Michigan: Harin bindiga a coci ya halaka mutum huɗu tare da Jikkata takwas

'Yan sanda a jihar Michigan da ke Amurka na gudanar da bincike a kan kisan aƙalla mutum huɗu da wani ɗan bindiga ya yi a wata coci da ke jihar.
Har yanzu ana jin cewa akwai mutanen da suka ɓata, ba a san inda suke ba.
Maharin wani tsohon sojan ruwan ƙasar ne ɗan shekara arba’in, kuma ya danna cikin cocin ne da motarsa, kafin daga bisani ya cinna mata wuta da kuma buɗe wuta kan taron masu ibada.
Jami'ai sun isa wurin mintuna kaɗan daga bisani, har ma suka kashe shi a wata musayar wuta, kodayake har yanzu ba a san dalilinsa na kai harin ba.
Ƙarin mutum takwas sun jikkata sakamkon lamarin.
Gobarar dai ta ɗauki tsawon sa'o'i kafin a iya kashe ta, lamarin da ya sa cocin ta ƙone gaba daya.
