Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Neymar zai ci gaba da taka leda a Santos

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku dukkan abubuwan dake wakana a fannin wasanni a faɗin duniya daga Asabar 21 zuwa Juma'a 28 ga watan Yunin 2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da Abdulrazzaq Kumo

  1. Stone yana takaici da yawan jinya da yake fama

    John Stones admits there were times he doubted if his career would resume amid a series of injury problems over the past two years.

    The Manchester City and England centre-back made only six Premier League starts in the 2024-25 season after thigh, foot and other undisclosed issues.

    That came after he also missed two months at the start of the previous campaign with a hip injury.

    These setbacks have prevented the 31-year-old building on what was an outstanding season in 2022-23 when, playing a hybrid defence-midfield role, he helped City win the treble.

    Stones has now battled his way back to fitness and is hoping to play a big part in City's challenge at the Club World Cup in the United States.

    He has not featured since February when he was forced off after just eight minutes against Real Madrid. He was an unused substitute in their opening game of the tournament against Wydad Casablanca on Wednesday.

  2. Chelsea na shirin sayar da ɗan wasan gaban Senegal Nicolas Jackson, mai shekara 24, a daidai lokacin da ƙungiyoyin Italiya Juventus da Napoli ke zawarcinsa. (Gianluca Di Marzio)

    Har yanzu Bayern Munich ba ta fidda rai kan ɗaukar ɗan wasan Sifaniya Nico Williams, mai shekara 22, daga Athletic Bilbao ba, duk da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ɗan wasan da Barcelona. (Mundo Deportivo)

    Ɗan wasan gaban Manchester United Marcus Rashford, mai shekara 27, komawa Barcelona duk da cewa kulob ɗin na gab da ɗaukar Williams. (Times)

  3. Mutum uku sun mutu a sitadiya a Algeria

    Mutum uku sun mutu, bayan da suka faɗo daga bene a sitadiya a Algeriya, bayan busa tashi daga wasan da MC Alger ta lashe babban kofin lik na kasar, in ji ministan lafiya.

    Da dama kuma sun ji rauni a lokacin da shinge ya karye, bayan da ƴan kallo suka jingina don taya murna a filin wasa da ake kira 5 July Stadium a Algeria.

    Sama da ƴan kallo 70 aka duba lafiyarsu a asibiti, kuma an sallami wasu da yawa daga cikinsu.

    Ƴan wasa da mahukuntan MC Alger sun je asibitin da aka kwantar da ƴan kallon, domin bayar da gudunmuwar jini ga masu bukata ta gaggawa.

    Filin wasan ya ɗinki da ƴan kallo a wasan da MC Alger ta kara lashe kofin da ta ɗauka a bara.

    Tun kan a tashi daga karawar magoya baya suka kunna abubuwan tartsatsin wuta mai launin shuɗi da ya turnike filin.

    Sakamakon haɗarin da ya faru ba a bai wa MC Alger kofin ba, sai nan gaba.

    Tuni shugaban kasar Algeria, Abdelmadjid Tebboune ya mika ta'aziyyarsa ga waɗanda suka mutu, sannan ya yi fatan samun sauki ga waɗanda ke kwance a asibiti.

    MC Alger ta samu ɗaukar kofin bana na biyu a jere, bayan tashi 0-0 da NC Magra.

  4. Wasannin Club World Cup a Amurka ranar Lahadi

    Rukuni na biyar

    1 River Plate da Monterrey a filin wasa na Rose Bowl Pasadena

    Rukuni na bakwai

    2 Juventus da Wydad Casablanca a filin wasa na Lincoln Financial Field

    Rukuni na takwas

    3 Real Madrid da Pachuca a filin wasa na Bank of America Stadium

    4 Red Bull Salzburg da Al Hilal a filin wasa na Audi Field

  5. Rashford ya ce yana son taka leda tare da Yamal a Barcelona

    Ɗan wasan Manchester United, Marcus Rashford ya ce yana son ya taka leda tare da matashin ɗan wasa, Lamine Yamal a Barcelona.

