Lalurar da ke mayar da yara kamar tsofaffi

Chizaram mai shekara 8 da ƙaninta mai suna Chiadi mai shekara 6
Bayanan hoto, Chizaram mai shekara 8 da ƙaninta mai suna Chiadi mai shekara 6
    • Marubuci, Uche Akolisa
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC News, Lagos
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

"Wasu cewa suke yi ba ni da lafiya, amma ni na san lafiya ta ƙalau," in ji Chizaram Akwuo.

Chizaram na son karatu sosai, amma a yankin da take, yawancin yara ba sa zuwa makaranta a ranar da aka koma saboda ana tunani rana ce kawai da yara suke zuwa domin wasa.

Amma duk da haka Chizaram da ƙaninta Chiadi mai shekara shida sun je saboda suna sha'awar zuwa makaranta.

A irin wannan lokacin ne suke samun damar wasa da sauran abokan karatunsu a makarantar da suke karatu a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Jim kaɗan ne lokacin hutun rabin lokaci ya yi, inda suka fito daga aji, yara suka taru suna wasa da waƙe-waƙe da raye-raye.

Makarantar ta zama tamkar maɓoya ga yaran na Akwuo, domin suna tsira daga yaran da suke musu nune da dariya saboda yanayin jikinsu.

"Wasu suna min dariya cewa ina kama da tsohon mutum," in ji Chiadi.

A watannin baya ne wasu masu bincike a Najeriya suka gano abin da ya sa yaran suke kama da tsofaffi, inda suka gano cewa suna ɗauke ne da lalurar Cutix Laxa, nau’in 2B, wadda take sa mai ɗauke da ita ya yi kama da tsoho.

Tsakanin canfi da abin da bincike ya nuna

....

Tun suna ƙananan yara, yanayin su yake jan hankalin mutane a garinsu, kamar yadda mahaifiyar su mai suna Mrs Ngozi Akwuo mai shekara 40 ta bayyana.

"Ban fuskanci wata matsala ba lokacin da nake ɗauke da cikinsu. Nakan fara gane cewa akwai matsala ne bayan na haife su."

"Lokacin da na fara haifar Chizaram, sai wasu bokaye suka ce min wai surukata da ta rasu ce ta sake dawowa.

"Da na haifi Chiadi, sai suka ce surukina ne na sake haifa."

"Wasu kuma suka ce ai wasu waɗanda suka mutu a lokacin yaƙin Biafra ne na sake haifa," in ji ta cikin dariya.

Duk da cewa yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, Kiristoci sun fi yawa, akwai mutane da dama da suke riƙe da addinin gargajiya, waɗanda suka yi amannar ana iya sake haihuwar mutumin da ya mutu.

Farfesa Khalid Adekoya
Bayanan hoto, Farfesa Khalid Adekoya
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A nasa ɓangaren, Farfesa Khalid Adekoya, masanin ƙwayoyin halitta a Jami'ar Lagos, wanda ya jagoranci binciken yanayin yaran ya ce, "mun gwada mutum tara: mahaifi da mahaifiya da yara. Sakamakon binciken ya gano abubuwa da dama da zai yi wahala a fitar da sakamako ɗaya.

"Amma dai bayan binciken ne muka gano cewa cutar da take damun su ita ce cutis laxa (CL) Nau’in 2B.

"Wata cuta ce mai sa fata ta tattare, kuma tana nuna tsufa tun mutum na da ƙananan shekaru," in ji shi.

Babbar alamar cutar ita ce tattarewar fata da ƙanƙancewar ƙafafuwa da hannu da sauran gabbobj, kuma yawancin cutar gadonta ake yi, amma wasu na kamuwa ba tare da gadon ba.

Waɗannan yaran su ne na farko da aka samu sun kamu da cutar a Najeriya, kuma suna cikin mutum 30 da aka tabbatar suna da cutar a duniya, kamar yadda Dr Utom-Obong Akpan ɗaya daga masu binciken ya bayyana.

"A duniya baki ɗaya, akwai masu cutar guda 30 zuwa 35, a Najeriya kuma ba mu taɓa samun mai cutar ba sai yanzu," in ji Dr Akpan.

Dr Akpan

Sai dai Dr Akpan ya ce Cutix laxa ba ta cika kisa ba, amma ya ce masu ɗauke da cutar za su iya shan fama da yawan karaya a gaɓoɓi, da kuma shiga damuwa.

"Amma da muka gwada ƴan gidan, mun fahimci cewa ba sa fama da cutar damuwa a ƙwaƙwalwarsu," in ji shi.

Malamarsu a makaranta, Ms Oluchi Ogbonna ta ce suna da ƙoƙari sosai a makaranta.

"Shekara ɗaya ke nan ina tare da su. Da farko Chiadi na takwas ya zo a makaranta, amma yanzu a jarabawar ƙarshe na uku ya zo. ’Yra’uwarsa kuma ta ɗaya ko ta biyu take zuwa."

Kama da mahaifinsu

..

Kafin wannan sabon binciken, iyayen Chizaram da Chiadi ba su taɓa zuwa asibiti ba, amma suna matuƙar ƙaunar yaransu.

"Ina yawan faɗa musu cewa ina ƙaunarsu a yadda suke," in ji mahaifinsu Nwabunwanne Akwuo mai shekara 53 wanda ke sana'ar fawa.

Sai dai ba kamar yadda ake zato ba, yaran nasa ba su cika kamuwa da ciwo ba, musamman yawan ciwon kai da zazzaɓi da mutane suke yawan yi.

Mr Akwuo shi ne na farko da aka ga irin cutar a jikinsa, "mu huɗu iyayena suka haifa, ina da yayyi biyu, sai kuma ƴarbiyu da aka haife mu tare."

"Allah ne ya san abin da ya sa ya halicce ni a haka."

Ya ce a wasu lokutan, a kan gayyace shi ya fasa kwakwa a taruka a yankin saboda ana masa kallon babba.

A Kudo maso Gabashin Najeriya, fasa kwakwa girmamawa ce ta musamman da ake ba mutumin da ya fi shekaru a wajen taro musamman a bukukuwan aure da jana'iza da tarukan unguwanni.

Ya ce an taɓa kama shi da laifin rashin biyan haraji alhali shekarunsa bai kai ba a dokar ƙasar lokacin yana aji biyar na makarantar firamare.

Ana warkewa?

Likitoci sun ce cutar cutix laxa ba ta warkewa, amma sauran abubuwan da suke biyowa ana iya maganinsu ta hanyar ko dai shan magani ko ma tiyata, duk da cewa ko an yi tiyatar za ta iya dawowa.

Amma Chizaram da Chadi suna da burukan da suke so su cika.

"Ina mayar da hankali kan karatuna sosai saboda ina son zuwa ta ɗaya," in ji Chizaram.

Ta ce akwai abokiyar karatunta mai suna Kamsi da ta ce suna fafatawa wajen zama na ɗaya a aji.

Haka kuma suna wasannin barkwanci da ake yaɗawa a kafofin sadarwa, sannan Chizaram na da burin buɗe katafaren wajen cin abinci ko kamfanin sufuri idan ta girma.

Shi kuma ƙaninta Chiadi ya fi so ya zama soja idan ya girma.