Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 28/06/2024.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Ibrahim Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba da Abdullahi Bello Diginza

  1. Bissalam

    Masu bibiyarmu a nan ne kuma muka zo ƙarshen wannan shafi, sai kuma gobe Idan Allah ya kai mu.

    Kada ku manta kuna iya bibiyarmu a shafukanmu na sada zumunta don tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a kowane lokaci, har da kallon bidiyoyi a shafinmu na shafin Youtube.

    Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. EU ta ayyana sabbin takunkumai kan ''masu tallafa wa Hamas''

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ayyana sabbin takunkumai kan ɗaiɗaikun mutane da kamfanonin da ta zarga da bai wa Hamas da ƙungiyar jihadin Falasɗinawa tallafin kuɗi.

    Kamfanonin da sabbin takunkuman zai shafa sun haɗar da kamfanin 'Al Zawaya Group' da ke Sipaniya da kuma wasu kamfanonin biyu a ƙasar Sudan.

    Ƙungiyar ta ce za ta ƙwace kadarorin kamfanoni da ɗaiɗaikun mutanen da sabbin takunkuman za su shafa, tare da haramta musu tafiye-tafiye.

    A farkon wannan shekarar ce EU ta ƙaƙaba wa shugabannin ƙungiyar Hamas, ciki har da shugaban ƙungiyar na Gaza, Yahya Sinwar takunkumai.

    Haka kuma ƙungiyar ta ɓullo da sabbin matakai kan Yahudawa 'yan kama wuri zauna masu tsattsauran ra'ayi, kan zarginsu da cuzgunawa Falasɗinawa.

  3. 'Yan tawaye sun kashe mutum biyar a DR Kongo

    Rahotonni daga Jamhriyar Dimokraɗiyyar Kongo na cewa an kashe mutum biyar a wani hari da ake zargin 'yan tawayen M23 ne suka ƙaddamar.

    'Yan tawayen sun ƙwace iko da wasu yankuna biyu masu nisan kilomita 100 daga arewacin birnin Goma, bayan wata arangama da sojojin Kongo.

    Wani jami'in ƙasar ya ce mazauna yankunan sun fice daga gidajensu tun da asubahi bayan da 'yan tawayen suka ƙaddamar da hari a garuruwan.

    Firaministar ƙasar, Judith Suminwa ta kore duk wani yunƙuri na tattaunawa da 'yan tawayen M23 ba.

    Gwamnatin Kongo da Majalisar Dinkin Duniya na zargin Rwanda da mara wa 'yan tawayen baya, zargin da Kigalin ta sha musantawa.

  4. Majalisar Ɗinkin Duniya ta koka kan halin ƙazanta da Falasɗinawa ke ciki

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata ma'aikaciyar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya a Gaza ta bayyana yanayin da yankin ke ciki a matsayin mafi muni da aka taɓa fuskanta.

    Laura Wateridge, ta hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da Falasdinawa ‘yan gudun hijira, ta yi magana da manema labarai ta bidiyo.

    Ta ce ana tilasta wa fararen hula zama a tantuna da ke kusa da tarin shara da ke ruɓewa a cikin zafi.

    Ms Wateridge ta kiyasta cewa akwai kimanin tan 100,000 na shara a kusa da wani sansani guda da ke tsakiyar Gaza.

    Ta ƙara da cewa Isra'ila ta ƙi barin ma'aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya su kwashe sharar.

    Isra'ila dai ba ta mayar da martani ba, amma ta sha zargin jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya da nuna son kai.

  5. Falasɗinawa sun soki ƙudurin sabbin gine-ginen Yahudawa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan

    Jami'an Falasdinawa sun yi allah wadai da sanarwar da ministan Isra'ila mai tsattsauran ra'ayi ya yi na cewa zai amince da sabbin gine-ginen Yahudawa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye.

    Hukumar Kula da Falasɗinawa ta PA ta ce ƙaruwar gine-ginen Yahaudawa a yankin ya saɓa wa dokoki da yarjejeniyoyin duniya.

