin, Putin ya ce sun inganta yarjejeniyar ne, sannan suka tattaunawa hanyoyin da za su ƙara ƙulla alaƙa a "ɓangarorin ma'adinai da makamashi da agaji."

    Goïta ya yi godiya ga Rasha bisa irin "karamcin" da aka masa, sannan ya nanata shirin Mali na ɗabbaƙa yarjejeniyar, waɗanda ya ce sun ƙunshi ɓangarori da dama.

    Alaƙar tsaro dai na cikin muhimman abubuwan da ke tsakanin Rasha da Mali.

  15. BBC za ta fara yaɗa labarai cikin harshen Polish

    ...

    BBC ta buɗe sabon sashen watsa labarai da harshen Polish wato BBC Polska domin faɗaɗa hanyoyinta na yaɗa labarai da isar da saƙo a faɗin duniya.

    Daga yau Talata, shafin bbc.com/polska zai fara yaɗa labaransa na ƙashin kansa a tsari rubutu da bidiyo, tare da ƙara yaɗa su a kafofin sadarwa na zamani domin masu magana da harshen na Polish.

    Burin assasa sashen shi ne "yaƙi da labaran ƙarya," kamar mataimakin babban jami'in gudanarwa na BBC Jonathan Munro ya bayyana.

    Ya ce sashen zai isar da "labarai na gaskiya" ga masu jin harshen, a wannan zamanin da ake fama da "yaƙi da kafofin sadarwa da dimokuraɗiyya da rashin tsaro tsaro."

    Wannan na cikin tsare-tsaren BBC na faɗaɗa hanyoyinta na isar da saƙo, da "kuma ƙarfafa dimokuraɗiyya," in ji Munro.

    Sashen BBC Polska zai riƙa amfani da fasahar fassara ta ƙirƙirariyar basira wajen haɗa rahotanni daga wasu sassan duniya, da kuma wasu labaran cikin gida waɗanda ƴanjarida masu jin harshen za su haɗa.

    A yanzu haka BBC na samun masu bibiyarta kusan mutum 5.1 a Poland a duk mako - kusan rabin manyan ƴan ƙasar ke nan.

  16. Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Iran na fuskantar barazana

    An fara musayar yawu tsakanin Isra'ila da Iran kan batun yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da suke gwabzawa, wanda Trump ya sanar.

    Ga abubuwan da ake ciki yanzu:

    • Trump e ya fara wallafawa a kafofin sada zumunta cewa Iran da Isra'ila sun amince su tsagaita wuta, kuma yarjejeniyar ta fara aiki
    • Bayan kimanin awa ɗaya, sai Isra'ila ta sanar da amince da yarjejeniyar tsagaita wutar, ita kuma Iran ta ce ba za tsagaita wuta ba, har sai Isra'ila ta fara tsagaitawa.
    • Daga bisani kuma rundunar sojin Isra'ila ta ce Iran ta harba mata makamai masu linzami, sannan ta ce ta kakkaɓo wasu.
    • Daga bisani Iran ta fito ta musanta zargin kai hari a Isra'ila.
    • Isra'ila ta yi barazanar mayar da martani kan Iran.
    • Kafin a shiga yarjejeniyar, ɓangarorin biyu sun yi ɓarin wuta a tsakaninsu
    • Aƙalla mutum tara aka kashe a Iran, ciki har a wani masanin nukiliya.
    • A Isra'ila kuma, an kashe aƙalla mutum huɗu, sannan aka jikkata mutum 22.
  17. Za mu ɗauki matakin hana sake faruwar kisan mutane - Gwamnatin Filato

    Mutfwang

    Asalin hoton, @CalebMutfwang

    Gwamnatin jihar Filato ta jaddada aniyarta ta ɗaukar mataki don hana sake faruwar kisan mutane a jihar bayan kisan wasu ƴan asalin jihar Kaduna a ƙaramar hukumar Mangu da ke jihar.

    A makon jiya ne dai aka kashe wasu matafiya 12 ƴan Zaria, da ba su ji ba su gani ba, wani abu da ya janyo Allah-wadai daga ɓangarori daban-daban.

    Joyce Ramnav, ita ce kwamishiniyar watsa labarai a jihar ta Filato, ta bayyanawa BBC cewa burinsu shi ne su nuna wa duniya cewa Filato jiha ce mai son zaman lafiya, mai maraba da mutane.

    Ta ce, "jami'an tsaron sun kama mutum 22, kuma idan allah ya yarda gwamnati za ta ɗauki matakin domin a tabbatar an hukunta waɗannan mutane."

    Ta ce yanzu gwamnati na jiran sakamakon bincike ne da ƴansandan jihar ke gabatarwa, "kafin mu san matakin da za mu ɗauka na gaba."

  18. NNPCL ya ƙara farashin litar man fetur

    nnpcl

    Asalin hoton, nnpcl

    Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya ƙara farashin litar mai daga naira 910 zuwa naira 945 a gidajen mansa da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

    Haka kuma kamfanin ya ƙara farashin litar mai a gidajen mansa da ke Legas daga naira 870 zuwa 915, kamar yadda rahotanni suka nuna.

    Wannan ƙarin ya nuna an ƙara naira 35 a kowace lita a Abuja, da kuma ƙarin naira 45 a Legas.

    Jaridar Daily Trust mai zaman kanta ta ruwaito cewa tuni wasu gidajen man suka fara sayar da fetur ɗin a sabon farahi, inda ta ruwaito gidan man NNPCL da ke babbar hanyar Fin Niger Badagry ya fara sayar da man a naira 915.

    Haka kuma a gidan man kamfanin NNPCL da ke yankin Kubwa na Abuja, tuni aka fara sayar da man a naira 945.

  19. Iran ta musanta kai hare-hare a Isra'ila

    Iran

    Asalin hoton, EPA

    Kafar watsa labarai ta Iran ta ruwaito gwamnatin ƙasar na musanta zargin Isra'ila na cewa ta ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami bayan fara batun tsagaita wuta a yaƙin.

    Isra'ila dai ta ruwaito cewa Iran ta kai mata wasu hare-hare, duk da cewa ba a samu labarin mutuwa ba, amma an tabbatar da mutum ɗaya ya jikkata.

    Isra'ila dai ta yi barazanar mayar da martani kan hare-haren, inda ta zargi Iran da karya alƙawari da yarjejeniyar tsagaita wuta.

    A nata ɓangaren, Iran ta ce ba za ta tsagaita wuta ba, har sai Isra'ila ta tsagaita.

  20. Isra'ila ta ce za ta mayar da martani, bayan zargin Iran da karya yarjejeniyar tsagaita wuta

    Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    Ministan tsaron Isra'ila, Katz ya bayyana cewa ya ba rundunar tsaron Isra'ila umarni "su mayar da martani" mai tsanani kan Iran.

    Ya ce za su mayar da martanin ne domin a cewarsa Iran ta karya yarjejeniyar tsagaita bayan ta cigaba da kai hare-hare makamai masu linzami.

    Ita dai Iran ta nanata cewa ba za ta daina kai hare-haren ba har sai Isra'ilar ta daina kai mata hare-hare.

    Tun da farko dai, rundunar tsaron Isra'ila ta sanar da cewa tana ta ƙoƙarin daƙile hare-haren makamai masu linzami daga Iran.

    Shugaban aikin ceto na ƙasar, Magen David Adom ya ce mutum ɗaya ne kawai ya samu labarin ya jikkata.