Adeleke ya kai wa Tinubu ziyara domin gabatar mishi da shaidar lashe zaɓen Osun

Asalin hoton, Bayo Onanuga
Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda ya gabatar masa da takardar shaidar sake lashe zaɓe a Karo na biyu.
Adeleke ya kai ziyarar ne da yammacin yau Alhamis, kwanaki kaɗan bayan da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Osun na ranar 15 ga Agusta.
Gwamnan ya samu kuri'u 511,067, inda ya kayar da ɗan takarar jam'iyyar APC, Bola Oyebamiji, wanda ya samu kuri'u 444,815.

Asalin hoton, Bayo Onanuga

Asalin hoton, Bayo Onanuga
Bayan ganawar tasu da ta gudana a sirrance, Adeleke ya gode wa Shugaba Tinubu bisa abin da ya bayyana a matsayin tabbatar da gudanar da zaɓen cikin 'yanci da adalci.
Ya ce Tinubu ya taka rawa wajen kare dimokuraɗiyyar Najeriya, yana mai bayyana shi a matsayin “uban ƙasa”



