    A ranar Alhamis ne ministan kuɗi na Isra'ila, Bezalel Smotrich, ya ce nan ba da jimawa ba za a amince da sabbin gidajen 'yan kama wuri zauna.

    Ya kuma ce zai soke izini da fa'ida ga jami'an hukumar Falasɗinawa - don ladabtar da ita saboda goyon bayan shari'ar da ake yi wa Isra'ila a kotun duniya da kuma yunƙurin ƙasashen duniya na baya-bayan nan na amincewa da ƙasar Falasdinu

  6. 'Rashin adalci ne ke haddasa riciki tsakanin manoma da makiyaya'

    .

    Asalin hoton, Umar Namadi/X

    Bayanan hoto, Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi

    Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Muhammad Namadi ya ce makiyayan da ke yi wa manoma ta'adi a gonakinsu, suna yi ne da nufin martani ga ƙwace musu wuraren kiwo.

    Gwamnan ya bayyana haka ne ranar Juma'a a cikin shirin 'Sunrise Daily' na gidan talbijin na Channels, lokacin da yake magana kan matsalar tsaro a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

    Mallam Umar Namadi ya ce mafi yawan abin da ke haddasa rikici tsakanin manoma da makiyaya shi ne manoma sun ƙwace wa makiya burtalai, da wuraren kiwo da mashayar dabbobinsu.

    ''A kan haka ne suke ganin kamar ana zaluntarsu, don haka suna buƙatar ɗaukar fansa, don haka suna yi ne da nufin ɗaukar fansa'', in ji gwamnan.

    ''Saboda tsoron kisa da manoman ke yi, ya sa suke barin gonakinsu, suna komawa amfani da kudi wajen sayen abin da za su ci''.

    Gwamna ya kuma ce abin da ya kamata gwamnati ta yi shi ne yi wa kowane ɓangare adalci ta yadda zai ji a zuciyarsa cewa ba a nuna masa bambanci.

    ''Da Bafulatani da Bahaushe da Kanuri kowa yana da 'yanci a ba shi damar ya gudanar da harkokinsu''.

    Gwamna ya ce a lokacin da ya karɓi mulki ya yi ƙoƙarin magance wannan matsala, ya kuma kawo yanzu ana samun ci gaba.

    ''Jihar Jigawa, jiha ce mai albarkar noma, don haka dole ne gwamnati ta yi duk abin da ya dace domin samar wa manoma yanayi mai kyau domin inganta sana'ar''.

    Jihar Jigawa dai na daga cikin jihohin ƙasar da ke fama da rikicin manoma da makiya, lamarin da ke haddasa asarar rayuka a wasu lokuta

  7. An zaɓi sabon mai ajiyar makullin ɗakin Ka'aba

    ..

    Asalin hoton, Haramain

    Bayanan hoto, Sheikh Abdul Wahab ne mutum na 110 a jerin masu kula da Ka'abar tun daga kan Sahabi Uthman bin Talha

    Iyalan Al Shaiba masu alhakin kula da ɗakin Ka'abah sun zaɓi Sheikh Abdul Wahab bin Zain Al-Abidin Al-Shaibi a matsayin wanda zai riƙe makullin ɗakin Ka'aba, bayan mutuwar Sheikh Saleh Al Shaiba a makon da ya gabata.

    Sheikh Abdul Wahab, mai shekara 78 shi ne mutum na 110 a jerin magadan Sahabi Uthman bin Talha, wanda ya fara ajiye makullin Ka'abar a zamanin Manzon Allah (S.A.W), kamar yadda shafin Haramain ya ruwaito.

    An zaɓi Shehin malamin ne a wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar a gaban fitattun mutanen iyalan zuri'ar Al-Shaiba da ke kula da makullin ɗakin.

    A lokacin bikin an miƙa makullin a hukumance zuwa hannun Sheikh Abdul Wahab, lamarin da ke alamta karɓar aikin kula da ɗakin mafi tsarki a musulunci.

    Iyalan Al-Shaiba sun samu darajar ba su damar kula da ɗakin Ka'abah na tsawon ƙarnuka, aikin da ake kallo a matsayin mai ƙima da daraja a duniyar musulunci.

