Ana ci gaba da aikin ceto a tsibirin Mayotte

Asalin hoton, reu
An gaggauta tura dakarun Faransa da ma'aikatan ceto da na agaji zuwa Mayotte ta jirgin sama da na ruwa domin taimaka wa mutane da mahaukaciyar gugguwa ta afkawa, irinta mafi muni a cikin karni, a yankin da ke tekun Indiya.
Guguwar da aka yi wa lakabi da Chido ta yi kaca-kaca da tsibirin a ranar Asabar, sannan ana fargabar daruruwan mutane sun mutu.
Wakilin BBC ya ce Layukan lantarki da na sadarwa sun katse, sannan tittuna da filin jirgin sama da asibitoci da gine-gine da dama sun lalace.
Mazauna yankin na ta kuka da yanayin da suka tsinci kansu na rashin abinci da ruwan sha da sauran muhimman abubuwan bukatun yau dakullum
