PSG ta kara lashe Champions League karo na biyu a jere

Takaitaccen Bayanin Wasa

Paris Saint-Germain 1 , Arsenal 1 After extra time , Paris Saint-Germain win 4 - 3 on penalties
Paris Saint-Germain
Arsenal
After extra time
Paris Saint-Germain ta yi nasara 4 - 3 a fenariti
Gama Wasa Paris Saint-Germain 1 , Arsenal 1,Hutun rabin lokaci Paris Saint-Germain 0 , Arsenal 1

Key Events

Paris Saint-Germain

  • O. Dembélé Penalty 65 minutes

Arsenal

  • K. Havertz Goal 6 minutes
Ba da ƙwallo a ci
Arsenal,L. Trossard (6 minutes)

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. An kammala minti 15 na farko, Paris St-Germain 1-1 Arsenal

    An kuma bai wa Mikel Arteta katin gargadi tare da Declan Rice saboda korafin da suka yi kan samun fenariti.

  2. , Paris St-Germain 1-1 Arsenal

    PSG da Nuno Mendes sun tsallake da sa’a a wannan karon. Wannan na iya kasancewa an bayar da shi a matsayin bugun fenariti, amma alkalin wasa bai yanke wannan hukunci ba. Muna ci gaba da wasa.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  3. , Paris St-Germain 1-1 Arsenal

    Hari daya mai kyau Arsenal ta kai a dukkan karawa mai hadari shi ne wanda Havertz ya ci kwallon farko da fara taka leda.

    Kenan kamar Gunners ta tsara salon tsare gida ne, amma yanzu an kusa juyawa a kara yin wani minti 15 daga nan a je bugun fenariti idan ba a ci kwallo ba.

  4. Katin Gargadi, Paris St-Germain 1-1 Arsenal

    Ɗan wasan gaba na Arsenal, Viktor Gyökeres, ya samu katin gargadi bayan da ya kama kafadar Gonçalo Ramos ba tare da wani ƙoƙari na neman ƙwallo ba.

    Live

    Asalin hoton, Getty Images

  5. , Paris St-Germain 1-1 Arsenal

    Wannan abin ya wuce tsammani! Wata babbar dama ce Arsenal ta ƙirƙira, kuma Jurrien Timber ba zai iya gaskata abin da ya faru ba, domin abin da yake yi kawai shi ne kare ƙwallon.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  6. PSG ta yi canji, Paris St-Germain 1-1 Arsenal

    Warren Zaire-Emery daga PSG ya maye gurbin Fabian Ruiz.

  7. , Paris St-Germain 1-1 Arsenal

    Arsenal sun samu bugun kusurwa sau biyu a jere, amma na biyu da Noni Madueke ya ɗauka ya lalace, inda ƙwallon ta tafi kai tsaye cikin gefen raga ba tare da wata barazana ba.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  8. An yi karin lokaci, Paris St-Germain 1-1 Arsenal

    Wasa ya koma za a buga minti 15, shin za a ci kwallo kuwa ko kuma fenariti ce za ta raba karawar?

    Paris St Germain mai kofi tana da 1 Arsenal mai fatan daukar na farko a tarihi tana da daya.

  9. PSG ta yi canji

    Daga karshe dai an canja Dembele wanda yake ta dingishi ya koma benci ya zaura.

  10. , Paris St-Germain 1-1 Arsenal

    PSG na ta kokrin fasa bayan rsenal a sauran lokacin da suka rage amma ta kasa samun wurin shiga.

    Shin za a ci kwallo kafin lokaci ya cika ko kuwa sai ta kai ga ci gaba da fafatawar.

  11. , Paris St-Germain 1-1 Arsenal

    Watakila a canja Dembele wanda ya farkewa PSG kwallo naga yana dingisawa daga gefen fili, amma har yanzu bai bukaci a canja shi ba.