    Yayin da yake jawabi a lokacin bikin, sabon mai kula da Ka'abar ya ce a shirye yake wajen martaba al'adar da aka san zuri'ar Shaiba da ita ta kula da ɗakin.

  8. An dakatar da dagaci da kansila kan zargin hannu a satar taransifoma a Gombe

    .

    Asalin hoton, Gombe State Govt

    Bayanan hoto, Gwamna Inuwa Yahaya ya alƙawarta hukunta duk wanda aka samu da hannu a laifin

    Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya amince da dakatar da dagacin garin Majidadi da ke yankin ƙaramar hukumar Akko, Mohammed Majidadi bisa zargin hannu a sace wata taransifoma.

    Cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya fitar, ya ce majalisar ƙaramar hukumar Akkon ta kuma dakatar da kansilan mazaɓar Kumo ta Gabas, Abdullahi M. Panda bisa wannan zargi.

    A baya-bayan nan ne dai rundunar 'yan sandan jihar ta yi holen mutanen biyu da ta ce ta kama bisa zargin haɗa baki da ɓarayi wajen sayar da taransifomar lantarkin Garin Majidadi.

    Sanarwar ta ce an dakatar da mutanen biyu daga muƙamansu ne domin bayar da damar gudanar da bincike yadda ya dace.

    Gwamnan jihar ya ce yana da ƙwarin gwiwa doka za ta yi aiki a kan mutanen idan aka same su da laifin da ake tuhumarsu da shi.

    Gwamna ya ƙara da cewa baya ga mutanen biyu, duk wanda aka samu da hannu a sayar da taransifomar zai fuskanci hukunci.

  9. An rufe kantinan sayar da magani 531 a Abuja

    Hukumar da ke kula da haɗa magunguna a Najeriya, Pharmacy Council of Nigeria (PCN) ta rufe kantinan sayar da magani guda 531 waɗanda suka saba ka'ida a birnin tarayyar Abuja, tsakanin ranar Litinin zuwa Alhamis.

    Darektan da ke tabbatar da bin ƙa'ida na hukumar ne, Pharm. Stephen Esumobi ya bayyana hakan ranar Juma'a a yayin bayani ga manema labarai a Abuja.

    Ya ce mutanen da ke sayar da magungunan ba su da ilimin yawan maganin da ya kamata bai wa marasa lafiya da kuma abin da ya kamata a yi a yanayin da maganin bai karɓi.

    “Su waɗannan magunguna ya kamata a ce a asibiti ake bayar da su,” in ji Stephen.

  10. An ba da belin jagoran yan adawa a Indiya da aka zarga da halasta kudin haram

    Wata kotu a Indiya ta bayar da belin wani babban jigon 'yan adawa da ake zargi da halasta kudaden haram.

    An tsare Hemant Soren, tsohon babban minista a gabashin jihar Jharkhand a watan Janairu, yan watanni kafin babban zaben kasar.

    Jam’iyyarsa ta ce zargin da ake yi masa na da alaka da siyasa da nufin hana shi yakin neman zabe a babban zaben kasar a wannan lokacin.

    Jam'iyyun adawa sun zargi firaministan Indiya, Narendra Modi, da yin amfani da hukumomin gwamnatin wajen cutar da abokan hamayyarsa amma gwamnatin ta musanta haka inda ta ce hukumonin na gudanar da ayyukansu ne kawai.

  11. 'Yan wasan Amurka sun sha kalaman wariya bayan rashin nasara a Copa America

  12. Yadda Biden da Trump suka yi gaba-da-gaba a muhawarar shugaban Amurka

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Shugaban Amurka, Joe Biden da tsohon shugaban Amurka Donald Trump sun kara a wata zazzafar muhawara wadda ita ce ta farko tsakanin 'yan takaran zaɓen na wannan shekarar.

    Zazzafar muhawarar dai ta ƙunshi jifar juna da miyagun kalamai kuma abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne yadda Shugaba Biden ya rinƙa inda-inda da sakin layi yayin muhawarar.

  13. An kama mutum 143 bisa zargin garkuwa da mutane a Kaduna

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar yan sanda a jihar Kaduna ta tabbatar da kamen mutum 143 da ake zargi masu satar mutane ne da kuma yan fashi a wurare daban daban na jihar a tsukin wata biyu.