    Ɗan ƙwallon tawagar Ingila, mai shekara 27, wanda ya buga wasannin aro a Aston Villa a karshen kakar da aka kammala, yanzu haka yana atisaye a Sifaniya, wanda ake ta raɗe-raɗi kan makomarsa a United.

    Yamal ɗan wasan tawagar Sifaniya, mai shekara 17, ya taka rawar gani a Barcelona a kakar da ta kare, inda ƙungiyar ta kai daf da karshe a Champions League da lashe La Liga da Copa del Rey da Spanish Super Cup da doke Real Madrid karo huɗu a kakar da ta wuce.

    Haka kuma Yamal ya taka rawar gani a tawagar Sifaniya da ta lashe Euro 2024 a Jamus.

  6. Mbappe ba zai buga wasan Pachuca ba a Club World Cup

    Ɗan wasan Real Madrid, Kylian Mbappe bai yi atisaye ba ranar Asabar, kenan ba zai buga wasa da Pachuca ba a rukuni na takwas a Club World Cup.

    An kai Mbappe asibiti a Miami a farkon makon nan, zai ci gaba da jinya a otal ɗin ƙungiyar, kenan ba zai je Charlotte ba Arewacin Carolina a karawar da Real Madrid za ta yi ranar Asabar.

    Mbappe bai yi wasan farko a cikin rukuni ba da Al-Hilal da suka tashi 1-1, inda RB Salzburg ke jan ragamar rukuni da maki uku, bayan cin Pachuca ta Mexico 2-1.

    An killace Mbappe tun daga ranar Talata daga baya aka kai shi asibiti ranar Laraba daga baya aka sallame shi ranar Alhamis.

    Real Madrid ta sanar cewar da ƙyar ne idan Mbappe zai buga wasa a zagayen cikin rukuni a Club World Cup a Amurka.

  7. Lehecka ya kai zagayen karshe a Queens Club

    Ranar Asabar Jiri Lehecka ya kai zagayen karshe a Queens Club, bayan doke Jack Draper da cin 6-4 4-6 7-5.

    Ya zama na farko daga Jamhuriyar Czech da ya kai zagayen karshe a ATP a wasan kan ciyawa tun bayan shekara 15.

  8. Duran ya sayi hannun jari a Paris St Germain

    Fitatcen ɗan wasan ƙwallon ƙwandon Amurka, NBA Kevin Durant ya sayi hannun jari a Paris St German, wadda ta lashe Champions League a kakar tamaula da ta wuce.

    Mai wasa a Phoenix Suns zai kuma bayar da shawara lokacin da PSG za ta buɗe ƙungiyar ƙwallon ƙwando.

    Duran zakaran ƙwallon ƙwando karo biyu da lambar zinare huɗu a Olympic tuni ya saka hannu kan kwantiragi.

  9. Vondrousova ta kai wasan karshe a Berlin Open

    Marketa Vondrousova ta yi waje da wadda take ta ɗaya a ƙwallon tennis a duniya, Aryna Sabalenka da cin 6-2 6-4 ta kai zagayen karshe a Berlin Open ranar Asabar - karon farko da ta yi wannan ƙwazon tun bayan da ta lashe Wimbledon a 2023.

  10. Idan Onana ya bar Old Trafford, Manchester United za ta karkata ga golan Atalanta ɗan asalin Italiya Marco Carnesecchi mai shekara 24 domin ya maye gurbinsa. (Gianlucadimarzio - in Italian, external)

    Manchester City ta shirya sakar wa Ilkay Gundogan marar barin ƙungiyar a wannan bazara yayin da Galatasaray ta Turkiyya ke duba yiwuwar sayen ɗanwasan tsakiyar Jamus ɗin mai shekara 34. (Guardian, external)

    Paris St-Germain da ta lashe Gasar Zakarun Turai ta gabatar da tayi karo na biyu kan ɗanwasan Bournemouth Illia Zabarnyi da jumullar kuɗi fam miliyan 55 sai dai ƙungiyar ta kimanta darajar ɗanwasan na Ukraine mai shekara 22 kan sama da fam miliyan 70. (Sky Sports)

  11. Alkalan wasanni a Italiya za su samu kariya - in ji Abodi

    Alkalin wasanni a Italiya za su samu kariya kamar na ƴansanda da jami'an gwamnati, in ji mimistan wasanni, Andrea Abodi, domin a kawo karshen cin zarafin da ake yi musu.

