, Paris St-Germain 0-1 Arsenal
Nuno Mendes na PSG ya kusan samun damar buga kwallo, amma William Saliba ya ƙwace ta cikin tsafta ta hanyar karewa mai kyau sosai.
Dukkanin ‘yan bayan tsakiya na Arsenal sun taka rawar gani sosai har yanzu a wasan.
Mohammed Abdu
Nuno Mendes na PSG ya kusan samun damar buga kwallo, amma William Saliba ya ƙwace ta cikin tsafta ta hanyar karewa mai kyau sosai.
Dukkanin ‘yan bayan tsakiya na Arsenal sun taka rawar gani sosai har yanzu a wasan.
Tuni an fara nisa a zagaye na biyu, kuma an nuna katin gargadi ga ɗan wasan Arsenal, Cristhian Mosquera, saboda jinkirta fara wasa da kuma ɗaukar lokaci fiye da kima wajen jefa ƙwallo.
PSG an hana ta yin tasiri gaba ɗaya daga dabarun Arsenal. Mikel Arteta ya riga ya umurci ‘yan wasansa su ci gaba da wannan tsarin kare gida kamar yadda suka yi a zagayen farko, amma dole su kuma nemi hanyar kai hari.

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal tana da sauran mintuna 45 tare da ƙarin lokaci kafin su iya zama zakarun Turai a karon farko a tarihinsu.
A bangaren tsare baya, sun yi aiki mai kyau sosai, inda Gabriel ya nuna babban ƙwarewa da kwazon da ya taimaka wajen hana PSG samun dama mai hadari.
Tambayar yanzu ita ce: za su iya ci gaba da wannan tsari a zagaye na biyu, ko kuwa PSG za su fara mayar da martani mai zafi da mallakar ƙwallo da matsin lamba ya zama sakamako ya canja daga ƙarshe?
Wannan zai ƙara ƙarfafa gwiwar magoya bayan Arsenal sosai…
Arsenal sun sha kashi a wasa daya kacal cikin 117 da suka yi a dukkan gasa idan suka fara cin kwallo a zagayen farko har aka je hutun rabin lokaci (sun yi nasara 101, sun tashi canjaras 15), kuma wannan shi ne rashin nasarar 1-2 da suka yi da Bournemouth a Premier League a watan Mayu 2025.
Arsenal ta samu kwana PSG na fargabar abin da zai iya faruwa, sai dai alkalin wasa ya busa a je a sha ruwa.
Kai Havertz, wanda ya riga ya zura ƙwallo guda ɗaya a wasan, ya samu damar buga kwallo, amma ƙoƙarinsa ya karkace bayan ya bugi Marquinhos, wanda hakan ya kawar da kowace barazana.
Wannan dama ce mai wuya ga Arsenal tun bayan da suka ci gaba a minti na shida na wasan.
An yi karin minti shida, saboda dan lokacin da aka bayar aka sha ruwa har yanzu Arsenal ce kan gaba da cin kwallo.

Asalin hoton, Getty Images
Fabian Ruiz ya samu dama sau biyu ga PSG, amma da ya buga kwallon sai ta sama daga baya Piero Hincapie ya dawo gare shi.
Sai dai PSG ba su iya amfani da wannan dama ba.

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal fa ba ta bayar da wata kafa ga PSG da za ta yi mata illa, tana kuma tare wasu lokutan mutum bibiyu ma.

Asalin hoton, Getty Images
Gabriel baya wasa ya tsare bayan Arsenal sai cire kwallo yake daga gidan Arsenal da alama bayan Gunners a dinke take.

Asalin hoton, Getty Images
Wannan yanayin ya dace da Arsenal sosai, domin ‘yan wasan suna iya zama a baya suna kare gida.
Ba sa son su rika bin wasa suna gaggawa, suna bin karawar a hankali. Gunners sun taɓa zura ƙwallo ɗaya a raga a cikin wasanni biyar da suka yi na baya-bayan nan.

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ba za su damu da abin da kididdigar mallakar ƙwallo ke cewa ba (PSG suna da kashi 74% har yanzu). Suna jin daɗi sosai ko da ba su da ƙwallo.
PSG har yanzu ba su samu hanyar wuce masu tsaron bayan Arsenal ba, kuma Arsenal suna da tsari mai kyau sosai. Kalubalen PSG shi ne su gano wasu gibi a cikin masu tsare bayan Gunners, amma a yanzu babu ko ɗaya da za su iya amfani da shi.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
Fiye da mintuna 24 sun riga sun wuce a wasan ƙarshe a Champions League, kuma komai yana tafiya da kyau ga ƙungiyar Mikel Arteta.
PSG ba su samu wani babban dama mai haɗari ba sai ƙoƙarin Fabian Ruiz da ya karkace zuwa gefen raga, kuma har yanzu ba su taɓa damun mai tsaron ragar Arsenal, David Raya, da wata babbar barazana ba.

Asalin hoton, Getty Images
Piero Hincapie ya fara wasa da kyau a matsayin ɗan baya daga hagu ga Arsenal, inda ya saka ƙafa a daidai lokaci domin dakatar da Achraf Hakimi daga ci gaba da gudu ta gefen dama na PSG.
Ƙungiyar Arsenal tana da matuƙar tsari sosai ba tare da ƙwallo ba, domin dukkan ‘yan wasan fili guda 10 suna cikin tazarar yadi 30 kacal daga ragar su yayin da PSG ke ƙoƙarin neman hanyar da za su tsallaka domin kai hari.
Amma a wannan karon ba zai yiwu ba, domin tsaron bayan Gunners kamar yadda ta saba a wannan kakar, ne ta tsaya tsayin daka kuma ta ci gaba da kare raga yadda ya kamata akwai aiki a wajen PSG..

Asalin hoton, Getty Images
Abin mamaki daga Gabriel, wanda ya yi amfani da doguwar ƙafarsa wajen miƙata ya tare wata kwallo daga hannun Khvicha Kvaratskhelia a daidai lokacin da yake shirin buga ta cikin yankin gidan Arsenal.
An daga bugun kusurwa (corner) zuwa ga Fabian Ruiz, amma saboda matsanancin kusurwar da yake ciki, ya iya tura ƙwallon ne kawai zuwa gefen raga ba tare da ta shiga raga ba.