    Kwamishinan yan sandan jihar, Audu Dabigi ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da manema labarai a hedikwatar rundunar inda ya ce an gano wasu manyan makamai daga hannun mutanen.

    Mutanen da aka kama sun hada da yan fashi 73 sai yan bindiga 70 ciki har da wanda ake nema ruwa a jallo da aka damke a lokacin da yake kokarin hada wa yan bindigar wani tsubbu domin gudanar da ayyukansu.

    Ya kara da cewa yan sandan sun halaka yan bindiga tara cikin wata biyu da suka gabata.

    Dabigi ya ce cikin makaman da aka gano a hannun mutanen da ake zargi sun hada da bindiga kirar AK47 da wasu bindiga kirar gida da kuma alburusai da dama.

    Ya kara da cewa an sake kama mutum 985 da ake zargi masu satar waya ne da yan fashi takawas da kuma wani da ake zargi da satar kaya a tashar jirgin kasa.

  14. Ko za a iya sauya Biden kafin zaben watan Nuwamba?

    ..

    Asalin hoton, GETTY IMAGES

    Muhawara mai zafi da aka tafka tsakanin shugaban kasar Amurka, Joe Biden da Donald Trump ta janyo cece-kucen ko Biden na iya janyewa daga takarar shugabancin kasar yayin da ya rage kasa da wata shida a yi zabe.

    Sai dai ko da Biden zai janye, batun sauya shi lamari ne mai dadewa da sarkakiya.

    Tuni duka jihohin Amurka 50 suka gudanar da zaben fitar da gwaninsu. Kuma a kowace jiha, Biden ya samu kuri'a daga kusan duka "wakilai" - jami'an da ke zabar dan takara a kowane taron jam'iyyar.

    Mutumin da ke da iko kan wadan nan wakilai sune Biden - wani abu da ba lalle ya faru ba sai dai idan ya sauya matsaya kafin taron jam'iyyar Democrat a watan Agusta.

    Kuma idan Biden ma zai janye, yan Dimokrat za su gamu da wani babban kalubale na wanda zai maye gurbinsa.

    Kuri'ar jin ra'ayi ta nuna mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris ba za ta yi fice ba a tsakanin Amurkawa. Sai dai babu wani kwakkwaran dan takara da zai iya kada Donald Trump.

  15. 'Ƴan bindiga' sun sace mahaifiyar mawaƙi Dauda Kahutu Rarara

    ...

    Asalin hoton, fb/Dauda Kahutu Rarara

    Rundunar ƴansandan Najeriya a jihar Katsina ta ce ta kama mutum biyu bisa zargin su da hannu a garkuwa da mahaifiyar wani fitaccen mawaƙin Hausa, Dauda Kahutu Rarara.

    A tattaunawarsa da BBC, Mai magana da yawun rundunar a Katsina, Sadiq Hikima ya ce "muna tsare da mutum biyu kan lamarin, muna ci gaba da bincike".

    Tun farko, kwamishinan tsaro na jihar Katsina, Nasiru Mu'azu ya ce an sace dattijuwar ce a daren Juma'a a ƙauyen Kahutu da ke ƙaramar hukumar Ɗanja.

    Mu'azu ya ce waɗanda suka sace matar sun yi hakan ta hanyar bi ta bayan gida, inda suka sace ta ba tare da jami'an da ke tsaron gidan sun sani ba.

    Ya kuma bayyana cewa tuni aka tura jami'an tsaro waɗanda suka bazama cikin dazuka domin bin sawun ƴan bindigan

    Katsina na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fuskantar matsalar tsaro, inda ƴan bindiga ke kashewa tare da yin garkuwa da mutane.

    Hakan ya durƙusar da sana'o'i da harkoki na yau da kullum.

  16. Mayakan Boko Haram uku sun mika wuya ga sojoji

    Mayakan kungiyar Boko Haram uku sun mika wuya ga sojojin hadin gwiwa da ke fatattakar masu tayar da zaune tsaye yankin tafkin Chadi a karkashin shirin Lake Sanity 2.