  12. , Paris St-Germain 1-1 Arsenal

    David Raya, mai tsaron ragar Arsenal, wanda har zuwa minti na ƙarshe na rabin farko bai fuskanci an buga masa kwallaye da yawa ba, ya yi wani babbar ceto mai ban mamaki wajen hana Bradley Barcola samun nasarar fara tasiri kai tsaye.

    Raya ya yi jarumta inda ya durƙusa ya fantsama ƙafarsa da ƙarfin hali ya fara kai ga ƙwallon kafin Barcola.

  13. Arsenal ta kara canji, Paris St-Germain 1-1 Arsenal

    Martnelli da Madueke sun shiga fili, inda suka canji Bukayo Saka da kuma Leandro Trosaard.

    Haka kuma PSG ma ta yi canji inda Bradley Barcola ya maye gurbin Khvicha Kvaratskhelia.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  14. , Paris St-Germain 1-1 Arsenal

    PSG ta fito neman kara cin kwallo kafin lokaci ya kura, Arsenal na nuna karfi a tsaron baya, amma itama tana kai kora yadda ya kamata.

    Zagaye na biyu ya fi daukar zafi da guje guje sai ihu kake ji a cikin fili daga magoya bayan bangarorin kungiyar.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  15. , Paris St-Germain 1-1 Arsenal

    Wasan ya dauki zafi Arsenal ta fito gabaki daya domin ta kara kwallo kuma PSG ta kwace ta kai kora mai muni da ta kai ta samu bugun kusurwa - yanzu wasan ya fi daukar zafi kowa ci yake nema.

  16. Arsenal ta yi canji biyu, Paris St-Germain 1-1 Arsenal

    Canji biyu daga Mikel Arteta. An cire Cristhian Mosquera, wanda aikinsa na ƙarshe a wasan shi ne ya yi laifin da ya kai ga bugun fenariti, sannan Jurrien Timber ya shigo cikin wasa — wannan shi ne wasan farko tun 14 ga watan Maris bayan raunin da ya hana shi buga wasa na kusan watanni biyu da rabi.

    Canji na biyu kuma shi ne shigar Viktor Gyökeres maimakon ɗan wasan tsakiya kuma kyaftin ɗin Gunners, Martin Ødegaard.

    Ødegaard yanzu zai ci gaba da kallon wasan daga benci, amma zai yi fatan cewa matakinsa na gaba shi ne ya ɗaga kofin a ƙarshen wasan.

  17. PSG ta farke a bugun fenariti, Dembele

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  18. PSG ta samu bugun fenariti, Paris St-German 0-1 Arsenal

    Cristhian Mosquera, wanda ke da katin gargadi, ya doki kafar Khvicha Kvaratskhelia.

    Yanzu PSG na da wata babbar dama ta dawo da kwallo da aka fara zura mata.

    Sai dai alkalin wasa bai nuna masa katin gargadi na biyu ba.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  19. , Paris St-Germain 0-1 Arsenal

    Kyakkyawan rike ƙwallo daga David Raya, yayin da Achraf Hakimi ya buga kwallo daga nesa, ƙwallon ta billa a gaban mai tsaron raga amma Raya ya yi ƙoƙari mai kyau ya riƙe ta ba tare da ta zame masa matsala ba ba.

    Wannan shi ne mafi wahalar ceto da ya yi har yanzu a wasan, amma abu ne da ake sa ran zai iya yi a kowane lokaci.

    Shekara 11 da suka wuce, Raya yana buga wasa ne a matsayin aro a ƙungiyar mataki na biyar ta Southport, amma yanzu yana da mintuna 40 kacal ya rage ya lashe Champions League tare da tsare raga ba tare da an zura masa ƙwallo ba a wasan ƙarshe.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  20. Katin gargadi, Paris St-Germain 0-1 Arsenal

    An bai wa Saka katin gargadi, sakamkon keta da ya yi wa dan wasan PSG, Desire Doue wadda take da hadari saboda dukkansu a guje suka nemi kwallo kuma kowa ya kai kafa, amma Saka ya yi keta.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images