Nuno Santo zai ci gaba da horar da Forest zuwa 2028
Nuno Espirito Santo ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da horar da Nottingham Forest har zuwa karshen kakar 2028, sakamakon da ya kai ƙungiyar zuwa gasar zakarun Turai a karon farko tun bayan 1995-96, kamar yadda ungiyar dake buga Premier League ta sanar ranar Asabar.
Nuno, ɗan kasar Portugal ya horar da Wolverhampton Wanderers da kuma Tottenham Hotspur, ya koma aikin kociyan Forest a Disambar 2023, wanda ya hana ƙungiyar faɗuwa daga Premier League.
Sai kuma Forest ta kare a mataki na bakwai a teburi a 2024/25 - mataki mafi ƙyau tun bayan shekara 30.
Forest za ta wakilci Ingila a Conference League a kaka mai zuwa ta zakarun Turai.