    Wata sanarwa da kakakin rundunar da ke yakar Boko Haram a kasashen Kamaru da Najeriya da Nijar da Chadi, Leftanat Kanar Abubakar Abdullahi ya ce mayakan Boko Haram biyu ne suka mika wuya ga sojoji a yankin Wulgo da ke Kamaru.

    A cewar sanarwar, runduna ta uku a Najeriya ta bayar da rahoton dan Boko Haram guda ya mika wuya a yankin Baga, kamar yadda gidan Talabijin na Channels ya ruwaito.

    Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa mutumin ya shafe shekara shida yana zama a yankin Kwaleram da ke tafkin Chadi a matsayin dan kungiyar Boko Haram.

    Sanarwar ta kara da cewa "a wani bangare na ayyukan rundunar hadaka ta dakarun kasashe da ke yaki da 'yan Boko Haram a yankin tafkin Chadi, runduna ta 1 a Kamaru ta soma wani shiri kyauta na duba lafiya a yankunan Darak da Kofia da Hile Alifa da Soueram da kuma yankin arewa mai nisa a Kamaru."

    Ta ce an bijiro da shirin domin kula da lafiyar al'ummar da ayyukan rundunar ya shafa inda take duba su kyauta tare da ba su magunguna don kula da lafiyarsu.

  17. Zanga-zanga ta fara lafawa a Kenya

    Al'amura sun soma lafawa a Nairobi, babban birnin Kenya bayan shafe kwanaki matasa a kasar na zanga-zangar nuna kin jinin dokar kara haraji da gwamnati ta bijiro da ita.

    Jami'an tsaro na shawagi a titunan birnin Nairobi, cibiyar da aka yi ta arangama tsakanin masu zanga-zangar da kuma yan sandan kwantar da tarzoma a ranar lhamis.

    Harkokin kasuwanci sun bude, wasu kuma na tantance irin barnar da suka yi sakamakon zanga-zangar.

    Wata kotu a ranar Alhamis ta yi fatali da bukatar wata kungiyar lauyoyi ta hana girke sojoji domin tallafawa yan sanda wajen dawo da zaman lafiya.

    A ranar Laraba ne, shugaba William Ruto ya soke aniyarsa ta sa hannu kan kudirin dokar kara harajin da ya janyo fushin al'umma.

  18. Nunez ya taimaka wa Uruguay kaiwa zagayen gaba a Copa America

  19. Yau za a binne gawar Mista Ibu

    ...

    Asalin hoton, MR IBU/INSTAGRAM

    A yau ne iyalai da ƴan'uwan ɗan wasan barkwanci na Najeriya, wato Mista Ibu ke binne shi a jihar Enugu da ke kudancin ƙasar.

    Za a binne gawar ne a ƙauyen Eziokwe Muri da ke ƙaramar hukumar Nkanu West na jihar ta Enugu.

    Mista Ibu ya rasu ne a ranar 2 ga watan Maris, 2024 bayan fama da jinya.

    Rashin lafiyar ta kai ga yanke ɗaya daga cikin ƙafafun ɗan wasan na barkwanci, sai dai duk da haka nan cutar ta yi sanadin mutuwarsa.

  20. Shin Trump zai amince da sakamakon zaben Nuwamba?

    ..

    Daya daga cikin martanin da mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris ta yi bayan muhawarar da aka tafka tsakanin tsohon shugaban kasar Donald Trump da Joe Biden shi ne Trump "ba zai bayar da tartibiyar amsa ba kan ko zai amince da sakamakon zabe."

    Duk da tambayar da yar jarida Dana Bash da ta jagoranci muhawarar ta yi ta yi masa kan ko zai amince da saKamakon zaben watan Nuwamba, Trump ya yi shakulatun bangaro.

    A yunkuri na uku kuma sai Trump ya kada baki ya ce zai amince da sakamakon "idan har aka yi zabe sahihi mai nagarta".

    Tsohon shugaban kasar ta Amurka ya kuma sake nanata ikirarinsa mara tushe na batun yin magudi a zaben da aka yi a 2020.