Man United ta kara farashin Mbeumo zuwa £60m
Manchester United ta mika karin farashin £60m domin sayen ɗan wasan Brentford, Bryan Mbeumo.
A watan nan United ta taya ɗan wasan mai shekara 25 kan £45m da karin tsarabe-tsaraben da ya kai £10m.
Ana sa ran United za ta ci gaba da tattaunawa kan cinikin ɗan wasan da zai zama na biyu da za ta saya.
Tuni United ta sayi Matheus Cunha kan £66.5m daga Wolverhampton.
United za ta fara karɓar horo daga ranar 7 ga watan Yulin 2025.
To sai dai sabon kociyan Tottenham, Thomas Frank na son ɗaukar Mbeumo, harma yana ƙwaɗaita masa cewar za su buga Champions League a kaka mai zuwa.
Frank ya bar aikin horar da Brentford ya koma Tottenham, wanda ya maye gurbin Ange Postecoglou.