Taliban ta rufe hanyoyin sadarwa a ƙasar

Asalin hoton, EPA
Mahukuntan Taliban a Afghanistan sun sanar da rufe dukkanin hanyoyin sadarwa a fadin kasar, makonni bayan da suka fara katse intanet, domin hana abin da suka bayyana a matsayin tabarbarewar tarbiyya.
Wata kungiya mai sa ido kan harkokin yanar gizo ta ce yanzu baki ɗaya ana fama da rashin intanet a kasar. Wani jami’in Taliban ya ce rufewar za ta ci gaba har sai an bayar da wata sanarwa a nan gaba.
Shugaban Taliban, Hibatullah Akhund-zada, ya bayar da umarnin fara cire wayoyin sadawar dake ƙarkashin kasa na intanet tun a farkon wannan wata.
Wakilin BBC ya ce kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce ya rasa ji ta hanyoyin sadarwa daga ofishinsa na Kabul, ciki har da ta wayar salula.


















