Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 28/06/2024.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Ibrahim Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba da Abdullahi Bello Diginza

  1. Kotu ta ba da damar amfani da karfin soji don dakile zanga-zanga a Kenya

    ..

    Asalin hoton, REUTERS

    Babbar kotu a Kenya ta amince a yi amfani da karfin soji wajen maido da oda a kasar, bayan shafe kwanaki ana zanga-zangar adawa da kara haraji a kasar.

    Fiye da mutum 20 rahotanni suka bayyana an kashe sakamakon zanga-zangar gama-gari da matasa suka jagoranta domin nuna adawa da tsare-tsaren gwamnati na kara haraji.

    Motoci masu sulke sun yi ta shawagi a titunan Nairobi, babban birnin kasar a ranar Alhamis yayin da yan sanda suka harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar da suka yi barazanar mamaye fadar shugaban kasa.

    Wani alkali ya ce jibge sojojin muhimmin mataki ne don kare gine-ginen gwamnati sai dai ya bai wa hukumomi kwanaki biyu su yi bayani kan tsawon lokacin da sojojin za su dauka suna wannan aiki da kuma bayanin irin aikin da za su yi.

    "Jibge sojoji ba tare da sanin yadda aikin nasu zai kasance ba da kuma tsawon lokacin da za su dauka, yana da hadari da ka iya janyo yaki a kasar," in ji mai shari'a Lawrence Mugambi.

    Kungiyar lauyoyi ta Kenya wadda ta bukaci kotun ta bai wa sojoji umarnin janyewa daga tituna, ta ce "ta martaba matsayin amma kuma ba ta yarda" da hukuncin ba.

    Shugaba William Ruto a ranar Laraba ya mika wuya inda kuma ya ce zai janye kudirin da ke neman kara haraji a kasar, kwana daya bayan da masu zanga-zanga suka yi kutse a majalisar dokoki tare da cinna wuta.

    Kakakin gwamnati, Isaac Mwaura, ya shaida wa BBC cewa janye kudirin babban koma-baya ne ga gwamnati saboda ta bar wani wawakeken gibi a kasafin kudi.

  2. Annobar kwalara ta yi ajalin mutum biyu a Katsina

    Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda

    Asalin hoton, fb/Dikko Radda

    Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar mutum biyu sakamakon kwalara da ta zama annoba a Najeriya.

    Hukumomin lafiya na jihar sun ce sun dauki matakan gaggawa na dakile bazuwar cutar inda yanzu mutum 118 suka harbu a jihar.

    Dr Bishir Gambo Saulawa, kwamishinan lafiya na jihar ta Katsina ya shaida wa BBC cewa cikin matakan da suka dauka shi ne na samar da magungunan da suka kamata a matakin kananan hukumomi har da sinadarin tsaftace ruwa da suka rarraba.

    "Babban musabbabin kwalara shi ne ruwa, shi ne kuma ake kokari a rage." in ji kwamshinan.

    A cewarsa, kananan hukumomin da aka yi asarar rayukan sune Dutsinma da kuma Katsina. Ya bayyana cewa cutar ta fi kamari a karamar hukumar Kusada inda a wajen kadai aka samu mutum 62 da suka kamu da cutar ta amai da gudawa.

    Kwamishinan ya ce babban aikin da ke gabansu a yanzu shi ne na dakile bazuwar cutar inda ya nuna cewa ana wayar da kan mutane game da muhimmancin tsaftace muhallansu domin kare kansu daga kamuwa da cutar ta amai da gudawa.

  3. 'Da wuya a samu wanda ya tsira cikin mutum fiye da 30 da kasa ta ruftawa a Neja'

    ..

    Asalin hoton, MINISTRY OF SOLID MINERALS

    Mahukunta a Najeriya sun ce babu tsammanin gano ko da mutum guda da rai cikin masu hakar ma'adanan da kasa ta ruftawa a jihar Neja.

    Wannan lamari ya faru ne a yankin Galkogo na jihar sama da sati uku ke nan da suka gabata

    Honorable Yussif Shu’aibu Mani Sule Jaa, shugaban kungiyar ma’aikatan hakar ma’adanai ta kasa a Najeriya reshen jihar Naija ya ce zai yi wuya a iya tantance adadin mutanen da kasa ta danne a ibtila'in kasancewar mutumin da ake tunanin yana da bayanai game da ma'aikatan da ake aiki a wurin shi ma yana cikin wadanda lamarin ya rutsa da su.

    Sai dai a cewarsa, bayanai sun nuna mutanen da lamarin ya rutsa da su sun zarce 30.

    Jami'in ya kara da cewa shawarar da suka bayar duba da cewa lokaci na kurewa shi ne a yi kokarin zakulo gawarwakin daga karkashin kasa don yan uwansu su iya shaida su, "wadanda za a iya masu sallah, a yi masu." in ji shi.

    A iya saninsa a cewarsa, ba ya tsammanin an yi wani abu don fitar da mutanen daga inda suke ba.

    Ya bayyana cewa "dutse ne ya rushe da su a cikin kogon da suke ciki, ka san aikin ma'adinai, rami aka yi a cikin dutsen, sannan saman an barshi, kasan kuma an riga an bude, da ya tashi rushewa, sai ya rushe daga sama ya rufe da su ciki.

    Ya kara da cewa "kusan kwana ashirin da wani abu a ce mutum na kunshe a rami - ba abinci ba ruwa ba iska, tana iya daurowa a bude a samu wasu da rai, kasan Allah Sarkin iko." kamar yadda ya ce.

  4. Ana zaben shugaban kasa a Iran bayan mutuwar Raisi

    Ana zaben shugaban kasa a Iran, bayan mutuwar Ebrahim Raisi a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a watan jiya.

    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi kira ga jama'a su yi fitar farin dango, yayin da ake tunanin jama'a da dama za su kauracewa zaben.

    Akwai 'yan takara hudu, ciki har da wanda ake kallo a matsayin mai ra'ayin kawo sauyi, Massoud Pezeshkian.

    Wakiiliyar BBC ta ce sanya sunansa na iya sa wa a samu fitar masu kada kuri'a, sannan abu ne da zai sa a sake mancewa da Iran.

    Sauran su ne kakakin majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, da tsohon mai shiga tsakani na nukiliyar kasar Saeed Jalili, da kuma wani malami Mostafa Mohammadi.

  5. Barka da Safiya!

    Masu bin mu ta wannan shafi na kai tsaye da BBC Hausa ke kawo maku a kowace rana, barka da wannan rana ta Juma'a.

    Kamar yadda aka saba, a yau ma za mu wallafa maku labarai da suka shafi Najeriya da makwabtanta da ma sauran sassan duniya.

    Sai ku kasance tare da mu sannan za ku iya lekawa shafukanmu na sada zumunta - Fesbuk da X da Instagram inda nan ma akwai karin labarai har ma da bidiyo da za ku iya kalla.