Arsenal da Tottenham na son Kean, Barcelona ta yi watsi da tayin Chelsea kan Joao

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal da Tottenham na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Fiorentina da Italiya mai shekara 24, Moise Kean. (Nicolo Schira)
Manchester United da Aston Villa a shirye suke su bada yuro miliyan 70 kan ɗan wasan Barcelona, Fermin Lopez a watan Janairu, amma matashin mai shekara 21 daga Sifaniya ba shi da niyar sauya sheka. (Sport - in Spanish)
Barcelona ta yi watsi da tayin Chelsea kan ɗan wasan gaba daga Portugal, Joao Felix a kasuwar cinikin 'yan wasan watan Janairu kafin ɗan wasan mai shekara 25 ya amince da yarjejeniyar tafiya AC Milan a matsayin aro a karshen kaka. (Sport – in Spanish)
Arsenal na son sayen ɗan wasan gaba a Portugal Diogo Jota, yayinda Liverpool ke son sayar da ɗan wasan mai shekara 28, kan kudin da ya dace saboda rashin buga wasanni sakamakon rauni. (Anfield Watch)
Atletico Madrid na son sayen ɗan wasan Crystal Palace, mai shekara 27 daga Faransa, Jean-Philippe Mateta, wanda kwantiraginsa da Eagles ke karewa a 2026. (Teamtalk)
Sai dai, mai kungiyar Lyon, John Textor, wanda ke da kaso mafi yawa a Crystal Palace, na son kungiyar ta Lig 1 ta gabatar da tayin fam miliyan 50 kan Mateta. (Sun)
Crystal Palace ta shiga zawarcin ɗan wasan Burnley Maxime Esteve, mai shekara 22, da mai taka leda a Middlesbrough, Rav van den Berg, mai shekara 20, domin maye gurbin Marc Guehi mai shekara 24 daga Ingila. (Sun)
Everton na son sayen matasan 'yan wasa daga Burtaniya domin sake sabunta alkibilarsu. (Football Insider)