    Kenan za a ɗauki matakai tsaurara da cin tara har da zaman gidan yari da zarar an ci zarafin alkalin wasa har da idan ka ture shi da nufun cin zarafi ko duka ko yin barazana.

    An kai ga cimma wannan matakin bayan tattaunawa da aka yi tsakanin gwamnatin Italiya da hukumar alkalan tamaular kasar.

    Ranar Juma'a gwamnati ta amince da hukuncin ta kuma ce hukunci zai bayar da kariya da dukkan alkalan da suke jan ragamar wasanni a faɗin kasar.

    Ana ta samu karuwar cin zarafin alkalan wasan tamaula a Italiya a karo da dama.

  12. Alcaraz ya kai wasan karshe a Queens Club

    Carlos Alcaraz ya kai wasan karshe a Queen a karo na biyu, bayan da ya caskara Roberto Bautista Agut da cin 6-4, 6-4 ranar Asabar cikin minti 90.

    Kenan Alcaraz zai fuskanci Jiri Lehecka a wasan karshe ranar Lahadi, bayan da ɗan kasar Jamhuriyar Czech ya yi waje da Jack Draper da cin 6-4, 4-6, 7-5 a ɗaya wasan daf da karshe.

    Tun bayan da Alcaraz ya doke Jannik Sinner ya lashe French Open mako biyu da ya wuce, mai shekara 22 ya kai wasan karshe karo na biyar a jere bayan da ya ɗauki kofi a gasar kan taɓo a Paris da Paris da Rum da Barcelona da kuma Monte Carlo.

    Alcaraz na fatan zama na farko da zai lashe gasar ta Queens Club karo na biyu tun bayan bajintar Feliciano Lopez a 2017 da kuma a 2019.

  13. Koriya ta Kudu ta amince a ɗauko mai tsaron raga daga wajen kasar

    An amince ƙungiyoyin dake buga babbar gasar Koriya ta Kudu su sayo gola daga waje daga kaka mai zuwa, bayan da aka hana yin hakan shekara 27 da ta wuce.

    An kafa dokar tun daga 1999, an kuma yi haka ne domin a bai wa masu tsare raga ƴan kasa damar buga wasanni a babbar gasar kasar.

    Tun farko ƙungiya 10 ake da ita mai buga gasar tamaula ta kwararru ta ta Koriya ta Kudu a shekara 26 da ta wuce, amma yanzu sun kai 26 tsakanin babbar gasa da mabiyarta.

  14. Rodri zai koma kan ganiya cikin ƙanƙanin lokaci - Nico Gonzalez

    Nico Gonzalez ya ce yana da tabbaci Rodri zai koma kan ganiya a karamin lokaci, wanda ya buga wa Manchester City Club World Cup.

    Wanda ya lashe ƙyautar Ballon d'Or bai samu buga wasa da yawa ba a 2024/25, bayan raunin da ya ji a watan Satumba a karawa da Arsenal a Etihad.

    Ya koma buga wa City tamaula a wasa da ya yi minti bakwai a karawa da Bournemouth a Premier League a watan jiya, sannan ya buga wasan da City ta doke Wydad Casablanca 2-0 a Club World Cup a Philadelphia.

    Gonzalez, wanda yake buga gurbi irin na Rodri ya koma City a watan Janairu, domin maye gurbin ɗan kasar Sifaniya.

  15. Ƴan wasan da suke buga wa Real Madrid Club World Cup a Amurka

    Masu tsare raga: Courtois, Lunin, Fran González, Sergio Mestre.Masu tsare baya: Carvajal, Militão, Alaba, Alexander-Arnold, Lucas Vázquez, Fran García, Rüdiger, Mendy, Huijsen, Youssef, Jacobo, Asencio, Fortea, Diego Aguado.Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Modrić, Tchouameni, Arda Güler, Ceballos, Chema, Víctor Muñoz, Mario Martín.Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Mbappé, Rodrygo, Endrick, Brahim, Gonzalo.

