Gwamatin Najeriya ta yi ƙarin kuɗin kafa jami'o'i

Asalin hoton, Other
Gwamantin Najeriya ta ƙara kudin samun lasisin kafa jami'a a kasar daga naira miliyan 5 zuwa naira miliyan 25.
Haka kuma gwamantin ta kara kudin siyen fom din kafa jami'ar daga naira miliyan ɗaya zuwa miliyan biyar.
Shugaban hukumr kula da jami'ao'in Najeriya NUC Farfesa Abdullahi Ribadu ne dai ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin.
Hukumar ta NUC ta ce matakin karin na daga cikin kokarin da suke yi na sake fasalin yadda ake kafa jami'o'in kudi a Najeriya, don ganin suna biyan bukatun yan kasar, da habaka ci gaban tsarin ilimi a banagren jami'o'in.



