  16. Liverpool ta ɗauki Kerkez daga Bournemouth

    Liverpool ta amince da farashin £40m, domin sayen Milos Kerkez daga Bournemouth.

    Ɗan wasan tawagar Hungary, mai shekara 21, zai koma Anfield da taka leda, bayan kaka biyu a Bournemouth.

    Tuni dai Bournemouth ta ɗauki Adrien Truffert daga Rennes a madadin Kerkez.

    Liverpool ta amince da cinikin Kerkez, bayan da take daf da kammala sayen Florian Wirtz daga Bayern Leverkusen a matakin mafi tsada da za ta saya kan £116m.

    Haka kuma ƙungiyar Anfield, wadda ta ɗauki kofin Premier League a kakar da ta wuce ta sayi Jeremie Frimpong kan £29.5m.

    Kerkez, wanda aka haifa a Serbia ya fara taka leda a ƙungiyar Gyor dake Hungary daga nan ya koma wasa a AC Milan.

  17. Ya yi wuri da Mastantuono ya koma Real Madrid

    Ya yi wuri da Franco Mastantuono ya koma Real Madrid da taka leda, bayan da mai shekara 17 ya kamata ya kara nuna kansa a River Plate, wanda yake cikin kashin bayan ƙungiyar, in ji koci, Marcelo Gallardo a lokacin da ƙungiyar Argentina ke shirin fuskantar Monterry a Club World Cup.

    Gallardo ya ce tafiyar Mastantuono ya bar gurbi a ƙungiyar, bayan da zai koma buga gasar Spaniya, sakamakon kammala cinikin da ya kai $45 million daga River Plate a farkon watan nan.

    Kocin ɗan kasar Argentina ya ce kamata ya yi Mastantuono ya kara bunkasa wasansa, domin kada ya je can yake ɗumama benci, amma ya ce ya san da cewar haka ƙwallon wannan zamanin ke bukata matasa tun daga lokacin da suka nuna kansu..

  18. Palmeiras ta koma atisaye bayan da ta doke Al-Ahly

    Palmeiras ta koma yin atisaye a Greensboro, Arewacin Carolina, bayan cin Al-Ahly 2-0 a New Jersey MetLife Stadium a Club World Cup.

    Da wannan sakamakon ƙungiyar Sao Paulo tana jan ragamar rukunin farko da maki huɗu iri ɗaya da Inter Miami ta Lionel Messi, waɗanda za su fuskanci juna a wasa karshe a cikin rukuni.

    Idan suka yi canjaras a karawar da za suyi a Hard Rock, za su kai zagayen ƴan 16 a matakin Palmeiras ta ɗaya da kuma Inter Miami ta biyu - duk sakamakon da za a samu tsakanin Porto da Al-Ahly ba zai hana kaisu zagaye na biyu ba da zarar sun tashi canjaras.

  19. Juventus a Serie A na sha'awar ɗanwasan Manchester United Jadon Sancho a wannan bazara yayin da zakarun Italiya - Napoli ke cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗanwasan Ingilan mai shekara 25 wanda ya shafe kakar da ta gabata yana matsayin aro a Chelsea. (Sky Sports, external)

    Zarin Liverpool na musayar ƴan wasa bai kai ga neman ɗan wasan Newcastle Alexander Isak, mai shekara 25 ba inda ake ganin za a iya cimma yarjejeniya da ɗan asalin Sweden ɗin nan kusa. (Telegraph - subscription required)

    Sai dai kocin Liverpool Arne Slot na zawarcin ɗanwasan Crystal Palace da Ingila Marc Guehi, mai shekara 24. (Talksport)

    Guehi zai koma Anfield ne idan ya samu tabbacin cewa zai kasance cikin ƴanwasan sahun farko da za su taka leda a filin wasa. (Sky Sports)